Chapter 46
Chapter 46
tayi taga sunan malik,da dai kamar ta share amman sai xuciyarta takasa yin hakan. Ahankali ta dauki wayar tana sawa ga kunnenta. "Qanwata ban sanki da haka ba,yaushe kika b'aci da fushi ban sani ba" Turo baki tayi kamar yana gabanta ta haye kan gado tana jingina bayanta ga allon gadon cikin sassanyar murya tace"yaya haka ma zakace bacin,bacin abunda akaimun har zaka ce kar nayi fushi" "Ni bance karkiyi fushi ba,amman saiki yi mashi uziri abunda ya sakashi yin hakan kinsani meyasa bazaki mashi uxiri ba," Sake sunburo bakin tayi kamar zata yi kuka tace"yaya malik Amman basai yazo ya ban hkr inshiga ba amman fa gabansa na tsayar da taxi natafi baiyyi yunkurin dakatar dani baya kyaleni natafi" "Sorry qanwata zaibaki hkr Amman saiya samu sauki" Gabanta yafadi rasss "yaya malik baya da lafiya ne" Iska yafesar yana gyara kwanciyarsa yace"fadowa yayi daga kan gado ya suma xuciyarsa ce ta halba numfashinsa ya tsaya,amman ya samu sauki don gashi can likita ya saka mashi oxygen.xuwa safe zai farka cikin koshin lfiya insha Allah" Kwalla suka zubo mata cikin kermar murya kiris yarage ta fashe da kuka tace"yaya malik ka tabbatar yana lafiya,ya samu sauki sosai yaya malik nice na bata mashi rai ko?wlh yaya malik ni banson hakan zai bata ransa ba kuma wlh ni kai nakoira bashi ba,amman sai kurin naganshi yazo.......kasa cigaba tayi da magana don kukanta ya kusa fitowa" Jinjina kai yake yajiyo sautin kukanta tabbas safiyya ta kamu da abunda yake zargin cewar shima Abdoul din ya kamu,duba da yadda duk yabi ta rude ta tashi hankalinta. "Kuka kike fiyah,miye na kukan to?bakison wani abu yasamai ne" Shashshekarta ce ta fito fili takasa ansashi murmushi yayi yace"ki kwantar da hankalinki babu abun da zai sameshi,kiyi mashi Addua daya farka da safe zan kiraki sai kimasa ya jiki ko" Shiru tayi tana jin kamar tayi tsuntsuwa tazo ta ganshi,amma bata son Yaya malik ya fahimci kotana jin wani new feelings akan Abokin nashi. "Kinyi shiru qanwata" "Saida safe yaya malik zan kwanta" Murmushi yayi yanajin ina mace shine yayi dacen samun wannan tsadaddar yarinyar mai kunya da tarbiyya. "Shikenan qanwata Mma i promise u immediately daya tashi zan kiraki kizo ki ganshi,sannan zakiyya na asibiti ta samu sauki itama da safe ko zuwa yamma zata iya farkawa ai zaki xo ganinta ko saimuyi magana daganan" Daker ta iya ce mashi "oky,goodnight" Ta sauke wayar tana silalewa saman gadon tana jawo filo tana kwakwumeshi ga kirjinta. Plssss kuyi hkr gobe ba zaku samu posting ba saboda muna aikin suna sorry plsssss nasan ba zakuji dadi ba,amman inhar nasamu lokaci zanyi maku Pls don't share it i beg [9/17, 3:41 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* FOR SALE 300 VIA KISIYA KISHA KARATUNKI CIKIN NATSUWA. GA MAI BUKATA TA TUNTUBI WANNAN LAYIN 09034722979 WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ALFAH FANS GROUP* 🅿️.........33 "Anty bazan iya zama har kigama wanka ba,kinga exams ke gareni ina bukatar inje na natsu gida nayi karatuna,kiyi hkr nidai kibarni natai tunda kinga wlh yya muhseen baxai barni nasake ba inhar yasan ina nan gidan gara dai na tai can gida." "Shikenan,Bari na dauko maki naman ku kowa na mashi kullinsa don haka babu wata rigima,halinki nasani kan nama idan na sake na hadaki dana yesmin wlh kwararta xakiyi,har gara inkeda mamane wanan tana iya ma raba nata biyu takara maki ita ko baba,don naga dagaske kin anshe ma yesmin fadarta" Dariya fiyah tayi tana yiwa little fiyah rawa tace"uhm shedar da zakiyi mun kenan Anty?kuma ai dama can fadata ce tana zuwa naga alamar da niyar juyin mulki tazo saina zage don kar na rasa matsayina,amman duk da haka Anty Ai yesmin tafini fada aji wajen mama,da dai babane wannan nasan bai bari abunda zai bata raina,don ta nama ma saiya hkr da nashi yabani incinye" Tafada tana dariya antyn dake cikin daki tace"wlh karma kifara,kowa anbashi nashi kiji tsoron Allah kibarshi yaci,haba safiyya wlh nasan zaki aikata don Allah karkiyi haka" Tana dariyar tace"to inbaki so inyi nawa yafi na kowa yawa aradu" Fitowa tai da babar lea viva ta ajiye gabanta,ta fido wata bakar leda cike tab daker aka kulleta tace"wannan na kine kici kiyi kashi don ubanki,wanna kuma na mama gashinan nayi alama,wannan kuma na baba shima ga shedar shinan,inna balaraba tunjiya suka wuce da nasu banda su anan ciki,ga na yesmin ga na yaya jalal asaka mashi akitse tunda ya tafi randa ya dawo sai yaci" "Kai Anty,saikace dole nidai gaskiya ki kyale yaya kiban shi in cinye in yadawo sai inbashi hkr" "Uban hkr zaki bashi wallahi karnaji wannan labarin kinji dai na gaya maki,kodayake ma bari kigani." Ya daukeshi daga cikin sauran tace"nizan ajiye mashi dakaina" Suna cikin haka uncle ya shigo yace"safiyya badai tafya ba?" "Wlh uncle tafiya zanyi,inje na natsu infara karatu lokaci yana kure mana" "To gama bari nazo na saukeki,muhseen baya nan da nasaka ya kaiki." Aranta tace"nagode Allah" Sunyi sallama da Anty jamilar tana tayi mata godiya akan hidimar da tai mata,kamar zatai kwallah haka taji don dan zaman da sukai saitaji inama taita zama da qanwar tata,koba komi sunyi wasa da dariya kuma ta rage mata ayyuka,amman tasan baba bazai yarda ba kuma itama fiyar tafison kusada mama da baban. Suna tafiya yana janta da hira tana biyesa,har yazo kan maganar abokinsa. "Nikau safiyya ina kika san Alfah,ayadda na fahimta ranan ba bankeki yayi ba,karki boyemun inason in sanine saboda wani dalili" Saitaji bazata iya boyewa uncle din nata ba ta sadda kai ta fara bashi labarin haduwarsu da kuma dalilin shigarta rayuwarsa,har kawo abunda ya tsayar da ita bata dawo gida da wuri ba,harda cigaban da ya samu tadalilinta. Shiru yayi yana jinjina kai kafin yace"niyyarki mai kyauce safiyyah,amman kinsan hakan akwai hadari ga rayuwarki,wannan aikin namiji ne ya dace dashi ba ke mace ba,saboda yadda amana tayi karanci cikin rayuwar nan,kuma nima nasan da wannan labarin,shiyasa na tambayeki tabbas nima raina ba yadda Alfah zai aikata haka ba,duk da kowane lokaci mutun zai ita canza wa,amman da kamar wuya gaskiya.don haka ki kula ki kiyaye ya dace tun farko ki sanar da mama koyaya dai in wani abu yabiyo baya duk da ba fata ake ba,atleast tasan mekike ciki" "Uncle wlh bazata barni na taimakesa ba saboda abunda ya faru tsakaninsu da mahaifinsa,gabace maitsawo tunma ba aifemu ba muduka,abun ya faru shiyasa duk unguwar babu mai kulamu bamu banda yan tsirarunsu,shiyasa na boye abun babu wanda yasani cikin gidan mu don kar ahanani kuma Alhamdulillah komi yana zuwa da sauki nanda dan lokaci komi ya kammala,nima inhuta in samu natsuwa." Murmushi yayi baice komi ba don yayi imanin shigarta rsyuwar Alfah baya nufin ta fita,don ga dukan alamu ita dashi kowa yana jin wani abu game da dan uwansa,shiyasa bai bada karfi wajen ganin muhseen din sa ya sameta ba,yana da burin ta dawo da abokin nashi cikin hayyacinsa,kuma zaiso ace sunyi aure sauran halayyarsa ta idasa daidaita shi,shiyasa ma zaifara nema wa muhseen din Auren yesmin,don bazai so ace ya rasa daya daga cikinsu ba,don yarane da suka samu kyakkyawar tarbiya yadda ya kamata. Sauketa yayi suka shiga ya gaida mama lokacin baba bai dawo gida ba,yaba fiya dubu goma ladar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101