Chapter 9
Chapter 9
damuwarki ba saboda yana yinki ya nuna cewar damuwar babbace,kuma tana damunki matuk'a don najima ban ganki cikin wannan yana yin ba,don haka maza gaya mun abunda ke damunki yanxu nan." Raurau tayi da ido zatai kuka don bata san taya zata gaya ma mama abunda ya faruba,amman dole zata boye wani abun don tasan makamar abunyi. Cikin dakoya da kokarin boye abunda ke ranta "tace mama bafa wani abu bane kawai dai wani abune daya faru yake daure man kai tunda abun yafaru duk nakejin babu dadi." Duk natsuwa sukai suna saurarenta mama tace "inajinki meye ne Allah yasa ba akan karatunki bane." Kwanciya tayi jikin yesmin dake gefenta tace"wanine yayi hadari bakin titi,yawwa mama inkin tuna rannan wanda nace maki ankasa tai makarshi." Cikin kulawa da maida hankali kan abunda take cewar tace mata"eh natuna sofyna meyafaru bayan nan." Ta sake mazewa yadda maman bazata gano komi ba tace"wlh mama abunne yaketa damuna tun rannan to yau naga mutumen kamar wani mahaukaci bakin titi yaci kwalar wani mutun daker aka kwaceshi,ni mama sai nake ganin kamar nasan shi wlh,kuma abunda yaban tausayi gareshi mutane sun zagayeshi sai duka suke ga wani Alhaji sai tijara yake yana zaginsa maganganu marasa dadi hada ce mai wai iyayensa ma sun gaza dashi balle wasu,abun dai babu dadin ji wlh harfa cemai yake dan iska fa mama.wlh yaban tausayi ya kira yan sanda suka tai dashi. Naji mai taxi din daya taho damu nida wani yana cema wanda ya dauko mu tare wai kowa yasan shi dan iskane kuma da iyayensa masu hali akwai abunda yayi suka korai." Shiru mama tayi tana jin abunda fiyah ke sanar da ita taso d'ago wanda take maganar kanshi amman bata tabbatar ba,cikin kulawa tace mata"dawa kikace yake maki kama." Aranta tace yawwa anzo wajen don daman so take tasan dagaske dan gidanne kuma me ya fiddashi inhar dan gidanne. "Mama yama sunan wancen mutumen mai kudin unguwar nan,uhmmmm yesmin yama ni wlh mance sunansa nake ma saboda mugun halinsa." Tayi hakane don ma kar mamar tagane dagangan tayi haka........cikin sauri yesmin tace "nagano shi wlh,mu'azzam canji tabbas sunan kenan ko mama." Wani irin kallo mama kewa Fiyah cike da tuhuma ganin haka yasa fiyah takiyarda su hada ido da maman don tabbas idan suka hada ido tasan zata gane karya tasheka mata do dai ta samu wani bayani. More comment more typing. Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........7 Kallon fiyah mama tayi tace"mama lfy,naga kinyi shiru kina kallona." Numfashi taja tace"babu komi ina nazarin yaron dakike magana akai ne." Yesmin tace "Adda daman kinsan shi ne." Girgiza kai tayi tace"nace maki nasan shine,bakiji ina cewa yana man kamada yaran wancen gidan." Mama tace"yaron gidanne shine babban gidan gaba d'aya." Wani dadi ya kamata tasamu abunda take son ji,canza fuska tayi kamar bata damuba tace"kinsan sa kenan mama,to abun mamakin shine meyayi haka da zafi zasu korai." Mamar yitayi kamar batasan me take fada ba,saida fiyah ta sake magana tace"mama kinji meya yi masu da zafi haka,wlh yaban tausayi." "Sofiyya bakijin mutuwar sarki bakina,babu ruwana ni kamar kisake baban ku yaji kina wannan maganar,don ranki zai mummunan b'aci.keda damuwar wani sai ta zama taki,kirufa ma kanki asiri ma kibar wannan halin don yana iya jefaki cikin matsala." Shiru sukai suduka don maganar mama ta daure mata kai,har ta kasa hkr tace"mama don ka ji tausayin halin da wani yake ciki kuma kayi niyyar taimakonsa sai yakoma matsala,tunani na aikin ladane taya zaka shiga matsala." Wani irin kallo mamar ke mata kamar zata maketa tace"mekike nufi sofiyya,dake nake nace mekike nufi karki cemun zaki saka kanki cikin wannan abun,wallahi karki kuskura kiyi gigin farawa,ina ruwanki ina abunda ya shafeki da rayuwar da yake.wannan halin na shegen tausayi saiya kaiki ga nadama,kisake kuma babanku yaji wannan maganar." Idon ta yayi rau rau k'iris takejira ta yi kuka,daman kuma sofiyya gwanace ta iya kuka da abunda ya kai da wanda bai kaiba. "Yanzu mama tsakani da Allah kinji nace wani abu,daga kawai nace haka ni wlh kibarcewa haka kuma ma ina ruwana dashi ina ma zan ganshi balle in taimakeshi ehy." Tatashi ta nufi dakinsu tana kuka yesmin duk taji babu dadi itama tashin tayi tacewa maman saida safe karfe takwas suna da pratical. Koda fiyah ta shige d'aki kukanta tayi mai isarta sanan ta kwanta,bakuma don ta hkr da cikar burin ta ba. Dr daya duba Alfah wancen karon wannan karon ma shi malik ya kira,ya samai drip yayi mashi allurai inda yaji raunika yayi dressing. Dr yace ma malik"Alfah ya na cikin jarabawar rayuwa,amman a bun damuwar shine yadda zuciyarsa ta k'ekashe babu wani abu dake girgizashi,babu kuma abunda ke sata tayi laushi.malik zama bai gammuba don kuwa idan ya cigaba DA zama haka wataran zaima kanshi illar da mu likitoci bazamu iya gyara taba." Jan numfashi malik yayi yana jinjina maganar Dr tabbas duk abunda ya fada gaskiyane,a bun ya isa haka yana bukatar matai maki cikin kulawa da Alfah. "Haka ne Dr nima zuwa yanzu na gaji da halin Alfah,shekara biyar ba kwana biyar bane yadace zuwa yanzu ansamu sauki,don haka Zan San abunyi insha Allah duk sanda nake bukatarka Zan maka a bun ya isheni haka dole asamu mafita." Haka sukai da dr ya sake yiwa Alfah wata allurar sannan ya tafi,bayan ya gama nuna ma malik yadda zai cire mashi drip din idan ya kare. Tunda Dr ya tafi malik yashiga tunanin abubuwan dasuka faru baya,yana son ya kamo bakin zaren duk yadda yake za to lamarin a bun yaci tura,don ya kasa fahimatar yadda lamarin yake,yana bukatar dogon nazari da kuma abokin shawara don samun taimako wajen yadai zai kamo makamar matsalar. ************ Tun data tashi yau bata koma ba saida ta gama duk ayyukan gidan,sannan tashiga wanka yau tana son ta samu ganin malik,sufara magana kafin komi ya daidaita.don tayi alkawarin taimakonsa koda yanaso ko baiso,yesmin tariga ta fita sannan itama ta tafi,bayan ta anshi kudin taxi da na break. Bata da lectures din safe shiyasa ta yanke shawarar Fara zuwa tayi magana da malik,idan ta fito karfe sha daya ta shiga wata 11:30 ta fito 1:00 bata sake komawa kuma sai 4:00 kafin nan har taje gidan Antyn tadawo. Unguwar ta kwatanta ma Mai taxi din tanajin kirjinta yana dukan Tara tara,runtse idonta tayi tana karanto adduoi,akan Allah ya bata Sa,a. Biyansa tayi ta tsaya tana kallon get d'in faduwar gabanta yana yawaita,kamar kwai yafashe Mata aciki take takawa zuwa wajen karamar kofar.hanunta yana karkarwa ta danna bell din kirjinta yana duka,ba komi take tsoro ba irin bak'ar zuciyar guy din,karya kafta mata irin Marin da feea tasha rannan. Saida ta danna sau biyu sannan taji alamun tahowar mutun,ai jitai kamar ta kwala da gudu,saboda tsananin tsoro da fargaba.........budewa akai suka tsurama juna ido itada malik,duk ta dirirce saboda yada yayi Mata kwarjini,kasancewar shima malik ba daga baya ba wajen kyau. Murmushi ta sakar mashi Mai tsananin kyau tace"ina kwana." Kallon ta yake fuskarsa da yalwar Fara,a yace"morning,what u want." Sai yak'e take tace"I'm sofiyya El-ladan Amman anfi Kira na da fiyah,I want discous serious
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101