Chapter 1
Chapter 1
[9/17, 3:34 PM] mom muhseen 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........1 Wani irin traffic ne aka had'a kan titin central park,wanda ya jawo tsaikon motoci.ko kad'an ma motocin basa tafiya tsaye suke,wasuna fitowa daga cikin motarsu suna hangen abunda ke faruwa,dan dazon mutane ne kan titin yayinda wasu keta fitowa kallon abunda ya faru.nima dai matsawa nai sosai don kashe kwarkwatar idona,mutane nake ta turewa ina kutsawa don isa inda wannan dan dazon mutanen yake..............wow oh may god masha Allah,wani tsalelen guy ne na gani kwance k'asa cikin jini,duk da yadda jini ya wanke fuskarsa da kirjinsa hakan bai hana tsananin kyawunsa fitowa ba,ko makaho ya shafa yasan wajennan akwai kyau na fitar sharia..............araina nace kai mutanen mu sai abarsu yanzu duk nan babu wanda zai iya kawo mashi d'auki......ban idasa tunani naba naga wani guy yashigo wajen a dari da hamsin yana shashsheka,,,,,bai tsaya ko inaba sai gaban wannan guy d'in dake kwance cikin jini.........kuka yake yana jijjigashi yana cewa mutanen dake zagaye dasu. "Don Allah ku tai makeni na kaishi asibiti,bana iya daukarshi....don Allah kuduba halin da yake ciki,ko numfashi fa bayayi."amman saboda rashin mutunci babu wanda ya kulashi saima tsogumi suke akan ya kauda masu shi suna da abunyi,wani babban mutun yakalleshi yace"wai ba d'an gidan ALH MAINAH bane,wannan tsinennen yaron zamu taimaka,ai baida wani anfani,tunda har iyayen dasu haifai ma sun yardashi basu so wa kuwa zai jefa kanshi cikin matsala,gara kabarshi ya mutu domin itace tafi dacewa da mai irin layyarsa la,anennen yaro kawai." Nanfa kowa yaita fad'an albarkacin bakinsa akan wannan guy dake wance har lokaci baisan wake kanshi ba,kuka guy din dake rike dashi yake yana neman taimako amman babu mai kulashi,daker yajashi gefen hanya yana kuka yana cewa. "Allah yana tare dakai *Alfah* insha Allah ba yanzu zaka mutuba,kowane mai rai da tashi jarabtar kai kuma haka taka tazo,Allah ya baka ikon cinyewa...........kwantar dashi yayi ya koma bakin titin yana tsayar damai taxi cikin ikon Allah yasamo,da gudu suka zo suka daukeshi shida mai taxin suka sashi cikin motar,basu tsaya ko ina ba sai asibiti. Cikin gaggawa suka ansheshi suna ta fad'an meyasa ba,a kawoshi cikin gaggawa ba shidai wannan bawan Allah baida bakin magana,domin shidai burinsa yaga aminin nashi yadawo hayyacinsa,card ya siya yaje aka rubuta mashi duk abunda ake bukata.ansa yai ya wuce pharmacy ATM yabada aka zara sannan aka bashi abunda ake bukatar,yaje yakai yadawo ya zauna yadafe kai.hawaye share share ga fuskarsa yake magana kamar mahaukaci shikadai. " babu abunda zai sameka *ALFAH* zaka tashi,insha Allah babu abunda xai faru,duk yadda kake kaunar mutuwa idan kwananka na gaba bazaka tab'a mutuwa ba,saidai kasha wuya kurun ban san har sai yaushe zaka gane abunda nake nusar dakai ba,ko mutuwar kayi Alfah bakada tabbacin acan din zaka dace da jin dadin daka rasa anan duniya,kayi hkr komi mai wucewa ne no condition is permanent.inaji araina watarana komi zai daidaita.........kuka yake yana tsananin tausayawa abokin nashi,baida kamar Alfah duk duniya shine gatanshi shine kominsa, duk abunda yasamai na dadi dana bakinciki tare suke raba wa,.........dafashi akai ya d'ago fuskarsa ta b'aci da hawaye wani likitane tsaye kanshi,saurin tashi yayi yana goge face d'insa cikin kermar murya yace"Dr ya farka yadawo hankalinsa ko,babu abunda yasamai." Murmushi Dr yayi yace"don't worry ur brother is a life,amman muje office i need to talk 2 u serious issure." Binsa yayi harma yaso wuce dr saboda sauri duk ya susuce,rik'oshi Dr yayi yana mashi dariya dafa kafad'arsa yayi suka k'arasa har office d'insa. 💞💞💞💞💞💞💞 "Assalamu alaikum." Wata tsaleliyar budurwa tayi sallama acikin wani gida wanda baza akirashi da gidan mai arzik'iba,haka baza ka kirashi da gidan talaka ba,gidane daidai wa daida ginin bulone na sumunti,saidai kallo d'aya zakayi mar kasan cewar ginin yasha jiki,kuma bana yanzu bane don wani wajen ma yad'an gugure,d'akuna ukune biyu ciki da falo saidaya single,sai kitchen acan daidai hanyar fita,public toilet daga can ciki yake.sai filin tsakargida mai d'auke da dalbejiyar umbrella tsakar gidan shafe da smuntu,dagani ba ajima da yin saba.duk dadai babu fenti tsakar gidan, saidai cikin d'akunan ya keda shi,shima yasha jiki dagani andauki shekaru dayawa dayinsa daga gefe idan kashigo zaka hango rijiya.gaba kadan kuma wajen kiwon dabbobine da kaji.........atakaice dai wannan gida mamamallakinsa yana da rufin asirinsa,daidai gwargwado daga waje kuma inzaka shigo akwai shaguna biyu jikin gidan,d'aya d'aki aka maidashi dayan kuma kayan masa rufine aciki ake siyarwa. "Assalamu akaikum" Wannan tsaleliyar budurwar tasake maimaita sallamarta tana yamutsa fuska,sai hakan yayi matukar sake k'awata fuskarta,farace fess don kadan zai hana ba kace mata zabaya ba,haskenta hade yake da jajaja amman saika lura zaka gane hakan........"wai gidan ba kowane sai sallama nake idan kuma nashigo ace ba ajiba saina sake,wlh nidai shigo zan nagaji da wage bakina har yafara ciwo." Wata matace ta fito daga wani lungu rik'e da buta da alamar ma daga ban d'aki take. "Wlh ina band'aki najiyoki nasan wasu kaya sai amale inba *SOFIYYAH* ba babu mai shigowa gida yayita kwala ihu yana hayagga." Turb'une fuska tayi tana sake yamutseta tace"wayyo Allahna mamana kefa kikace indaina shigowa gida banyi sallama anjiba,yanzu kuma nayi kince ina hayagaga ke kullum yasmeen ce keyin daidai,nadawo ma ko sannu bakiyi man ba,ga yunwa ga kishirwa ga gajiya,koma kice *FIYAH* yau kin dade meya tsaidaki aa sai kika hau yiman fad'a.......tafiya take zuwa d'akinsu tana wannan tsogumin. Murmushin matar tayi tana biye da ita tace"Allah yashiryaki bazaki tab'a canza waba fiyah." Binta tayi cikin d'akin tana cewa"to yi hkr uwar masu gida,yau lafiya kika jima haka ko lectures d'inne suka yi yawa." Kaya take tub'ewa tana turo d'an bakinta kamar na tsuntsu,tace "mama yau dawuri muka tashi wlh,inata murna zandawo intai islamiya,mama muna zuwa titin wajen central park wanda ya mik'e har zuwa *ALFAH STORE SHOPPING MALL* wlh mama traffic ya tsaidamu munkai one hour wajen,ashe wanine yayi had'ari amman akarasa mai taimakonsa,mafarin muka kai har kamar yanzu." Daga itasai undey da bra,sai surutu take ma maman.matsa kusa da ita tayi tace "mama ballemun donAllah." Girgiza kai uwar tayi tana balle mata bra d'in tace"baki tab'a canzawa fiyah ace katuwar budurwa dake fiyah kullum ni ko yasmeen mune y'an 6alle maki breziya,kinji kunya wlh aibanganin laifinta intayi maki dariya."turo baki take tana sun6ure sun6ure. "Bari naje in sauke miya kin d'auke man hankali karta babbake,ta fice ita kuma ta d'aura karamin towel d'inta daya bayyana santala santalan k'afafunta,farare tas idona yakai ga bombom d'inta zaro ido nai nace masha Allah madaidaita masu ban sha,awa,komi dai jikin fiyah masha Allah,komi yaji gashinta kwance yake kan tsakiyar bayanta,toilet dake cikin d'akin nasu tashige *fiyah* kenan matashiyar budurwa yar shekara ashirin cif. *********** "Dr kakirani kuma kanata y'an rubuce rubuce,na matsu naji wane hali d'an uwana yake ciki." Ajiye biron hannunsa yayi yana cewa"sorry abokina,ya sunanka ma dai." " *malik*" yafa d'a atakaice Dr yace"nice name,yi hkr malik ina rubuta wasu magungunan nanne,i think wad'ancan bazasuyi mashi aiki sosai ba." Shafa kanshi yayi yana fesar da iska yace"nifa ba wannan natambayeka ba cewa nai wane hali yake ciki yanzu,shine abunda nafi bukatar ji daga gareka." Ajiyar zuciya Dr ya sauke yace"ka kwantar da hankalika ya dawo ciki hayyacinsa,munyi masa d'inkin raunikan da yaji,sannan munyi kokari
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101