Chapter 63
Chapter 63
Cikin tsananin tsawa yace"zakiyya nace kije ki dora mata breakfast now,wlh har nadawo bakiyi ba zakisha mamaki na." Ta tsorata da tsawar da ya mata tunda take dashi haka bata taba faruwa ba,hawaye suka xubo mata ta sadda kai kasa tace"kayi hkr zanyi zuciyata ce take cike da kunci shissa" Sai tausayinta ya kamashi ya sassauta murya yace"idan xuciyarki tana cike da kunci zakiyya bakisan me zaki yi ta warware ba,bafa halinki bane kar son rai yasa ki aikata abunda zaki dade kina nadama,safiyya wani bangarene na rayuwar Abdoul,baza ki iya rabasu ba bazan ce suna son juna ba haka bazan ce basa son juna ba,amman tabbas suna ji da juansu,Abdoul yada baki tunani haka yake ji da fiyah.kuma abunda kikai mashi har yau yana kule dake,da zakiji shawarata dakin kauda idonki akansu,da kin saka masu ido kinga abunda Allah zaiyyi.nasan kina son Abdoul ni shedane amman kaddarar rayiwa ta hadashi da fiyah,ke kuma ta jefo wani babban shamaki tsakaninku.kiyi addua komi ya daidaita karki bata rawarki da tsalle,bana tunanin Abdoul yabar sonki zakiyya zan dai iya cewa kaso sittin aciki ya bare.don haka kisan mekike ciki muddin zaki ringa aibata safiyya kina fadar maganganu marasa dadi akanta,to ba Abdoul kadai ba nima nan zan kullaceki haka zalika zan canza maki,ya rage naki ki gyara tun kina da sauran lokaci,zanje store indawo kilan kingama time din" Haka zakiyya tasha kukanta ta gode ma Allah ta lallashi kanta,hakika tana jin wani azabebben kishi akan Abdoul,amman ya zatai dole zata hkr zata koyi danne wa har Allah ya dorata kanshi,bata iyajin zata barshi muddin bashine yafurta dakansa cewa yabarta ba. Jiki amace take hada breakfast din,kaza ta gasa mata tayi laushi sosai ta zauna ta zare kasusuwan,sannan ta soya dankalin turawa tayi mashi vegetable sos sai kamshi miyar take,sannan ta dafa ruwan zafi mai kayan kamshi sai tayi mata wainar indomi mai hade da kwai taji tarugu da albasa..........tagama ta hada su cikin basket taje tayi wanka,sanda ya dawo harta shirya tace"zan bika yaya malik inganota" Murmushi yayi yace"kokuma ki ganoshi ba" Sadda kai tayi tace"aa wlh suduka zan gano" Dariya ta bashi yace ta samai mota,mayafinta ta yafa ta dauko basket din ta biyosa,babu laifi tayi kyau tunda ita ma daidai gwargwado kyakykyawace sosai. Tunda yayi salla ya dan sake koma wa sai da kiran malik ya shigo ya tadashi,yayi mashi bayanin abubuwan da babu acan shopping mall dinsa da kuma wasu abubuwan,sun jima suna mgna yace zaije ya taho masu da breakfast.Abdoul yace ya taho mashi sa brush da merclean. har sha daya tataho yinwa yakeji, wayarsa yake danna nawa yana duba wasu abubuwan,yaji kamar sautin numfashinta,kamar tayi motsi ko nishi. Tsayar da idona yayi tam akanta yana kallonta,tsawon minty uku yaga ta sake motsawa tashi yayi yaje gaban gadon ya dora hannunsa bisa kanta yana mata addua,jiyai bakinta yana magana can kasa sosai saika kanga kunne zakaji abunda tace. "Alhamdulillahil lazi ahyana ba,ada ma amataha wa ilaihir nushur,innalillahi kaina zai fashe mama kaina ciwo yake kinji mama" Zuwa yanzu maganar tana fitowa adduar yake tofa mata akan da kuma fuskarta,ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai,dishi dishi tafara gani hannunta mai kanula ta saka zata murza idon yayi saurin rikeshi. "Akwai Canuler karki saka" Kamar mafarki take taji sautin muryarsa,amman dakin juyawa yake da ita ta gaza yarda ma a ina take shin,hannunsa yasa yana murxa mata idon ahankali,kamar yasan haka take so dandanan ganinta yafara dawowa. Dakin take kallo kafin ta dire idonta akansa,zaro manyan idonta tubar kalla tayi akanshi,wani irin yammmm yaji ajikinsa har saida ya lumshe idonsa yasake budewa still kallonsa take. Kafin kwalwarta tafara mata tariya abunda yafaru da ita,. Cike da rudani ta tashi tana waige waige duk ta firgice,idonta duk kwalla. "Inane nan,mesu kamun?menai masu don Allah kai ina nike bangane ba,miye wannan nashiga ukuna" Wata kara tafasa tana kiran "mamaaaaaa" Hankalinsa yayi masifar tashi riketa hake tana fizgewa duk ta haukace mashi,jikin ai rawa yake daidai shigowar su zakiyya da malim,sai yasmin. [9/19, 11:52 AM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️.............46 Gaba ki daya hankalinsu ya tashi ganin yadda fiyah duk ta bi ta haukace,tana fixge fixge tana kiran mama.yesmin kuka take sosai don inkaganta zaka dauka sabuwar mahaukaciya ce. Ganin tana niyyar fixge canuler hannunta yasaka yahadeta dukanta yayi mata wani kyakykyawan ruko cikin jikinsa,yana hura mata iska cikin kunnenta idan kagansu zaka yi mamakin yadda suka hade waje guda,numfashi takeja tana kuka kasa kasa yana shafa kanta tare da yimata alamar lallashi kamar yana lalashin yaro. Zakiya wani kudulelen abune ya tokare mata wuya,duk yadda take kowa da xuciyarta da kwayar idonta akan kar tayi kuka abun ya ci tura,juya baya tai tana shere kwallarta. Malik yana lura da ita bai ce mata komi ba,yesmin dai sai sharar kwallarta take. "Malik ka kira dr pls" Jinjina kai yayi yana fita daga dakin,zakiyya ma ficewar tai yabita da kallo kasan ransa tausayinta yake,amman bazai iya yin halin ko inkula da safiyya ba bacin tana bukatar taimakonsa. Ajiyar xuciya yaji tanayi kuma rikon da tayi mashi tana sassautashi,jikinta yana saki ahankali. dago fuskarta yayi ahankali ta bude idonta ta zuba mashi su lumshe mata nashi yayi yana karkta kai tare da dage girarsa guda,yakai bkinsa kan kunnenta cikin sanyin murya yace"cute baby relax mana,bude idonki ahankali zaki gane inda kike,qanwarki yesmin ma kinganta anan,karki sake rikice man plsss nima zan iya birkicewar oy open ur eyes and relax" Kalamansa kamar saukar kankara fakejin su cikin xuciyarta,waye yake mata wannan kalaman da takejin suna saukar mata da wata natsuwa ta musanman,jikinta yana sakewa kwalwarta tana dawowa daidai tare da tariyo abubuwan dasuka faru,ahankali yake zare jikinsa daga nata wanda yakejin wata irin kasala tana mamayesa,har yana jin tsikar jikinsa tana tashi. Komawa tai jikin bango ta tattare kafafunta ta rungume tana kallon dakin har idonta ya sauka akan yesmin,wata nannanuyar ajiyar xuciya ta sauke ahankali bakinta yana rawa tace"yesmin" Rugowa tayi wajen Addar tata ta rugumeta tana kuka"Adda kin warke ko,kice mun baxaki sake irin abunda kikai ba,kin tayar mun da hankali........dr ne da malik suna shigo ahankali take kallon malik tana kallon Dr ta juya ga Abdoul dake gefe yana dafe da kansa idonsa arufe. "Sannu qanwata kin tashi ko Allah ya sawake" Daga kai tayi tana kallon yesmin. Dr ne ya dubata yace"jiki alhamdulillah xuwa anjima ma idan ruwan can ya kare, ana iya bata sallama,anyi ta barka wlh wasu har rasa hankalinsu suke ta silar wannan allurar,Allah ya kiyaye gaba" Abdoul ne yace "dr tana gama karya wa zaka sallameta zaman me kuma zata zauna tayi bayan komi success" "To yallabai yadda kace din amman inso samune anfison ruwan yakare tukun" "Anjima zan sake dawowa idan ruwan yakare saina bata sallamar", Ajiyar xuciya yaja yana dora idonsa akanta,akai sa,a itama shi din take kallo. Tama rasa wane tunani zatai,sadda kai tayi malik ne ya fita yashigo da zakiyya daka kalli idonta kasan tasha kuka ba kadan,tunda ya mata kallo daya ya kauda kai bai sake kallonta ba,don zata raunana mashi xuciya,bacin bacin ran data sakashi. Toilet yashiga yayi brush ya fito ya zuba breakfast dinsa ga plet yaja gefe yana ci kamar babu kowa dakin,malik yace zakiyya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101