Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 74

Chapter 74

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,281 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

aka daureta aka rufeta adaki sannan,amman taki shiru itace keta wancen ihun,ankiraka yafi sau ba iyaka yallabai naka dauki waya ba kagafarcemu" Murmushi yaga Abbi yanayi cikeda jin dadi yace"daddaden labari kana da kyauta ta dubu dari,ka tuna man da safe ban kuma ce uban kowa yashiga ba kunajina ya fada yana nuna sauran security din dake wajen. Dady yace"karkayi haka yaya..........Abdoullahi idan baka son raina yabaci kaimun shiru kama hanya kuma ka nufi gidanka iyalin ka najiranka" Ya wuce part din su Mami yanajin wata matsananciyar kewarsu ita da ni,ima.har tun tube yakw ya shiga jikinsa har wata tsuma yake,falon shiru sai karar Ac kallon falon yayi furniture's duk sun lalace,gabaki daya ma part din ya Lalace babu kulawa bawai rashin tsafta ba,aa komi ya lalace yana bukatar canji,wasu kwalla suka xubo mashi. Sako da lungu na part din yake dubawa yana hawaye. Motsi yaji kitchen ya leka mami ce keta kokarin sarrafa yar cus cus din data rage masu rabin leda tayi ma dady waya basuda abinci yace sai xuwa gobe. Julluf tayi ta juye ga plet zata bar kitchen din don ni,ima ce keta amai bata lafiya dataci abu saita amayar dashi,mafarin ta yimata ita. Juyowar da zatai taganshi tsaye bayanta yana goge kwallarsa,saboda tsorata sakin plet din tai kasa tana ja baya,don bazata iya tuna rabon data ganshi ba.......tsora ya kamata tuni hawaye sun wanke idon ta. *_ABDOUL-NASSER_* Ya na isa gida dakin zakiyya yayiwa tsinke................ *naga adduoin ku ina godiya sosai Sannan ina rokon Alfamar ku cigaba da man uxiri saboda yanayin jikina,ngd da nuna kauna* [9/30, 3:43 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️..........53 Saida yashiga falon yaga baidace yashigo mata acikin yanayin dayake ciki ba,frig dinta ya bude ya dauko ruwa har zaikai bakinsa yatuna da dokarsa,saurin dakatawa maimakon yasha saiya fito waje da robar ya tuttulewa kanshi ruwan har xuwa ga fuskarsa,yana sauke ajiyar xuciya sanyin yana ratsa xuciyarsa yana sauke mashi duk wani zafi daya debo. Jingina bayansa yayi da bango yana yin relax,saida ya kwashe minty biyar ahaka sannan ya samu sauki ya najin duk wasu makamai dake cunkushe cikin ransa suna sauka,duk da ba duka ba. Har yanxu kunnensa yana sake jiyo mashi munanan kalamanta,wannan ya nuna cewar hasashensa akanta duk gaibune,yana tunanin yadda yakejin masifar kaunarta cikin ransa yazaji itama haka,koma fiye dahaka ashe haukan banza yake.yana bukatarta cikin rayuwarsa da zai dora agaba idan Allah yabashi iko,yana ma yaransa tanajin uwa da tagari da zata dorasi bisa daidai.yana mafarkin zamun hasken acikin rayuwarsa agaba,amman duk wani burinsa da fatansa ta rusa mashi su. Saiwani nanata mashi maganar auren zakiyya take,ina ruwanta da aurenta da rashin auren ta dazai,amman yanaga wannan ce kurin damar shi.yadda ta nuna bata yi dashi duk maitarshi shima ya kamata yadaga mata kafa hakanan,karon farko yaji xuciyarsa ta raya mashi daidaitonshi da xakiyya,har xuwa sanda zai yanke shawarar data dace dashi. Bedroom dinsa ya nufa kurin ya fada toilet ya saki ruwa ya jima yana sauka jikinsa yafito da Alwallah yayi sallar isha,i sannan ya canza kaya yaje ya hado tea marar zafi sosai,yana sha ya gama ya duba system dinsa sakonnin costomers masu son ganawa dashi,yayi accepting wasu wasu kuma yayi reject. Haka yayita aikin da zai dauke mashi hankali daga tunaninta da bacin ranta,har dare ya tsala ya ajiye ta kwanta daker da sidin goshi baccin yayi nasarar daukarshi. Muryarta cikin kuka kukanda duk wanda yaji saiyaji kamar ya tayata,tundaga kasan xuciyarta kukan yake tahowa,numfashinta har sama da kasa yake maganar ma bata fita sosai,don muryar ta dishe saboda kuka. Yana rungume da ita cikin kirjinsa yana tayata kwallar shima,don shima kukan kurin zaiyi yaji ya samu saukin xucoyarsa. "Na gode ma Allah da wannan jarabtar domin na yi imani dashi,hakan yana cikin kaddarar rayuwarmu nida yarana,kuma bazan butulce mashi ba zan gode mashi da har ya waiwayo maka da hankalinka akanmu.hakika wannan hukuncin sa ne ba na kowa ba.sai kuma sila da dalili,banda kamar wannan yarinya aduniyata hakika Allah zai mata kyakkyawan sakamako aduniya da kuma lahira,malam kabir daka tsana arayuwarka shine dalilin dayasa kake raye ahalin yanxu,haka diyarsa safiyya itace dalilin dayasa muka tsinci kanmu cikin wannan halin na farin cikin daidaituwar komi,idan baka nemi yafiyarsa ba Allah saiya tambayeka matayinsa na makocinka mai hakki akanka,amman kasa kowa ya tsanesa bada wata hujja ba Abbin ni,ima kadawo cikin hayyacinka idan baka gina lahirarka ayanxu ba yashe zaka ginata,kana da tabbacin kana da kwana ki dayawa arayuwarka..........rufe mata baki yayi yana kwalla harda shashsheka yace"insha Allah nai alkawarin gyara kura kuraina mamin ni,ima nai alkawarin dawowa mutumen da al,umma zasuyi alfahari dani kuma zan dage da neman tsari daga shaidan da makarrabansa,domin hada rashin kiyaye azkar yasa koma me mariya tayi mun ya sameni.amman na dauki hakan matsayin darasi da kuma hanyar gyarace Allah ya nuna man,hakika zan gyara alakata da malam kabir inhar yaban dama xuria zan hada dashi." Jawota yayi suka zauna kan kujera yana rike da hannunta,yasoma bata labarin duk abunda ya sani ayau dinnan,kuka ta kamayi tana fadawa jikinsa yana sake godema Allah daya kawo silar fitarsu cikin wannan kangin. Wannan dare haka Abbi ya rungume mami da ni ima ajikinsa har garin Allah ya waye. ********* Yau da shirin koma wa wajen aikinsa ya tashi,tun wajen bakwai ya gam shiryawa yafito bai saka ran samun abun kari ba,don yasan irin wannan lokacin daga ita har malik basu isa tashi ba. Amman sai yajiyo wani kamshi wanda ya ankarar dashi cewar tatashi,dandanan yaji yunwarsa ta ake yunkurowa. Agogonsa ya kalla yaga ya kusan makara kuma yanzu haka mutanen da ya ansa zama dasu suna can har sun iso tun da asuba jirginsu ya sauka. Hanyar kitchen din ya nufa yana dan daidaita fuskarsa. Ta juya baya tana soya kwai ga dankali nan ta kwashe cikin gwagwa,saman gas din kuma farfesun yan cikine take idasa dafawa.ga placx nan komenene ta hada ciki kilan tea ne,inji xuciyarsa, Rungume hannu yayi ga kirjinsa yana kallon bayanta,doguwar rigace ta bacci iyakar guiwarta amman mai kauri baka ganin jikinta,gyaran murya yayi wanda ya sata tsorata har tana yadda ludayin datake juya kwan dake cikin kasko.lumshe ido tayi tana ajiyar xuciya ta duka ta dauki spoon dinta tana juya tace"ina kwana" Murmushi yayi ya ida sa shigowa sosai yana cewa"uhmmm wannan kamshi dakika bude gidan dashi haka,mekike aikata mana ne" Banza tayi dashi amman kasan ranta murna ce fal kamar me. "Don Allah ataimaka mun ahada mun cikin basket sauri nake kuma bazan iya jira naci ba,Allah yasa andafa dani" Nanma taimashi banza ta gama soya kwan ta dauko kwandon da yaje xuwa office dashi da containers din da take xuba mashi,ta fara xubawa ko inda yake bata kalla ba. Jinjina shariyar da take dashi yayi amman sai yaji hakan kuma ya burgeshi,hakika ballagazar mace marar aji batai ba ace kina mace Mai daraja kina watsar da ajinki da kimarki. (Yan mata take not akula da kima da martaba,suna da matukar muhimmanci ga rayuwarki ko kau ga mijinki ne balle saurayi) "Wai har yanzun fushin ake dani zakiyya" Wani kallo ta jefa mashi ta dauke kai ta cigaba da aikinta kurin. Dariya ya danyi kadan harta kalleshi don shidin bai

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});