Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 138

Chapter 138

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_* _________________________ *Page 54* ...........Duk yanda taso dojewa a baya doleneta ta yarda suka shigo sashen nata a tare, kusan duk sai da suka ɗago suka kallesu jin sassanyar muryarsa na sallama. Bayansa ta koma ta maƙale saboda kunya da taji na iyayenta da ƴan uwanta. Gani take kamar kowa zai gane abinda ya faru kafin su shigo, Aunty Salima ce ta bashi kujerar da take zaune. Babu musu ya zauna yana musu sannu da zuwa fuskarsa a ɗan sake. Cikin mutunta juna sukai gaisa. Yana musu godiya suna masa, tare da jera musu addu'oin zaman lafiya mai ɗorewa na har abada da zuri'a mai albarka da nagarta. Gwaggo Maryama ce tai masa bayanin kowa a wajen da matsayinsa wajen Zinneerah, ya ƙara musu godiya yana ambaton masha ALLAH. Kafin ya miƙe bayan suma su Meenal sun gaishesa. Sai da yazo saitin Zinneerah dake tsaye yay magana ƙasa-ƙasa yana raɓata ya wuce. “Ki sameni idan sun tashi tafiya”. Binsa da kallo kawai tai ta gefen ido dan ya riga ya shige bai bata damar amsa masaba. Hankalinta ta maida akan ƴan uwanta dake yabonsa da sake jera masa addu'an fatan alkairi. Ita dai uffan bataceba sai zama data sakeyi. Sun ɗan ƙara taɓa hira kafin su mike domin ganin ɗaki. Lungu da saƙo babu inda basu shigaba, Sa'a nata santi da ƙarajin daɗin sauyin rayuwa da ƴar uwarta ta samu. Hakama Yaya Gajeje bakinta yaƙi rufuwa dan farin ciki. Karima da Atine kam dai anata naɗar rahoton da za'a kaima Inna fuska a taɓe. Babu wanda ya damu dasu, dan ƴan ɗan-musan ma dasu Gwaggo Laritu sai faman yabawa sukeyi abinsu. Bayan sun gama zagayensu sukai haramar tafiya, maganar cewa ta sameshi yasata cewa su jirata tana zuwa. Duk da ranta cike yake da fargabar abinda ya faru ɗazun ga kunyarsa haka dole ta nufi sashen nasa again. Yanzu kam bata tsaya knocking ba sallama kawai tayi da murɗa kofar ta shiga, yana tsaye alamar shirin fita yake ta shigo bayan ya amsa mata sallamarta da bata izini. Kanta a ƙasa saɓanin shi da yake kallonta kai tsaye, yanda batai magana ba shima baiyiba, sai ma ya ɗauke kansa daga kallon nata yana ƙoƙarin tattare takardun daya baza a falon. Ganin haka yasata faɗin, “Yayanmu zasu wuce”. Bai amsataba sai da ya gama abinda yakeyi, ƙananun ledoji guda biyu dake a saman kujera ya nuna mata, “Ki bama Gwaggo Maryam ɗaya taba ƴan ɗan-musa, ɗayan ki bama Gwaggo ta danya nasune suma”. Ɗaukata tai tana kaiwa tsuggune. “ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara arziƙi mai albarka da amfani, ya cigaba da baka kariya a dukan al'amuranka”. Har cikin ransa yaji daɗi da farin cikin wannan addu'a tata, dan haka yay ɗan murmushi yana amsa mata da “Amin, nagode”. Kamar yanda ya bata umarni haka ta aikata, aiki suka shiga godiya da masa addu'a harta rakosu harabar gidan ita da su Meenal. Kasancewar motocin da zasu wuce dasu suna ta waje yasata jan birki iya nan tana hawaye. Rungumeta Sa'a tayi itama tana hawayen, dan harga ALLAH tanason Zinneerah. jitake kamar karsu rabu a yanzu, amma yaya zasuyi da ƙaddarar aure sai haƙuri. Tanaji tana gani suka wuce su Bahijja suka tafi rakasu har waje. Jikin bango ta lafe hawaye na cigaba da sakko mata, ɗan kwana ukun can da taje tayi a Danya sam ba isarta sukai ba, musamman da ayanzu baba ya samu ƴancin kansa daga hannun Inna, sai taji inama tana a zaman gidan ne har yanzu. Dawowar su Bahijja ya sata share hawayenta suka koma ciki suna mata tsiya ƙasa-ƙasa gudun kar Yayansu yaji. Ita dai hararsu kawai tayi dan basusan yaya takejinta bane. Da taimakonsu ta gyara falon, suna ƙoƙarin dasa zaman hira AK ya shigo. Tsit sukai daga dariyar zancen Meenal dake basu labarin abinda wata innarsu datazo daga bauchi tayi a sashen Granny yau da safe. “Ku baku wuce ba?”. Ya faɗa idonsa akan Zinneerah. Meenal ce tai ƙarfin halin bashi amsa. “Yayanmu muna nan sai anjima, dan ƴan bauchi ma zasu zo suyi muku sallama”. Baice komaiba sai kallon agogon hannunsa da yayi ya sake duban Zinneerah. “Ni zan fita, Khalipha zaizo da mai gyaran ruwa dake fita ta baya, idan sun gama ki ɗauka masa kuɗi a ɗaki saman bedside drawer”. Kanta ta gyaɗa masa da cewa “to” idanunta a ƙasa. Daga haka shima ya juya ya fita a binsa suna masa a dawo lafiya. Sai da suka tabbatar da fitar motarsa a gidan sannan bakin su Meenal ya buɗe. Suka sheƙe da dariya suna tafawa da faɗin, “Soyayya ruwan zuma. Abin mamaki Yayanmu da auta a gado ɗaya”. Hararsu kawai Zinneerah tayi ta ɗauke kanta. Bahijja ta kamo hannunta murya ƙasa tace, “Tawan dan ALLAH da gaske ɗaki ɗaya kuka kwana da Yayanmu a gidan nan?”. “Ya ilahi”. Zinneerah ta faɗa tana zaro idanu, sai kuma ta rankwashi kan Bahijjan da faɗin, “Kirasa a waya ki tambayesa mana, wai yaushe kuka lalace haka ne?”. “Karkiga laifinmu, tunda kema jiya Yayanmu ya lalataki a gado muma gara dai ku guntsa mana kafin a kaimu dan wlhy nima aure nakeso”. Cewar Meenal tana wani karya jiki. Bahijja tai zaram tana faɗin, “Haɗa dani ƴar uwa”. Kallonsu kawai Zinneerah take baki buɗe, suko ko'a jikinsu. A haka su Jamal suka shigo suka samesu ɗauke da abincin rana, yanzu kam a sake suka shigo dan sunsan sun baro boss a can gidan. ___________________★ A ɓangaren su Farah kam lafiya lau ta farka yau, sai dai tunda ta tashi hawaye basubar sauka mata a idanu ba, sai faman sambatu take akan dan ALLAH suce mata mafarki take bada gaske AK yayi aure ba. Da farko daga Mammah har Mahma lallashinta sukeyi, ganin abun nata bana ƙare bane yasa Mahma fara mata masifa. “Ke dan ALLAH kin ishemu haka nan, ba'irin wannan ranar ake hanngo mikiba ana nuna miki hanya kina kaucewa. Ni bansan wane irin rashin hankali ke damunku ku yaran yanzu da bakwa aiki da tunaninku ba. Abinda kawai kuka ɗauka idan namiji na sonku dolene ya cigaba da sonku, kun manta ita soyayya ado ce a cikin aure, a duk lokacin da ɗiya mace ta kasa toshe ƙofofi da ramukan ginshiƙan aurenta adon soyayya zai disashe. Duk yanda zakiso miji ki nuna ƙin danginsa rayuwar aurenki na cikin matsala koda kuwa su suna nuna miki basa son nakine ƙiri-ƙiri a gabansa. Koda shike kawo miki sukar danginsa ki faɗi alkairi da tausar zuciyarsa karki yarda ki tofa mara daɗi. Kiyi haƙuri da halayensa ku kashe ku rufe a ɗakinku dan kai ƙarar miji ga iyayenki ko nashi na zubar miki da kima, ke hatta ƙawayenki kikace ke kullum ƴar fallasa asirin gidankice da niyyar neman shawara to kina cikin kwan gaba kwan baya kuwa a garesa da zubar muku da kimar aurenku. Domin shi aure ibada ne ba komai ake samu hundred percent a cikinsa ba. Dole yau ayi dariya gobe kuka, jibi rabi da rabi tsakanin ɓacin rai da farin ciki. Sannan duk son da namiji ke miki kika nuna zaƙewa da yawa

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182