Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Makauniyar Kaddara Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ai. Wannan yasa duk bikin na Karima yaƙi armashi kamar yanda Inna taci buri. An ɗaura aurene kawai hankalin mutane ba'a kwance ba. Kamar ko yaushe yanzunma Baba baice ƙalaba akan al'amarin, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci tsantsar tashin hankali da damuwar dake a tattare da shi. Yana tsananin so da ƙaunar Zinneerah, musamman daya zam soyayyar da yakewa mahaifiyarta bayan barinta gidan nasa duk sai ya tattarata akan Zinneerah bayan itama wadda yake mata. Dan wannan tsantsar soyayyar Inna ta hango tattare da shi ai ta shiga ta fita ta raba tsakaninsa da ƴar tasa har bai iya cewa uffan akan al'amarinta a gidan. Haka wannan dare ya kasancewa duk wani masoyin Zinneerah a cikin tashin hankali da damuwa da tausayinta. Inda washe gari kuma suka sake tashi da wani sabon tashin hankali na barin baba shima garin. Wannan tashin hankalinne ya sake ruɗasu suka sake ƙare yinin ranar da neman Zinneerah da Baba a dukkan garuruwan dake da maƙwaftaka da su. Sai dai babu koda labarin ɗayansu. Yau kam saɓanin jiya harda Inna a wannan tashin hankalin. Dan bata taɓa tunanin Baba zai iya bin bayan Zinneerah ba. Duk haukanta da rashin tausayi tana bala'i-bala'in son mijinta uban ƴaƴanta. Dan badanma soyayyar da take masanba bazata taɓa zuwa wannan ƙauyen ta zauna ba da sunan aure. Saboda garinsu Marabar musawa yayi ashirin din Danya yawa da komai na kayan more rayuwa. ★★★ Tamkar jiya yau ɗinma sai gabannin asuba Zinneerah ta yada zango a wani ƙaramin ƙauye da ke a bakin titi. Yau kam a ƙarƙashin wata bishiya ta samu ta kwanta sai barci. A haka mutanen ƙauyen suka wayi gari suka ganta. Da farko ma su tsoronta suka farayi, dan a fuska da jikinta babu mai ɗaukarta mara hankali kasancewar komanta fes yake. Haka yara suka zagayeta harma da manyan kowa ya kasa zuwa inda take. To duniyarce babu gaskiya ai. Barcinta tasha sosai sai wajen sha biyu ta farka da yunwa kamar jiya. Ta shiga bin mutanen dake zagaye da ita da kallo ɗaya bayan ɗaya. Batare da tayi magana ba ta maida kanta ƙasa ta duƙar tana yamutsa fuska da dafe cikinta dan yunwa takeji sosai. A ɗan tsorace wani dattijo a cikinsu yace, “Mutum ce ko aljana?”. Banza Zinneerah tai bata amsaba, sai faman riƙe ciki take ita dai. Kusan min tuna biyar ta ɗago tana kallonsu hawaye na zirara mata. Cikin rawar murya tace, “Dan ALLAH ku bani abinci”. Kallan kallo suka shigayi a junansu batare da wani ya amsa mata ba. Cikin fisgar numfashi ta kuma faɗin, “Abinci dan ALLAH zan mutu”. Tausayintane ya kama wani matashin saurayi dake tsaye gefe da jikka a hannu alamar abin hawa yake jira. Ya matso kusa da ita yana faɗin, “Komi aka baki zakici dai ko?”. Da sauri ta kaɗa masa kanta. Fuskarsa cike da tausayinta ya zaro hamsin a aljihu ya bama mai wainar ƴar tsala ta gero a gefe yana faɗin, “Bata ta duka”. Amsar kuɗin mai ƴar tsala tayi ta zuba mata wainar a roba, tasa yaji a gefe ta miƙawa saurayin. shine ya ajema Zinneerah gabanta, zata saka hannu ya dakatar da ita akan ta bari ta wanke hannun. Ina bata sauraresaba ta hau cin kayanta hannu baka hannu ƙwarya. Sai gashi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta cinye tas. Ruwan da ya ajiye mata dan wanke hannu ta raruma ta kafa kai tasha sosai. Sai gata tana lumshe idanu da sakin murmushi, a fisge tace masa “Nagode”. Daga haka ta zame ta kwanta a wajen sai barci. Yanda tai din ya bama kowa mamaki, sai dai bayanin wani tsoho ya sakasu maida kallonsa garesu. “Wannan yarinyar ba mahaukaciya bace, da alama kurciya akai mata ko makamancin hakan”. “Baba lado miye kurciya?”. Saurayin da ya sai mata ƴar tsala ya tambayi tsohon. Kamar tsohon bazai sake magana ba, sai kuma ya ɗan girgiza kansa yana mamular goron dake bakinsa. “Kurciya asirine mana shamsu. Akan yima mutum idan ba'a son ya zauna a waje. Akanyi asirin a jikin tsuntsuwar kurciya. Duk inda kurciyar ta nufa can mutum zai nufa shima”. A take jikin mutanen wajen yay sanyi, tausayin Zinneerah da batasan sunayiba ya shigesu sosai, suka shiga ambaton ALLAH ya saka mata. Yauma kamar jiya yunwa ce kawai ke farkar da ita. Data samu taci saita koma barci, da daddare tsohon nan ya saka aka kama masa ita zuwa gidansa da nufin zai taimaketa. Babu musu kuwa matarsa ta amsheta hannu bibbiyu dan dama ya mata bayani akan Zinneerah ɗin hasalima itace ta bada shawarar su taimaketa. Sai dai kuma yauma cikin daren ta farka a firgice kusan ƙarfe ɗaya. Cikin sanɗa ta silale tabar gidan dan ko katangar kirki tsoffin basu da ita. Haka ta ɗauki hanyar titi taita tafiya cikin ficewar hayyaci. Sai dai wayar gari sukai babu ita. Sun tausaya mata matuƙa. Dan basusan inda ta nufaba kuma. gashi ko jikkarta bata ɗaukaba nan ta barta a gidan nasu. Haka al'amari ya cigaba da kasancewa akan Zinneerah. Duk inda asuba tayi takan tsaya ta yada zango, a wani garin ta samu tallafin abinci, wani garin kuwa babu mai kallonta. Dan zuwa yanzu kamanninta sun fara canjawa saboda rashin wanka da sauran buƙatu. Ba kullum take samun damar yada zango a gariba. Watarana a daji take yada zangon, haka zata yini kuka da juye-juyen yunwa har barcin nata na ƙa'ida ya ɗauketa. A randa ta cika kwanaki goma sha ɗaya da baro gida ALLAH ya iso da ita cikin garin kano, inda ita batasan inane ɗinba. Sai dai taga yawan jama'a da gine-ginen nan yafi na duk garuruwan data baro a baya. Anan ɗinma ba a hayyacinta takeba. Dan kamar yanda ta saba kwanciya da tashi taita tafiya haka ta cigaba dayi, hakanne yasa taita nausa kanta cikin ƙwaryar kano sosai har batasan tanayiba. Zuwa yanzu har takai kowa kallon mahaukaciya yake mata, dan yaran kan tsokaneta. Harma manyan sukan koreta idan ta ɗan laɓaɓa wani gurin zata huta ko tana neman abinci. A haka ta sake share kusan sati biyu cikin ƙwaryar kano, indan kuma an haɗa da barowarta gida tana neman ƙulla wata ɗaya. Ɗan cikinta ya fara fitowa fili kowa yana gani, duk da ba wani uban girma yayiba na azo a gani. Duk da yanayin da take ciki haka take kasancewa cikin laulayi, dan kusan kullum da zazzaɓi take kwana, wani abin kuma idan taci takanyi amansa dan baya zama. Yau data kasance juma'a mutane nata kai kawo na zuwa masallatan juma'a a cikin garin na kano, wanda a yanzu haka Zinneerah na gab da barin garin tana neman ɗaukar hanyar jigawa dutse. Tafiya take a hankali cike da kasala saboda rashin samun inda zata raɓa ta kwanta tun ɗazun, dan tun barcin gabannin asuba data kwanta a ƙofar wata maƙaranta gari na wayewa aka korota. Shine har yanzu bata samu ta sake samun wajen kwanciyarba kuma. Ga yunwa na cin hanjinta da zazzaɓi. Tun tana tafiya tana kallon inda take saka ƙafarta har takai idanunta sun lulluɓe da duhu. Gudu motar takeyi sosai daga hanyar jigawa tana nufo cikin Kano. Yanda passengers ɗin cikin motar basu damu da gudun da direban keyiba zai tabbatar maka da suma son ai gudun suke dansu sami sallar

Table of Contents

Chapters

182 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182