Chapter 54
Chapter 54
naki to kinyi daidai kije kiyi duk abunda kikaga yadace da rayuwarki" Tatashi zata shige daki don ranta yabaci da fiyah sosai. Rarumo kafafun mamar tai tana kuka"kiyi hkr mama wlhh kinji na ramtse maki babu wanda nakeso,kuma babu wanda nake tsayawa dashi atiti,kiyarda dani idan da akwai aibazan yarda kisan halin danake ciki ba,nidai kiyi hkr idama don makaranta ce kike ganin ina fakewa da ita ina haduwa sa wasu to bazan sake fitaba,shikenan sai hankalinki ya kwanta mama" Janye kafarta tayi ta shige daki tabarsu da yesmin,kukan ta cigaba dayi tana data sanin yanayin data shiga har haka ya jawo fitina itada mahaifiyarta,abunda suka jima basuyi ba irin wannan fadan ita mamar. Yesmin keta bata hkr tana cewa"kiyi hkr Adda mama ba tayi bane don bata sonki ba,ita don tarbiyyarki takeyi wani idan ya ganki xai maki wani kallo na daban,kiyi hkr karki kullaceta." Kallon yesmin din take tashare kwallarta tace"kintaba ganin da nagari ya rike uwarsa mahaifiya garai,duk girman laifinta kuwa,don haka kibar cemun haka." Tatashi tashige daki tana shirin kwanciya,amman kalaman mama na mata yawo akai,hakika mama iyakar gaskiyarta ta fada,kuma tana tsoron lalacewar tarbiyarta shiyasa. Wayarta tadauko tana ma malik text,sai taga gara takirashi tayi mashi bayani. Ta gama komi ta kwanta yesmin dakin mama zata kwana,shiyasa ta sake ta kirasa. Lokacin sun rabu da Dady shikuma yana zaune gefen Alfaj daketa bacci,kallon wayar yayi ya yi picking. "Yaya malik ina wuni" Shima muryarsa tadan disashe yace"lafiyalau qanwata ykk yagidan" "Yaya malik baka da lafiyane?" Ajiyar xuciya yasauke yana kallon Alfah yace"dasauki dai qanwta,Alfah ne ba lafiya yayi doguwar suma daker akasamo ransa,Qanwata ashe Abdoul yana da wani ciwo bamu sani ba,nan yayi mata bayani atakaice,kuka yaji tanayi kasa kasa.shiru yayi yana tunanin daman sai haka ta faru barinta yayi take kukan ta samu natsuwa. "Yaya malik don Allah idan Allah yasa ya farka kace ina mashi sannu,zanso nazo na ganshi amman yaya malik Im sorry to say bazan sake zuwa inda kuke ba,domin kare abunda zaizo yaje mamana ta fara harbo jirgina,har tayi dogon fushi dani.kasan kuma fushin iyaye akan y'ay'ansu masiface babba,don Allah yaya malik kuyi hkr da rashina nayi iyakar abunda Allah ya bani iko,sauran kuma na barshi gareka da Zakiyya,ku karasa ni banyi don wani cikinku yabiyani ba nayine domin Allah da kuma tausayin sa daya shigeni ganina dashi na farko.don haka kuyi hkr zaku daina ganina,amman kila mun ringa gaisawa don gujewa fushin mamana" Hakika baiji dadin wannan labarin ba,don ya sake dagula mashi lissafi baiso ba yaso ace komi anyishi da ita,amman kuma iyaye suna gaba dakomi,shima mai goyon bayanta ne akan hakan. Numfashi yaja yace"bakomi safiyya ai aiki kam yazo karshe insha Allah,kin riga kinyi komi da kikai alkawari insha Allah ladarki naga Allah,haka nima daga gareni zan baki tukuici badan biyanki zanba,saidan yabawa da kokarinki don kinyi abunda dayawa mazan ma bazasuyi ba,ki sadaukar da lafiyarki,lokacinki kudinki da jin dadinki duk aka Abdoul ya dawo cikin hayyacinsa,to Alhamdulillah mungode Allah ansamu nasara don haka karki saka wata damuwa,Abdoul yagama dawowa *ABDOULNASEER ALFAH* Dinsa kuma insha Allah da kafarsa zaizo maki godiya,don haka ayima mama biyayya sannan abata hkr har sai ta sauko,kinjiko kanwata." Hawaye take sharewa sai takejin sunayin bankwana ne,kamar bazasu sake haduwa ba har abada.ga wani nauyi da kirjinta ya mata Abdoul take hangowa ranar da suka hadu Asibiti an sallami zakiyya,shigarshi cikin taci dinta da abunda ya faru wajen sai kurin taji kuka ya kubce mata. Shiru yayi yana saurarenta tabbas safiyyah ta kamu da soyayyar Alfah,Amman ita kanta bata sani ba don wannan kukan yasan duk akan shi takeyi,saiyaji tausayinta ya kamashi. "Kuka kikeyi safiyyah,miye abun kuka." "Yaya malik ka kula dashi don Allah,karka bari wani abu ya samai kagani baya da kowa saikai,kaine yake gani yana jin dadi,kamun alkawarin kulawa da shi yadda ya kamata." Baisan murmushi ya kubce mashi ba yashafa kanshi yace"indan wannan ne qanwata namaki alkawari,kidauka ma anyi angama kuma ai zamu ringa gaisawa time to time ko" Muryarta kasa kasa tace"insha Allah" "Oky to share kwallar,ki maida komi ba komi ba ai daya tashi zuwa safe ma zan kiraki saikiyi mashi yjikin da kanki ko" Shiru tai tana ajiyar xuciya.share maganar tai tace"yaya malik zan rako ni,ima nan asibitin yau mun hadu taje kawowa baba abinci inji mami munyi magana da ita har nai mata alkawari. Kawota wajen yayanta don haka idan zanje exam zan taho da ita na ajiyeta natai,kai saika sata taxi ta koma gida.wane asibitine kuke" Jinjina kokarinya yake lallai masu xuciyar fiyah sai antona. Gaya mata sunan asibitin yayi sukai sallama tana cewa yaje ya kaima daddy m.card dinnan komi kenan shiyasan yazaiyyi. Haka suka rabu kamar tabiyosa taganshi. Malik ya ajiye wayar yana nazarin hirarsu,duk abunda suka tattauna akan kunnensa,tas yaji wani babine mai girma ya budewa yarinyar cikin birnin xuciyarsa,hakika ita din wata fitilace mai mugun haske ga rayuwarsa,shin dame ya dace yayiwa wannan yarinyar sakayya.ta kawo cigaba arayuwarsa tayi tsaye tsayin daka akan rayuwarsa ta baya,ta sadaukar da ranta da kominta akansa,duk don ya dawo da rayuwarsa kamar baya,tana son dawo mashi da kimarsa daya rasa. Bai nuna ma malik ya tashi ba,cigaba yayi da kwanciyarsa yana nazarin kalamanta da yanayinta. Har wani sabon baccin yasace shi. Washe gari da safe duk wasu ayyuka da tasan tanayi tatashi da wuri ta farasu,don karfe tara da rabi time din shigarsu yaje farawa.ko yesmin bata tada ba ita kadai keta shige da ficenta tsakar gidan,ta share tas ta dora kalaci ta hau wanke wanke ahaka har ta gama ta dama koko ta juye ga plax,sannan ta shiga tuyar fanke,daman kuma tunjiya da daddare tanajin sanda mamar ta fito ta yi kwab'in. Tana gama wa taje tashiga wanka sai lokacin su mamar sua fito,yesmin nata kallon gidan tana mik'a. "Mama mun makara yau,duba kiga Adda duk ta gama ayyukan" Mamar ta dauki buta ta nufi bayi tana cewa"ta kyauta Allah yayi mata Albarka." Inda kurin bata gyaraba wajen kiwon kajinsu da dabbobinsu shine yesmin taje ta gyara shi. Duk sungama komi har wanka kowa yayi dalha yashigo yana gaida mama ta bashi kalacin baba yayi gaba kafin su gama nasu su taho. Fiyah tayi sukuku tunda ta gaida maman ta ansa bata sake cewa komi ba,duk jikinta asanyaye take break din Allah sarki uwa da diya sai mama taji duk babu dadi,yadda safiyyar ta saba da karkaina taringa karadi sa surutu tana jansu da abun dariya,duk sai taji tabata tausayi. "Kike ma Kalacin wani irin ci,kina duba lokaci kuwa" Inji maman. Yesmin tace"Adda tara saura minty ashirin fa" Kamar mai ciwon baki tace"na sani ai sai tara da rabi muke shiga." Feea ce tayi sallama duk suka jiyo suna ansa mata,idon fiyah akanta fuskar rafeea cike da annashuwa,kallonta taitayi suna gaisawa da mama har ta jiyo kanta tana cewa. "Kefa nabiyo mawa amman baki gama ba,zafa mu anshi exam card kar aje rabawa bama nan" Kasa cewa komi tayi taringa tura fanken tana binsa da ruwan kokon har ta samu suka shige baki daya,tatashi ta dauko abayarta da jikkarta,onready wayarta na ciki da duk abunda zara bukata. "Ki cire duk wata damuwa aranki kiyi jarabawarki cikin kwamciyar hankali,Allah yabada sa,a yatsare hanya sai kundawo kilan sanda zaki dawo muna can asibitin" Tace"to mama" Bin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101