Chapter 32
Chapter 32
sit din gaban ya silale ya kwantar da bayansa da kansa,idonsa rufe ruf. Jin malik yatashi motar yasa shi magana batare daya iya bude idonsa ba . "Kasan nan zaka barta meyasa kazo da ita?" Daman haka yake jira ya bude motar yafota ya iso wajenta magana zai mata ta juya ta barsa wajen. Gudu gudu sauri sauri haka take hadawa don isa inda zata samu abun hawa...........jitai kamar tana bisa iska zuwa sadda zata dawo cikin hayyacinta saidai tajita anyi jifa da ita cikin mota.........sannan suka tafi. Wai ashe Alfah ne yabiyita yadaukota kamar yar tsana yasata motar,don yayi imanin kafin ma ta isa inda zata samu taxi sai kafarta ta kusan cirewa don ciwo........shiyasa kawai yaje yadaukota don idan suka tsaya janjani zata bata masu lokaci,shiyasa kawai yayi mata haka. Kuka ta fashe dashi don tama rasa me zatayi tama hana zuciyarta yin wani tunani ta kuntace ta waje guda,babu mai magana amotar don su ukune yaran sa sun wuce company da kayan d suka duko. Sutin kukan kurin kakeji mai cike da bakin ciki kafin ta gaza jure k'un cinta take cewa. "Allah ya isana ban yafe ba mug.........kasa idasa mugun tayi tana shashshekar kuka Alfah dake gaba kwance idonsa lumshe jinta kurin yake murmushi yayi mai sauti har saida malik ya juyo yana kallonsa, "Malam Kalli gaban ka karka zubar damu." Dole malik ya kauda kai don shi yau Alfahn duk ya zamema sa kamar wani sabon mutun. "Haka kawai ka samun wana kazamin bakin naka mai shan giya,gashinan ji nake kamar zanyi amai wlh kaida Allah ban yafe ba." Sika sakejinta tana fadar haka. Bai motsa ba yace"naga dai alamar giyar nan sonta kike kina sha,awar d'an d'anawa karki damu zan baki kisha." Bata sake magana ba har suka isa gidan su Malik,don babu abunda taki jinin ji daga garesa irin yace zai bata giya,tasan kadan daga cikin aikinsa ne tsaf zai danneta ya dura mata ita.wai Allah da tashiga ukunta kau. Fitowa tayi tana sharben majina ta wuce titi bata saurari kowa ba ta tari taxi ta wucw gida.........koda taje anty tace ta huta tayi masu girkin dare cewa tai bata da lfiya,dole sai Mai aikinsu ce tayi masu. Mrs bbce Mom muhseen 09034722970. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.......... Wannan dare safiyya bata iya runtsawa ba ta tayi kiskuren runtse idonta sata ganshi yana lashe mata kumatu,dandanan zata ji tsikar jikinta tatashi tayi zunbur ta tashi zaune ta rabka tagumi..........ga baccin yana cinta amman bata son ganinsa cikin baccita,meyasa ya tsaya man garai ni fiyah?meyasa wulakancin sa bai tsaya man sosai irin yadda salonsa ya tsaya mata ba.hatta kayan jikinta yau ta gagara musanya su saboda kamshinsa dake jikinsu,dandanan Allah yasa mata kaunar turaren.daga ta mirgina can saita mirgina can har dai mulmulowa tayi kasa bata ma san tayi ba saida tajita tim kasa.........dafe kai tayi tana mamakin kanta wai meke damuna ne yau,akan wancan dan rainin hamatar na ke duk wannan,aa ba zai yuwuba shidin banza da wofi wlh saina yi baccina yau insha Allah. Koma wa tayi kan gadon tana sake wata adduar tana gama wa ta tofe ko ina ta shafe jikinta ta kwanta. Duk yadda take dambe da zuciyarta abun yaci tura,amman haka ta daure ta runtse idonta gam da tsiya sai baccin ya dauketa. Ganin babu sarki sai Allah yasa tatashi tayo Alwallah tazo ta fara sallah,saida tayi raka,a shidda sannan tadauko qur,anin ta tafara jero karatu cikin tsantsar tajwidi.........saida ta shafe akalla awa daya da rabi sanan ta ajiye ta koma ta kwanta.......dan danan baccin yazo ya sureta. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Tunda suka shigo ya wuce ya watsa ruwa sanan yyi sallar magrub a cikin dakinsa yunwa yakeji da gajiya baison yin magana kwata kwata yanzu,soyake ya kwanta yana bukatar tunani. Yasan malik inzai shigo zai taho masu da abinci tunda kukun nasu baya nan. Kasa ya kwanta yana filo da hannayensa idonsa rufe kafafunsa ya dora su bisa wani dan table,yayi crossing dinsu yana girgiza guda. _haka kawai kasa mun wannan qazamin bakin naka mai shan giya gashinan ji nake kamar zanyi amai wlh.kaida Allah ban yafe ba_ Murmushi ya subuce masa mai shegen kyau,har fararen hakoransa kyawawa suka bayyana. Kafin Annurinsa ya fara b'acewa saboda kalamanta na farko. _ur highly welcome drinker guy_ Runtse idonsa yayi yana jin zafin kalamin cikin ransa,tabbas yasan ankirasa da wadanda sukafi wadanna ada bama da ba har yau akwai masu yi mashi wannan kallo,amman zuwa sadda ya rikice ya daina jin zafi da dacin kalaman shine lokacin da ya kulla damarar shanta.daga lokacin baya jin haushi baya jin radadi don ance masa mashayi.........ammman yanzu da yaji din rad'in kansa ya barta bari na har abada,sai yaji kalaman basu dace dashi ba,Allah shike ganin zukatan bayin sa amman yasan badan wannan yarinyar yabar giya ba,saidai yasan cewa kalamanta suntaka rawar gani wajen taimaka barinsa da ita,don tunda yaje Australia daya shata ma sai yayi amai kuma sai yayi masassara,lokacin ya dan gana da asibiti don radin kansa wanda shi knsa yayi mamakin ganinsa gaban likita wai ya kawo kansa,bacin kullum hanyar da zata lahanta rayuwar yake nema. Amman baisan meyasa yanzu yakejin yashirya yin rayuwa mai kyau koda shokadaine cikin duniya,yaji haushin kansa lokacin da dr yohana yake gaya masa cewar wine din takai limit din da bata kara iya daukar hunhunsa,saboda ta mashi rauni a wajen wanda muddin ya sake yasha ta ko yasha lemo mai gas yana iya rasa ransa,haka zalika ya hana shi shan abu mai zafi sosai da kuma mai sanyi sosai,don zasuyi mashi lahani........sannan abun daya sake bashi mamaki da haushin kansa wai arne da baisan kansa ba wanda bai yarda da Allah da manzon sa ba yake mashi nasihar zaman duniya,da kuma abunda zaiyyi maikyau da marar kyau. Ranar yayi kukan da tunda yabar gidan iyayensa baiyyishi ba,yayi nadama da dana sani yafi akirga,saida ya kwana biyu baifita ma aikin daya kawoshi ba. Mafarin ya fara ansar magani daga shi dr yohanan yace masa duk bayan wata uku yazo aduba shi don zai iya yuwiwa amai aiki,idan kuma yana warkewa to basai anyi aikin ba......duk sanda ya tuna wannan lamarin saiyaji kansa yana sarawa,hakika yayi sake yabari shaidan da sherin zuciya sunyi galaba akansa.meyasa abunda ake masa kallo dashi bayyi yunkurin kiyaye kanshi dashi ba,yanzu kenan da Allah bai sa ya bar sauran shaye shayen dayayi ba Allah kadai yasan abunda zai faru da rayuwarsa.da mezaice ma mahaliccinsa baida bakin da zai iya kare kansa. Hawaye suka silalo mashi yaji wata kaunar malik ta cika mashi zuciya,tabbas malik abokine na musanman duk wanda yasamu aboki amini irinsa yadace yayi dacen da har tutiya ma inyayi babu laifi. Don yasan irin wuyar dayasha kafin ya rabashi da sauran kayan mayen.sannan binciken dayasa akai mashi ya nuna mashi cewar shine ya kawo wannan yarinyar cikin rayuwarsa,don ta taimakeshi yadawo dashi daidai..........meyakai wannan arayuwa inda wanine fita sabgarsa zaiyi yaje koma me zayyi yayi aiba dan uwansa bane ko wami nashi.........wannan dalilin yasa yaji zuciyarsa tayi sanyi tayi cool dinda baisan rabonsa dajin haka ba,yaji natsuwarsa na dawowa yaji happenes dinsa cikin kaso dari kashi arba,in yana dawo wa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101