Chapter 13
Chapter 13
gabanta. "Bismillah tukunna,kafin infara zuba maki surutu in kwareki." Dariya tayi tace"haba dai yah malik." "Ehy mana,inason in sanar dake waye ABDOUL-NASSER ALFAH,don kisan ta ina zamu shawo kan abun." Jinjina kai tayi ta d'an kurb'i lemun ta d'anci springros ta goge bakinta da tishu. "Yah malik ina jinka,naci ai wlh bana jin yunwa nayo kalaci sosai." Baice komi ba ya gyara zaman shi yafara magana kamar haka cikin sanyi da tausasa harshe. "Abdoul Nasser muazzam kabir canji d'ane ga Alh muazzam canji shugaban y'an canjin Abuja gaba d'aya,yyi suna yayi fice a k'asa baki d'aya,domin bai anan kadai arxikin sa ya tsaya ba,ya rik'e minister a oxport sannan yana da kamfanin motoci M.K motors dake cikin garinnan,wande kika sani sannan yana kasuwancin shinkafa babu inda motocin sa basa zuwa,legos,ibadan,adamawa,maiduguri state daban daban.atakaice Alh muazzam mashahurin mai arzikine na bugawa ga jarida,babu inda sunansa baiyyi yawo ba sannan manyan yan siyasa Suna hudda dashi saboda jama,arsa mutunne shi da Allah bai hore mashi yawan kyauta ba,ba marowaci bane amman kafin ya bayar ana jimawa,baidamu da talaka ba hasalima baisonsu baison su rab'eshi ko kadan,inkinga wani na cin arxikinsa to kuwa abokinsa ne mai kudi irinsa,ko wanda bai kaisa ba.wannane babban kalubalensa. Agefe guda Alh muazzam matansa biyu hajiya mariya itace uwar gida,Allah ya basu zuria itada Alh duk mata guda hud'u,akwai Amina da Haulat zuwairat sai khadija.sai agolarta data zo da ita gidan zakiyya duka yarinyar bata wuce shekara ashirin da daya ba ayanxu sa,ar ni'imah ce kanwar Alfah. Amina da haulat yayyene ga Abdoul-naseer yayinda zuwairat da khadija suke k'anensa,hajiya Ushe itace mata tabiyu ga Alh muazzam kuma uwa ga Abdoul,Allah ya azurtata da samun d'a namiji daya tamkar da dubu ko ma ince miliyan,don shine d'a na farko wajenta dayar macece maisuna ni,imah don su biyu kadai Allah yaba mami. Hakikanin gaskiya zaman lfy yayi karamci gidan Alh muazzam,domin hajiya mariya wadda ake kira da umma wstau uwar gidan tana bala,in jin zafin mami badan komi ba saidan ita kadai ce wadda ta haifa ma Abbi magaji,kuma magajin jarumi mai dakakkar zuciya,mai tsayuwa kan lamarin gidan baki daya,don komi dakika sani game da dukiyar Abbi Abdoul shine ja gaba wajen tafiyar da komi,har su matan nashi komi suke so to shi zasu tambaya,haka kannensa da suma yayyen nashi. Wannan ne ya jawo matsanan ciyar tsana da kiyyyar su wajen umma da yaranta. Bata kaunar Abdoul ko miskala zarratin,yayinda shikuwa kamar ya kwanta mata wajen biyayya,domin wannan umurnine daga mami ta bashi shida ni'imah,cewar kome umma zatayi masu karsu kuskura suyi mata koda kallon banza. Bayan yaran yaran umma daga baya ta d'auko d'an kanwarta rik'o gidan mai suna Mamman.saika rantse anan aka haifeshi,Abbi bai ce don me ba don shi bai cika damuwa da irin wadannan abubuwan ba,sannan rigimar cikin gidanshi yasan da ita amman bai tab'a magana ba. Shiyasa umma take tsula tsiyarta yadda takeso sannan abu na mai ciwo ga halayen Abbi shine duk abunda akazo akace mashi wane yayi,bazai tab'a bincike ba zai yarda kuma yayanke hukunci,ko waye kau amman banda Abdoul,don babu wanda yayiwa yar da irin wadda yayi wa Abdoul.umma tasha kai mashi karar Abdoul cewar yayi mata kaza yayi mata kaza amman kullum maganarsa guda itace "Naseer baxai yi abunda zai b'ata rai na ba mariya,kidai ji tsoron Allah." Shiyasa ta dauki tsawon lokaci batayi nasara akan Alfah ba,don kuwa Abdoul ya zama tauraro mai haske xuciyar iyayensa,mutunne mai fara,a koda yaushe zakiga fuskarsa cikin walwala,ko b'ata mashi kayi zaiyyi murmushi kawai ya wuce bazai tab'a ce maka don me ba yanada jama,a sosai don yana hud'd'a da talakawa sosai,yana kuma sakarmasu aljihunsa ko fita sukai da Abbi marok'a suka rufesu tofa shizai ringa masu b'arin kudi.Alfah Allah yayi shi mai dogon hannu,jin dadinsa da Abbi keyi yasa ya gina mashi Wani kantamemen store dake cikin garinnan nasan zaki sanshi ALFAH STORE SHOPPING MALL ya cikashi da kaya ta ko ina kuma du abunda kikeso na b'angaren more rayuwa inkika shiga Alfah store kin samu. Bacinan ya sakarmashi ragamar kamfanin MK motors duk wasu kudi dake shiga da fita to sai sun biyo ta wajen Alfah sannan suje ga Abbi. Fiyah ta katseshi tace"waye daddy wanna da muka ganshi station." Ajiyar zuciya yayi yace"Daddy babban aminin Abbi ne,kuma d'an uwansa guda tal dasuka fito ciki guda,shima yana cikin estate dinan cikin mai tama." Shiru tayi ta sake cewa meyasa aka samai Alfah." Murmushi yayi yace"wannan sunan daga mami yake,don tace tunda tataso wajen yayarta bayan rasuwar iyayensu take son yaron yayarta mai suna Alfah,sunyi soyayya kamar su cinye juna karshe uwar mijin yauar tata ta zab'a mashi mata.mafarin kenan mami data haifi Abdoul tace inkiyarsa kenan Alfah shikenan Abdoul-naseer ya b'ace saidai Abbi kawai ke kiransa da ABDOUL-NASS,wlh fiyah Abdoul ya fuskanci bak'in ciki ta dalilin umma,don kau umma tun Abdoul yana cikin ciki take son ganin bayansa Allah bai bata dama ba,domin kuwa Allah yace sai yafito saiya rayu rayuwa mai kyau.Abdoul yana son y'an uwansa yayinda sukuma babu abunda suke son gani irin mutuwarsa,don mahaifiyarsu ta riga ta dasa masu tsamarsa tun suna y'an kususan su,haulat da Amina sunyi aure suna gidan mijinsu sai zuwairat da khadija da kuma zakiyya. Ana cikin wannan hali fiyah Abdoul ya fad'a soyayya da zakiyya diyar umma agolarta data zo da ita gidan. Wanda zakiyyar itace ta fara nuna mashi tana sonsa,don tunda tazo gidan Allah ya dasa mata kaunarsa,amman komi suke yi babu sanin uma,ab'oye sukeyin kaunarsu ni kadai na san da wannan soyayyar." Sake katseshi tayi da cewar "yah malik ina kai banji taku alak'ar ba,nai tunanin kaima d'an gidanne." Ruwa ya d'ansha sannan yace....... Mrs bb ce Mom muhseen. *Comment and share it* [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........11 "Banda wata alak'a da Alfah sai abota ko nace amintaka,na had'u da Abdoul wajen dawowarsa daga taron siyasa ya wakilci Abbi wajen taron rantsar da wani minister.abunda kuwa ya had'a mu shine Richard card na waya,go slow ya tsayar dasu nikuma Ina bin layin layin motoci ina masu tallar wani sabon layi da kuma katin waya,Ina daidai motarsu naji drivern yakirani abunka da maison ciniki aguje na iso har ina ingije wani mai Babur,ya dunga antayo man zagi nibama tashi nake ba,cinikin da kekirana nake ma hanzarin isa gareshi.Ina shashsheka nace. "Gani" Driver yajuya baya yace"yallabai gashi nanawa zai mik'o." Abdoul dake baya hakimce yasha wat a arniyar gizner yace"anso duka kona na wane." Jinai kamar anmun gafara,don kuwa wannan cinikin yayi masifar yimun dadi Ina rawar jiki na ciroshi duka na mika mashi daman na 5k ne kawai. Maimakon naga 5k fiyah sai naga 15k kankace me tuni idona yacika da kwallah,godiya zanyi Amman baibani dama ba yamiko min card dinsa yace on Tuesday inasamai maitama around 6:30 haka suka barni da farinciki kamar me,ranar har kukan dadi nayi. Don ban tab'a samun kyauta makamanciyar irin wannan ba,na shigo Abuja cikin bakin talauci da rashin gata,nine buga can nine buga can,haka nake rayuwa. Shago na Kama Ina za man haya,duk bayan wata uku nake biyan dubu goma sha biyu. Aranar da ana gobe zanje wajensa, sai naga dare ya jima bai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101