Chapter 63
Chapter 63
tasan akwai banbancin al'adu da yanki a tsakaninsu, kuma ko wancan zuwan da tayiyyi haka ta dinga mata gaisuwa, shiyyasa takemata uziri idan tayi wani abun. Hannu biyu ta karɓeta tana sake faɗaɗa murmushinta. Kafin ta ɗagota tana faɗin, “Uhm lallai yau munada manyan baƙi ashe”. Murmushi Farah tayi cikin basarwa, dan tanajin hausa ras yine saita gadama take, tafi yin larabcin ƴan Morocco da turanci. Sai a yanzu suma yaran gidan suka fara gaidata, duk da mamakin a yanda ta shigo gidan ɗazun ya kasa barinsu. Binsu kawai take da kallo tana amsa musu a yatsine. Kowa ta gane a cikinsu tunda tanada hotunansu na biki, duk da sanda akai auren nasu su Meenal basu da wayo sosai, amma tana jin hirarsu bakin Khalipha koshi uban gayyar idan yaso, musamman idan ƙanwarsa tana tare dashi. Kafe Zinneerah dake can ƙarshe tai da idanu, kamar zatai magana sai kuma ta basar abinta ta maida kallonta ga Khalipha da Hajiya Iya ke masa magana ya rakata ɗakin Moddibo ta huta. Da to ya amsama hajiya iyan. Shi dai oga na zaune har yanzu yana aikinsa kamarma ya manta dasu a falon, sai da Hajiya iya ta zauna a kusa dashi sannan ya ɗago ya kalleta. Ganin yanda launin idonsa ya canjane ya sata sakin murmushi ta shafa fuskarsa. “Babba da haƙuri aka sanshi, tunda ta kawo kanta karka wani saka damuwar hakan a ranka. Mu dama ai burinmu ta dinga shiga cikinmu a koda yaushe. Ba daɗin nisantarmu da kuke mukejiba”. “Amma Granny sau nawa nake cemata tazo domin gaisheku tace batason zuwa. Sai yanzu dan son fitina. Wai kinmaga a yanda ta shigo gidannan da farko ma kuwa?.......” “Shiii! ya isa, koma dai a wane dalili tazo ko ta shigo kai ka ɗaukesa ƙyaƙyƙyawa a ranka, ka kuma ɗauki ɗamarar canjata yanda kakeso duk da kayi sakaci tun farko, amma lokaci bai ƙure makaba”. Huci ya ɗan furzar kawai yana jingina da kujera da lumshe idanunsa. Sudai su Zinneerah da bajin mi su Hajiya iyan ke faɗaba sauri-sauri duk suka kammala cin abincinsu suka miƙe dan suna neman makara. Ɗakin hajiya iya ta nufa ɗakko school bag ɗinta, lokacin data fito su Yah Moos'ab duk sun fice, harsu Jamal ma. Da alama ita kaɗaice ta rage. Sau ɗaya ta kalli sashen da yake zaune har yanzu yanata faman aiki a lap-top, shi kaɗai ne a falon yanzun. Hajiya iya ta tashi zuwa kitchen saka su Baba Rahi haɗama Farah breakfast tare da Khalipha dake nuna musu yanda zasuyi. Sum-sum ta wucesa a tunaninta baya ganinta saboda aikin da yake kamar ya kwashe dukan hankalinsa. “Zonan”. Ta tsinkayi muryarsa cikin kunnenta a bazata. A lokaci guda ƴan cikinta da jinin jikinta suka yamutsa na tsoro, tuna maganar su Jamal da sukace baya maimaita magana idan yay maka yasata nufosa. Zinneerah yarinyace mai tarin nutsuwa, sam bata da garaje akan komai, hakan yasa ko tafiya takeyi saika ɗauka yangace. sai dai sam ba haka bane, halittartace hakan. Komai nata cikin sanyi da nutsuwa bana sakarciba ko rawar kai. Gabansa takai tsugunne kanta a ƙasa tana faɗin, “Yayanmu gani”. Batare daya ɗago daga abinda yakeba, a daƙile yace, “Ɗiba tissue ki kwashe wannan jambakin”. Ɗagowa tai babu shiri ta kallesa tare da waro manyan idanunta masu tsananin haske, cikin suɓucewar baki tace, “Iyeee Yayanmu miye laifinsa? Malaman basa faɗa f.....” Sai kuma tai saurin ɗora hannunta a baki saboda tuna a ida take. A karan farko yaɗan ɗago ya dubeta, hararar data saka kayan cikinta sake hautsunawa ya wulla mata tare da maida kansa ga aikinsa. Da sauri takai hannu ta cira tissue ɗin dake a centre table ta kaisa kan bakinta ta kwashe pink lipstick ɗin da yay mata ƙyau sosai tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallarta. Cikin ɗan rawar murya tace, “Na kwashe”. Yanzun ma batare daya ɗagoba yay mata nuni da hannu alamar taje. Tana miƙewa Hajiya iya na fitowa da ga kitchen, tabi Zinneerah ɗin da kallo. “Inno lafiya baku tafi bane?”. Ɗan juyowa Zinneerah tayi kanta a ƙasa tace, “Eh Granny yanzu zamu tafi”. Daga haka ta fice da sauri kafin hajiya iya ta sake cewa wani abu. Duban inda yake zaune Hajiya iya da zuciyarta ke ayyana mata ba lafiyaba tayi, “Moddibo mike faruwane da Inno, ko wani abu akai mata?”. “Waye haka?”. Ya faɗa yana ɗan ɗagowa ya dubeta. Harara ta zabga masa tana kaiwa zaune. “Kaifa wulaƙancinka yawane dashi Moddibo, ita Zinneerah ɗince baka saniba ko yau na fara kiranta Inno a gabanka?”. Ɗan murmushi yayi hankalinsa a aikinsa, a taƙaice yace, “ALLAH ya baki haƙuri”. Daga haka yaja bakinsa ya tsuke batare daya amsa mata maganar farko ba. Ƙwafa tayi ta miƙe da sauri ta nufito ƙofar fita danta leƙa. tana fitowa maigadi na rufe gate alamar su Zinneerah sun wuce. Dawowa tai ranta daɗan damuwar ALLAH yasa ba wanine yayma Zinneerah ɗin wani abuba mara daɗi. Koda ta dawo falon bata kulashi ba saima harar inda yake da tayi ta shige ɗakinta abinta. Murmushi yayi a karo na biyu yana girgiza kansa. dan yaga hararar da Hajiya iyan tai masa. Ajiye lap-top ɗin yayi zai miƙe Khalipha ya fito ɗauke da tire. Yaɗan bisa da kallo harya ƙaraso inda yake. “Yayanmu ga abincin Aunty”. Kauda kansa yayi yana ƙarasa miƙewa. Sai da ya raɓa Khaliphan zai wuce sannan ya bashi amsa da, “Ka ajiye mata anan mana ta fito taci inma zatacin”. Sanin abinda Yayan nasu ke nufi ya sakashi yin ƙaramar dariya, ganin zai shige yace, “To kaima ai baka karya ba”. “Karka damu Besty yau ina azumine”. Ya bama Khalipha amsa yana shigewa corridor ɗin ɗakin nasa. Zaune a bakin gado ya iske Farah ɗaure da towel nashi ajiki alamar wanka tayo. Sallamarsa ta sakata saurin zare wayar dake a kunnenta ta ajiye alamar magana takeyi da wani, kuma bataso yaji. Wayar yaɗan kalla tamkar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Cike da basarwa itama ta miƙe duk da tasan ya fahimci waya take ya basar dan shi mutum ne mai lura. Sai dai bai zama lallai ya nuna makan ya fahimtaba sai yaso. Ganin yanda ta ciskule fuska cike da isar tata shima sai ya basar da ita ya nufi wadrobe zai dauka abu. Bayansa ta harara da miƙewa sanin idan miskilancine ya fita iyawa. Rungumesa tai ta baya tana jero masa kalaman kewarsa da tayi a kwanakin nan da basa tare. Komai bai ceba sai janyeta a jikinsa da yayi. Tabbas yana son Farah fiye da hasashen mai tunani. Dan duk inda mace takai ƙyaƙyƙyawar Farah takai, a zaman takewarsu tana ƙoƙarin ganin ta ƙyautata masa da faranta masa. matsala ɗaya ce ke cimasa tuwo a ƙwarya game da ita zuwa uku. Na farko shine ƙin danginsa. Sai dai yasan wannan training ɗin su Mammah ne, dan mafi yawan rayuwarta a hannunta tayi. Shiyyasa yakan mata uziri da hakan da ƙoƙarin ganin ya canjata. Sai kuma shegen kishinta da sam ta tsani taga wata mace ta raɓesa koda a wayane, ga ɗan banzan zargi daya tabbatar duk kishinne yake kawo matashi. Na uku son isa da nuna gadara a dole ita isashshiyace ƴar masu mulki. Zaune yakai saman sofa yana lumshe idanu. Da wannan damar tazo ta zauna a cinyarsa tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182