Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 64

Chapter 64

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

ɓata fuska da faɗin, “Wai kana nufin fushi kake dani? Bayan nice ya kamata nai fushi da kai Yah Mutallab”. Banza yay mata kamar bazai tankaba, sai da yaji ta fara masa murje-murje a jiki cike da salo ya buɗe idanunsa da sauri. “Kinga tasarmin a jiki azumi nakeyi”. “Azumi kuma? Nami to?”. “Ina ruwanki da ko namiye?”. Ya faɗa yana tureta. Kallonsa tayi da ƙyau idanunta na kawo ruwan hawaye dan tanada saurin kuka dama. Muryarta na rawa tace, “Dan nazo gidanku zakaimin wulaƙanci?”. “Anmiki wulaƙancin, ni bance karkiyi abuba amma kikayi saboda kin rainani yanzu kina ganina dai-dai dake ko? Sannan tsabar iskanci wai gidanmu zaki shigo da wani salon sakarci, yanzu da Hajiya iya ko Baffah wani na falon kika shigo ɗin nan mi zasuyi tunanin kin koma kuma?”. A take jikinta yayi sanyi, hawaye na rige-rige sake zubowa. Kamar baza tayi maganaba sai kuma mita tuna oho mata ta kallesa da sakin ƙaramin murmushi tana share hawayenta. “Kayi haƙuri nayi kuskure, kuma daka tabbatar min hakan sai naji ban ƙyautaba, nima kuma salon bai dace dani ba sam. Amma maganar tahowa ba laifina bane har da su Mammah”. “Tunda su Mammah ɗin ke aurenki saiki kirasu ki sanar musu kin iso su nema miki wajen zama. dan ba zaki zauna a gidan nan ba. Lokacin da nake lallaɓaki kizo domin gaishesu matsayinsu na iyayena kai tsaye kike cemin bakison zuwa inda suke. To suma yanzu basa buƙatarki”. Ya ƙare maganar da miƙewa ya fice a ɗakin batare da ko waiwayenta ya sakeyiba. Bayansa ta raka da kallo idanunta na wani ƙankancewar bacin rai, ta cije baki zuciyarta na mata zugi da sakejin zargin jiya na dawo mata a rai sabo. Tabbas huɗubar aunty data hauce taso jamata wannan wulaƙancin nasa. Duk da dama bata isa tanƙwarashi ko juyasa yanda takeso ba tunda shima bauɗaɗɗen ne, dan ya fita zafin kai da shegen taurin kai tamkar shine jinin mulkin ma ba itamba. Tayi alƙawarin bazata ƙara kamanta irin kuskuren dataso tafkawa a yau ba nason kwatanta zubar da kimarta. Dan wani raɗaɗi takeji a zuciyarta idan ta tuna a yanda ta shogo gidan a dole ita wayayya. Bandama shirmen aunty data bata shawarar ba ita kuma ta hau ai ko ba'a faɗaba duk wanda ya ganta yasan wayayyace ita, bawai saita nunama duniyaba kodan jinin mulki dake yawo cikin jikinta da tarihinta. Taja ƙaramin tsaki da ɗauka waya ta kira Mammah, labarta mata duk yanda sukai yanzun tayi. Faɗa sosai Mammah keyi kafin ta yanke wayar domin nemansa. Itakuma sai ta juya akalar kiran ga auntynta. dan dama da ita suke waya ɗazun daya shigo, itama ta labarta mata komai daya faru da nuna mata gaskiya shawaran data bata na shigowa gidan a yanayin gatse-gatse baiyiba. Dan gashi hakan da tayi yaso taɓa mata kima har a idanunsa, balle ƙannensa da tasan suma kowa ya gumtsi gulma ne dan babu damar yi a gabanta ne ko shi Abdul-Mutallab ɗin dan tasan yanda suke shakkarsa a gidan. Itama dai auntyn tata kamar Mammah faɗan ta kamayi kamar Adnan ɗin ne a gabanta. Ta kumace ita ai batace tayi gatse-gatse a gabansu kamar wata sashasha ba ko mara tarbiyya, tadaice ta nuna musu banbancin da da yanzun kawai, daga haka ta yanke wayar itama ta koma neman Yah Adnan ɗin. Su dukansu daga can nemansa a waya suka shigayi, sai dai babu wanda ya iya samunsa dan cama ake musu switch off. Mammah tai ƙwafa dan tasan kashe wayar yayi tunda yasan tsiyar daya shuka. A falo kam a yanda ya fito ɗakin a fusace ya fice abinsa yasa Khalipha dake zaune yana karyawa fahimtar babu lafiya. Duk da dama dai ba wannan ne karon farkon daya fara ganin rikicin yayan nasu da matarsa ba. Duk da shi yayan nasu kan kauce faruwar hakan a gaban idonsa, amma da yake Farah mace ce mai nacin masifa da mita saita kaisa ƙarshe ya yaɓa mata maganar da zata koma rusar kuka. Dama kuma da yawan faɗan nasu ana yinsane akan zamansa gidansu nacan london ɗin, dan kullum zancenta baya wuce sai ya barmata gidanta ya koma hostel da zama. Hajiya iya na ɗaki tana gabatar da walha dan haka batasan wainar da ake toyawaba. Sai da ta idar ta fito ne ta iske shi da Khalipha ɗin duk basu a falon. Baba Rahi ma ta sake gyara falon tsaf sai tashin ƙamshi yake. A tunaninta yana ɗaki tare da matarsa yasa bata damuba ta koma ɗakin danta ɗan kwanta itama ta huta. ________________________ *_DANYA_* Yau a lissafi kwanaki bakwai kenan da bizne aikin Malam da Inna tayi, hakan yasa tun a daren jiya take zuba ido akan dawowar baba. Sai dai har garin ALLAH ya waye babu shi babu labarinsa. Bata damuba dan tasan akwai yau. Aiko yau ɗinma dai tunda gari ya waye idanunta basu huta da kallon ƙofa ba. Da taji an motsa ƙyauren gidan sai ta hau washe baki, sai kuma taga bashi ya shigoba saita haɗe fuska dajan tsaki. Kamar wasa tana zaune a bishiyar tsakar gidan har aka kira azhar. Maimakon ta tashi tai sallar sai ta cigaba da zama wai idan ya shigo ta haɗa duka tayo ai. Duk wannan zaman zuba ido da Inna keyi na dawowar Baba Tinene na a gidan tana wanki, ta ƙure waƙa a wayarta da inna bata taɓa tambayarta daga ina ta samotaba. Koda ta tambayi Innar zaman mi take ta sanar mata sai kawai ta hau dariyar shaƙiyanci tana faɗin, “Oh kice tsohon tsimin soyayya ne ya motsa Innarmu”. Banza Inna tai mata tunda tasan ba kunyace da Tinenen ba, yanzu saita yaɓa mata wata maganar. Haka ta cigaba da zama a wajen har akai sallar la'asar. Tinene data gama wankinta har tayi wanka tana kwashe kayan da alama fita zatayi a gidan. Buga ƙyauren gidan da akai da masifar ƙarfi ya sakasu dubar hanyar zauren a firgice su duka. A bazata Karima ta shigo gidan jaye da akwati buju-buju da ita tamkar wadda aka ƙwato daga bakin kura. Babu shiri Tinene ta watsar da kayan hannunta ƙasa. Innama ta zabura kan Karimar dake tafiya kamar ma da tangaɗi. “Mi nake gani haka ni Asabe. Karima daga ina kike tahe da maraicen nan?”. Ina babu bakin amsawa daga Karima, sai ma zubewa datai a ƙasa cikin hakki tace, “Innarmu ku bani abinci yunwa nakeji”. Tinene dake tsaye tana kallonsu har yanzun tace, “Tab abu mai wahala anan gidan yanzu Yaya Karima, amma bara naga inada wazobia ko awarar gidan Rashida a samo miki idan bata ƙareba dan maraice yayi”. “Nagode auta. Inna bani ruwa”. Ta sake faɗa tana kaiwa kwance da zare hijjabin jikinta gaba ɗaya ta jefar. Ruwan Inna ta ɗebo mata da sauri ta kawo mata, ta ɗagota daga kwancen da take danta bata sai a lokacin idanunta suka sauka akan sayin duka dake a wuyan Karima da damtsen hannunta ruɗu-ruɗu ga tsohon ciki. Duk da kasancewarta baƙa hakan bai hana fitar sayinba da ƙyau. “Na shiga uku ni Asabe waya maki wanga bugun haka ga ciki Karima? Badai sheɗanin yaron nanbane Babawo?”. Karima ta sake zamewa ta kwanta cikin tirɓayar jar ƙasar batare data bama Inna amsaba. Ganin Innar zata takura mata tace, “Inna

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182