Chapter 12
Chapter 12
wadda yayi duk da dai basanin abunda ya faru dashi tayi ba. Cikin sanyin jiki tace"insha Allah baba zan kiyaue kasa mun Albarka to" Murmishi yayi yace"sofiyna kenan to Allah yayi maki Albarka ya baku miji na gari." Yesmin ta shagwabe fuska tayi tace"baba nifah to." Dariya duk aka yi mata yace "kema Allah yayi maki Albarka ya baki miji nagari." Tana jin dadi tace "ameen baba." Bayan sun koma d'aki ta shiga kiran no d'in malik,lokacin ma yanata aiki don cikin satin yake saka ran zuwa switzerland saro kaya. Alfah yana zaune kan kujera idonsa a lumshe ya shiga duniyar tunani,ahankali kuma zaka ga hawaye suna bin gefen idonsa,gorgiza kainkawai malik yake don baisannya zayyi da Alfah ba,yakasa daukar kaddara yakasa hkr da rayuwar ya ansheta ayanda tazo mashi. Wayarsa yaji tayi kara ya dan kalla yaga babu suna kamar zai share saikua ya tsaya da aiki ayakin ya dauka, tare da sallama. Tana kwance lokacin ma harnyesmin tayi bacci don bata da wuyar bacci . Itama cikin cool voice d'inta tayi mashi sallamar. "Assalamu alaikum,ina wuni yah malik." Jingina yayi daga jiin kuerar yaa maida hakalinsa kan wayar don yamaso saiwaye. "Wa,alaiki salam wake magana pls." "Sofiyya E-ladan." Murmushi yayi yace"okyy fiyah ce,ykk yakika koma gida." Idonsa nakan Alfah da har lokacin bai bude idonsa ba kuma ba bacci yake ba. "Lafiya lau wlh yah malik ya na barka ya kuma rikitacce abokin ka." Murmushinsa ya fidda mai sauti yace"bari nabaki shi sai ku gaisa." Zaro ido tai kamar yana gabanta tace"rufan asiri ina zaman lfy wannan ai saika yah malik,wazai iya da wannan rikicin." Dariyarsa ta fito har Alfah ya bude idonsa yana kallonsa "kin cika tsoro wlh,amman soon zaku saba yanzu ya zai muhad'u gobe around 4:00." Ajiyar zuciya tayi tace "inada test lokacin yah malik amman mezai hana da safe zuwa yammar." "OK hakan ma is ok 10:am yayi mki ko." Murmushi tayi tace "yes yayi insha Allah amman ina zan sameka." D'an shiru yayi yana kallon yadda alfah yake mashi kallon tuhuma yace"zan maki text da safen." "OK yah malik sai da safe zan kwanta." Sallama sukai ya ajiye wayar har lokacin idon Alfah na kanshi yasan soyake yayi mashi bayanin wacece amman miskilancinsa bazai barshi ya tamaya ba,shima kuma sai ybiye shin yayi shiru ya cigaa a aikinsa. Zuwa can ya tashi cikin fushin sa na farillah yayi ball da table d'in dake gaban sa ya wuce bed room d'in sa. Malik yace "Allah ya yaye maka ya kawo maka sauki cikin lamarinka." DON ALLAH KUYI HKR HIDIMAR SUNA MUKA SHIGA SHIYASA BAKWAJINA KULUM,AMMAN DAMUN GAMA INSHA ALLAH ZAKUJINI KUYI MALEJI DA WANNAN. MRS BB CE MOM MUHSEEN. [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* *Wannan page d'in nakune masoyana,inhar kinsan ke masoyiyata ce mai nuna kauna gareni to nakine na sadaukar dashi gareku,saboda irin soyayyar da nake samu daga wajenku,Allah yabarmun ku ya kuma kara mana kaunar juna,kuma baby humaira tana gaida kowa da kowa da irin aduar da take samu daga gareku.* 🅿️.........10 Fiyah ta gama komi yau da safe kasancewar yau Wednesday baba baya fita da wuri sai takwas na safe koda ya fito yaganta har takwas bata yi shirin fita ba yace"sofiyya yau babu makarantar ne." Tana sauke tukunyar danwaken da zasu ci da safen tace"baba ina kwana" Ya ansa cikin kula tace"aa baba akwai amman sai ten saboda malamin bazai zo ba da zai ma na seven to nine thirty baida lafy" Ta gilla mai karya nashi ta zubo mashi da kununsa na gyada data dama,yana kalacin suna hira har sadda mama ta fito daga d'akin sa ta gama gyara mai,itama ta zauna aka hau hirar tare yesmin ce cikin uniform na makaranta ta fito tana ma su saita dawo,naira dari yabata ta yi break sannan ya bata dari uku tayi abun hawa. Godiya tayi sosai ta fita tana d'aga ma addarta hannu. Shima tashi yayi bayan ya gama yaba fiyah kudin ta itama ya yimasu saiya dawo suka bishi da addua,mama tace"tunda bazaki makarantar ba ki tashi ki kwab'a alkubus yayanku yana tafe yace mun kiyi mashi." Gabanta ya fad'i don sunyi da malik zasu had'u karfe goma,intace saitayi wani alkubus bata san ranar fita ba,cikin murna tace"mama dagaske yah zaizo aikuwa zanso in shirya mashi abinci wlh,amman karfe goma inada lecture wlh kuma kanta zai mana test gobe,bacin haka aida bama zan je ba." Maman tace"to abunda zai ai kafin lokacin yayi tashi ki d'ebo fulawar ki kwab'a mun,saina idasa nima da fita zanyi inje gidan yaya balara ba,ingano hasana bata da lfy." Tashi tayi ta je ta dauko kayan had'in tazo ta fara kwab'in tana cewa"meyasa meta mama" Tace"kinsan tana da iska to daga makaranta aka maidota sun matsa mata wlh,basu bari ma tayi karatun karshe dai kilan day zata dawo." Nan suka ci gaba da hirar suna jajanta abun,hasana diyar yayar mamace dake can wata unguwa bama nan cikin abujar suke sosai ba. Karfe tara da rabi tayi wanka ta shiga shiryawa doguwsr riga tasa mai dan karen kyau,don Antynsu ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta tare masu sitira,duk da shima baban ba baya ba duk salla kala biyu yake masu,jamila ta kara masu kala gida da gyaluluwa da takalma,har mada kayan kwalliya da turaruka shikuwa jalal shike dauke duk rabin hidimar gidan,yana da kokari sosai don inzai zo daga kaduna d'unkuna yake zoma baban dasu da kuma takalmomi kayan abinci da dadai sauransu. Tana cikin saka turare text d'insa ya shigo wayarta,saurin ajiye turaren tayi taduba. _ina silver bird place guiding yanzu haka ina jiranki._ Shiru tayi tana tunanin yadda zatai ta isa wannan wajen,anya Malik yasan kuwa inda yake cewa ta samai,wannan wurin ai ba na irinta bane,kuma kudin taxi kansu sun isheta don dari bayar bata kaita ta maidota..........abayarta milk ta saka tana jimamin abun,wsta yar jakace mai kyau ta dauka ta fito mama na tsakar gida tana yankan alayyahu na taushen da za,ai tace"har kin fito." Tace"mama don Allah in anshi dari uku wajen dalha,hand out zan siya na manta ban gaya ma baba ba." Kalonta take kafin tace"shikenan kije ki ansa allah ya kiyaye kiyi addua idan zaki fita." Sallama tayi mata ta fita ta anshi kud'in ta wuce. Taxi ta tata bakin titi ta gaya mai inda zai kaita saoda sukai ciniki sannan suka tafi. Sadda suka je get din arufe ta rasa yadda zatai don wajen yana da k'a idoji wayarta ta fiddo ta mashi text cewar ta iso yazo yayi mata iso. Tana nan tsaye na wasu minty na sannan taji an bude wajen,malik ne yasha kananan kaya sunyi masifar ansar jikinsa,don shima malik badai kyau ba,murmushi yayi mata yayi mata nuni da cewar ta taho. Itama ansar murmushin ta bashi ta isa inda yake suka jera har cikin palace din,waje ya had'u yahad'u iyakar had'uwa,fad'an yadda yake b'ata bakine don wajen sai wane da wane suke zuwa don wajene na shak'atawa ne. Wajene na musamman ya sauketa rumface wayayya anjera kayan cinye cinye da lashe lashe. Zama tayi shima ya zauna yana kawata fuskarsa da murmushin shima,lemu ya samata tare da tura mata plet d'in snacks
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101