Chapter 121
Chapter 121
wajenta. Ta cancanci sadaukar mata da komai kodan alkairinta a gareta. Takumayi imani hajiya iya bazata badata ga wanda zata cutuba insha ALLAH, dan haka zatai haƙuri tayi biyayya a gareta insha ALLAHU. Ashe shiyyasa mmn sadiq keta mata nasiha mai harshen damo ita da hajiya falmata. Lallashinta sosai hajiya iya tayi da sake mata nasiha itama tana hawayen, dan dauriya dama kawai takeyi, amma harga ALLAH tana tsananin ƙaunar yarinyar, wannan kuma hukuncine na ALLAH mai saka soyayyar wani a zuciyar waninsa dominsa badan wani abu dake garesaba. Sannan ta sanar mata yau za'a kaita danya wajen babanta, daga can za'a ɗakkota insha ALLAH zuwa gidan mijinta. Nanma dai Zinni tayi kuka dajin fargabar tunkarar garin nasu data baro bisa ga dalili mai ƙarfi, takumaji ɗokin zuwa taga babanta da akace ya dawo da ƴan uwanta kuma. Hajiya iya na gidan har Zinneerah da hajiya falmata suka kammala shirinsu na tafiya, sai Saifudden da zai kaisu wanda ya iso gidan hajiya Falmatan daga baya ya samesu. ★★★★★ Koda suka baro gidan hajiya Falmata gidan mmn sadiq suka nufa domin ɗaukar Gwaggo Maryama, ai ko Zinneerah nayin arba da ita ta faɗa jikinta tana kukaama. Ta basu tausayi daga ita har maman sadiq, to amma wannan shine kawai gatan da zasuyima rayuwarta koda ace babu ransu ta dinga tunawa sun mata gata. Dan little ga mahaifinsa kawai zai kasance itama ta samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Lallashinta suka sake zamanyi da mata nasiha, kafin Gwaggo Maryama ta shirya su fito dan da ita zasu wuce danya kafin su Mmn sadiq su biyosu suma daga baya. Tunda suka ɗauki hanya Saifudden ne kawai ke hira da hajiya falmata da Gwaggo Maryama, itako tayi shiru lafe cikin kujera idanunta a lumshe. Kasancewar tafiyar ba ita kaɗai bace sai taji fargabar tunkarar danyan ta ragu mata a zuciya. Har suka iso gidan mutun ɗaya suka ɗauka hanyar kusada bata buɗe idoba. Sai da taji sun hau hanyar Danya ta buɗe idanu da kallon hanya cike da kewar garinta da tunano abubuwa masu yawan gaske da suka gudana. Isowarsu cikin garin yasa zuciyarta karyewa, sai gata tana hawaye shaɓe-shaɓe. Zuwa yanzu kam ƴan Danya sun saba ganin yawan shigowar waɗanan manyan motoci, dan haka kai tsaye aka fara ƴan ƙananun maganar cewar angon Zinneerah ne yazo. Su Zinneerah dai basusan anaiba, dan motar na tsayawa a ƙofar gidansu daya sha gyaran biki da aketa shirye-shiye sai zuciyarta ta ƙara karyewa. Itace ƙarshen fitowa jiki a sanyaye, sai da ta ƙarema anguwar tasu kallo da yara da suka baibaye motar waɗanda takeda tabbacin babu wanda ya shaidata, wasuma basu santaba. Murmushi tayi a karo na farko da ambaton Alhmdllhi cikin matuƙar rauni. Da sauri ta buɗe idanun nata saboda jin maganar baba dake fitowa yanama Saifudden sannu da zuwa. Juyawa tai a hankali ƙirjinta na harbawa da sauri-sauri. Shima baban tunda idanunsa suka sauka akanta dukkan maganar bakinsa ta gagara fita. Yay tsai yana kallonta zuciyarsa fal wasiwasi. Tabbas fuskarnan dai ta ɗiyarsace, kuma irinta tsohuwar matarsa mafi soyuwa a garesa. Sai dai kuma yana tantama ace Zinneerah ɗinsa ce ta zama budurwa haka tamkar wata jinin larabawa. (Dan gyaran datasha ya sake ƙawatata da ƙyawu mai ɗaukar hankali) A wani irin slowly Zinneerah ta nufi baba, batama san ta faɗa masa a jikiba ta fashe da kuka ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Tinene ƙofar gidan wadda tun ɗazun aka aiketa amma sai yanzu take dawowa gidan, dan yanzu bata samun damar fita yawonta saita hanyar aikan. Da mamaki take kallon wadda ke runme musu da baba, dan haka cikin sassarfa ta nufi cikin gidan kai rahoto. A zabure Inna data gama yima yarinyar karima wanka ta miƙe, hakama Sa'a dake wanke-wanke. Karima ma madai da Yaya Atine dake a cikin ɗaki sai gasu waje wuff babu shiri. Yaya Gajeje dake can gaban murhu ita da ɗiyar Baba Sabi'u suna suyar naman ragon sunan Karima suma dai duk duban Tinenen sukai, amaryar baba dai datasan ina zancen ya dosa tana ƙofar ɗaki zaune tana gyaran ƙumba da tsohon cikinta, murmushi kawai tayi hankali kwance. Kafin bakin wani ya samu damar furta kanzil sai ga baba ya shigo baki washe yana sharar ƙwalla, hannunsa riƙe da Zinneerah dake kuka rurus. Hajiya Falmata da Gwaggo Maryama biye dasu suna faman murmushin jin daɗi. Yaya Gajeje ce ALLAH ya bama ikon gane Zinneerah, a take ta saki ludayin hannunta tana ƙwalalo idanu waje da faɗin, “Zinneerah!!”. Da gudu Zinneerah ta saki hannun Baba tai kan Yaya Gajeje. Bata damu da a yanda yaya Gajejen takeba ta faɗa jikinta suka saki kuka tare. Tuni Sa'a ta saki soson wanke-wanke itama tayo kansu. Su kansu su Yaya Atine da ba ƙaunar Zinneerah ɗin sukeba, kuma tunda aka kawo kayan lefen nan nata ƙiri-ƙiri suka nuna hassadarsu suda Inna basu san sanda suka nufo ƴar uwar tasuba suka haɗu wajen rungumeta. Hakan da sukai ya matuƙar saka baba jin daɗi, yayinda Inna ta daka musu wata irin gigitacciyar tsawa. Sai dai ina su bama susan tanaiba. Amaryar baba kuwa tashi tai da ƙyar tanama su Gwaggo Maryama barka da zuwa, waɗanda sai yanzu Inna tama gansu. Gabanta ne yay matuƙar faɗuwa datai tozali da fuskar Gwaggo Maryama, dan sarai ta ganeta. A kiɗime tace, “Dangin Hauwa a gidana?”. Karaf kuwa sai a kunnen baba. Kansa tsaye yace, “Hauwarma tana nan tafe a gidan naki”. Ya raɓata ya wuce abinsa dan tabarma zai amsa ya kaima Saifudden. Ba ƙaramin dukan ƙirjinta furucinsa yayba. Tai baya tana neman faɗuwa ALLAH ya taimaketa ta dafe bango. Babu wanda ya lura da halin da take ciki dansu ta murnar ganin ƴar uwarsu sukeyi. “Zinneerah kece kika koma haka kamar wata ƴar ƙasar waje?”. Yaya Gajeje ta faɗa tana sharema Zinneerah hawayenta, itako murmushi kawai take ga hawaye shaɓe-shaɓe. Sa'a dake riƙe da hannunta tace, “ALLAH na gode maka daka nunamin wannan rana da naketa mahwalki da fatan gani, nagodema UBANGIJI daya maido ƴar uwata gida cikin kamala da mutunci harda igiyar aure akanta”. Yanda take maganar da kuka ya sake raunana zuciyar Zinneerah dasu Gwaggo Maryama da amaryar baba ta sama tabarma a ɗakinta, dan suna jiyosu. Sake faɗawa jikin Sa'a Zinneerah tayi tana sakin wani sabon kukan. Sai a lokacin baba daya dawo ɗaukama Saifudden buta zaiyi alwala yay sallar la'asar ya ɗauka hanyar komawa ya lura da halin suma da Inna ke ciki. Sallallami ya fara da nufarta, a take suma hankalinsu ya dawo kanta duk suka juya. Ita Zinneerah ma sai yanzu idanunta sukaga Innar. Ruwa aka yayyafa mata ta farfaɗo, tana buɗe idanu sai akan Zinneerah, ai sai kawai ta fashe da kukan daya bama kowa mamaki da tsoro a wajen. Tashi Baba yay abinsa ya ɗauka butar data kawosa ya fice. Zinneerah ta matsa jikin Inna tana hawaye da nufin rungumarta, hankaɗeta Inna tai cikin kuka da faɗa. “Munahika karki taɓeni, kinje kin gama yawon tazubar ɗinki zakizo ki goga mana ƙanjamau. To idan uwarki tayo asiri da rufe ido da bakin kowa akan hakan ni na gagareta, asirinta bazai ciniba. Nasan komai kina ikko kina karuwanci, shima shegen da aka ɗaura muku auren ƙaryar abokin cin mushenki ne. ALLAH ya wadatanki tambaɗaɗɗiyar yarinya gantalalla”. “Kece gantalalliya, ni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182