Chapter 97
Chapter 97
na tsananin ciwon kai dana zuciya jarumtarsa ta shanye kaso mafi yawa. Sam bazaka iya hasaso damuwarsa a saman fuskaba, sai dai idan ka masa sanin ƙwarai a kallo ɗaya zaka gano damuwar cikin ƙwayoyin idanunsa da rauninsu ya bayyana ƙuru-ƙuru. A falo ya samu su Jamal nacin abinci su uku. Yay musu kallon nazari ganin yanda suke kowa fuska da damuwa ya ɗauke kansa. Sai da yazo dab dasu suka farga da shi saboda motsin takunsa da yawaitar ƙamshin turarensa. Gaishesa sukayi, ya amsa musu yana wucewa ɗakin hajiya iya. Koda ya shigo bayan sallamar da yayi baiji an amsaba bai samu kowa a ɗakinba sai Zinneerah dake kwance tana barci har yanzun. Hanyar toilet ya ɗan duba saboda jin motsin ruwa, da alama Granny ce a ciki. Ya ɗauke kansa yana maidawa ga Zinneerah. Bayanta kawai yake iya gani, dan haka ya taka a hankali zuwa inda ta juya fuskarta, kansa tsaye ya zuba mata fitinannun idanunsa dake cike da abubuwa masu yawa a wannan yinin, kallo yake mata irin na ƙurulla da bai taɓa matashiba, ya kai tsahon minti ɗaya da wasu sakanni a haka kafin ya matso dab da ita, ahankali yaɗan ranƙwafo kanta, tare da kai hannusa a fuskarta ya janye mata jelar gashinta daya zubo biyu da akai mata kalba da ɗan yatsansa manuniya. Motsawa tayi alamar zatai juyi. Kauda kansa yayi yanaja da baya kamar bashi ya aikataba. A dai-dai nan Granny ta fito. “Lafiya kuwa na ganka da jikka moddibo?”. Juyiwa yay ya dubeta, kansa tsaye yace, “Zanje Nigeria ne Granny”. “Nigeria kuma? Akanmi to?”. “Akan abubuwa da yawa. Kimin addu'a ke dai”. “To addu'a kam kullum cikin yimuku ita muke Moddibo, amma daka sanar dani nikam da tare muka wuce, dan zaman garin nan fa ya isheni”. Guntun murmushi yayi yana matsawa inda take. Ya kamo hannunta, cike da lallashi yace, “Kiyi haƙuri kinsan baki gama ganin likitaba, nima bawani jimawa zanyiba inagama 2days zanyi insha ALLAH”. “To ALLAH yasa haka. Amma wannan birkitacciyar matar taka tare zaku tafi? Dan bazaka barmana ita nanba”. Maganar tata ta bashi dariya. sai dai baiyiba. hannunta ya saki da faɗin, “Matar tawace birkitacciya Granny? To ai duk birkicewarta kin iya da ita na sani. Karki damu babu abinda zai faru insha ALLAH”. Ya ƙare maganar yana ɗan duban inda Zinneerah take ya ɗauke kansa. Duk da hajiya iya batasan manufar tafiyar tasaba bataso ya tafi ya barta ananba. Amma duk da haka sai tai masa fatan alkairi da gargaɗin karfa yaje yay zamansa. Shidai fita yay kawai yana ɗan murmushi. Yasan ko mi zaiyi Farah bazata sauraresaba a yanzun, dan haka baibi takantaba dan ya bar mata saƙo a ɗakinsa. A falo ya tsaya ya aika Jamal kiran Khalipha. Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito cikin shiri. Tare suka fita shi da Jamal da Khalipha ɗin da zasu masa rakkiya airport. _____________★ Zinneerah batasan da tafiyar AK ba, koda ta tashi kuma su Khalipha sun dawo gida. Kowa yaji daɗin yanda ta farka normal, sai dai jikinta duk a sanyaye, komai yinsa take kamar mara ƙashi a jiki, gashi sam bata da walwala. Abinci ma sai da Hajiya iya ta takura mata sannan tacisa tasha ruwan addu'oin da tai mata tun ɗazun kamar yanda Mahma ta faɗa. Ta farka da abubuwa masu yawa a cikin rai. sai dai miskilancinta da rashin son nuna damuwa akan abu ya shanye kaso mafi yawa, dan haka yanayin ya rikiɗe mata kawai zuwa sanyin jiki da rashin son hayaniya. A ɓangaren Farah kam kamar yanda bata fito ta nema kowa ba babu wanda ya nemeta. Sai dai mai aikinta dake ɗan shiga da fita zuwa ɗakinta lokaci-lokaci tana kai mata abunda ta buƙata, itama batasan AK yabar gidanba sai a bakin mai aikin nata daya barma saƙon cewa ta sanar mata yabar abu a ɗakinsa. Sosai hakan yayma Farah ciwo, badan tana tsoron hukuncin Mahma ba da wlhy saita bar masa gidansa. Bata kira Mammah ba sai aunty Zakiyya. Mammah kuma saita tura mata text message akan tafiyar AK ɗin. Ta kuma tabbatar mata wani ƙullin AK ya tafi yowa a Nigeria danya binne abinda ya shuka akan yaron. Itama kanta Mammah ranta yay matuƙar ɓaci da tafiyarsa bai sanar mataba. Hakan yasa ta shiga gayama Mahma rai a ɓace. Murmushi kawai Mahma tayi, a nutse tace, “Duk ke kikaso hakan Hindatu, na daɗe da nuna miki tsaurinki akan Abdul-Mutallab bashike nufin zaki iya rabasa da mahaifinsa ba. Adilah mace ce zaki iya tanƙwarata ko bataso tamiki biyayya. Amma Abdul-Mutallab namiji ne, su kuma maza da kike gani kullum tunaninsu dabanne da namu, suna da saurin hango kuskure idan sun so hakan, sai dai su ɗauki mataki kosu bari wannan zaɓinsu ne, dan hakan a jininsu yake. Ni banga dalilin da zaisa kicigaba da damuwa da alaƙar da ALLAH ya haɗaba, tun ran ginifa tun ran zane, kuma da uba ake ado kema kin sani. Inba hakaba miyasa sanda Mama ta koma Morocco kika dawo london kika zauna da Daddy? Ai da saiki bita can kota hanaki zama anan ɗin wajen Daddyn. Yakamata ki dawo da hankalinki jikinki, dan amatsalarki da Kabeer daban ki daina ƙoƙarin saka yaranku a ciki, hakan bazai haifar miki da ɗa mai ido ba. Da yawan labarai a tarihi maza ke nuna ƙarfa-ƙarfa wajen amshe ƴaƴa a hannun uwa idan ƙaddarar rabuwa ta ratsa, sai dai abinda mutane basu saniba ko suke gaza tunawa idan mu mata muka sami damar nasarar karɓe yara a hannun ubansu bisa irin wannan ƙaddarar munfi mazan atsabibancin cusama yaran aƙidar ƙin uban koda ace mune da kaifi a wajen haifar da rabuwar auren. Ya kamata ki dawo cikin hankalinki, ki daina azabartar da Abdul-Mutallab da laifin Kabeer. Dan na fahimci haushin Kabeer kike saukewa akan Abdul-Mutallab akowane lokaci, wannan itace kawai gaskiyar dazan iya gaya miki dan karkiyi biyu babu. Daga lokacin da zuciyar Abdul-Mutallab ta fara raya masa tsaurinki yayi masa yawa to tabbas zaki rasashi ki kuma rasa Adilah itama dan zatabi ɗan uwanta kodan so da shaƙuwar dake a tsakaninsu mai ƙarfi”. Mahma ta miƙe tabar mata wajen tana gama faɗa. Da kallo kawai Mammah ta bita batare data iya cewa komaiba. Tabbas gaskiya Yayar tata ta sanar mata. Sai dai bataji a ranta zata ɗauka dan itafa bazatabarma Kabeer da uwarsa ƴaƴanta ba. Dan ita tasha wahala akansu bawani shege ba. Zata riƙe ƴaƴanta shima ya riƙe nashi daya tara da shegen aure-aurensa da idan ta tuna sukafi baƙanta ranta fiye da komai. Taɗau alwashin zatayi yaƙi mai girma akan tabbatar da cigaban wanzuwar ƴaƴanta tare da ita duk wuya duk rintsi. *_NIGERIA_* Koda AK ya iso Nigeria Baffah yayi mami matuƙa, amma da yake shima a yunwace yake da son ganinsa sai hakan yay masa daɗi. Ko gaisuwar kirki basuyi zaman yiba AK ya sanarma Baffah abinda ya kawosa. hundred percent Baffah ya gamsu da hakan, shiyyasa ya shiga saka masa albarka. a take kuma ya kira Mmn Sadiq. Bayan sun gaisa itama kamar yanda suka saba cike da girmama juna, ya sanar mata hukuncin da suka yanke. Sosai mamakin hakan ya kama mmn sadiq. Cikin sanyin jiki tace, “Ya ilahi, Yaya mufa bamun faɗa muku labarin nan bane domin zargin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182