Chapter 56
Chapter 56
bita wajen xuwa wajen mota ta anshi no dinsa sukai sallama. Malik shiryawa yayi don samun daddy ayi wacce za,ai don yau insha Allah sai sun saurari abunda kecikin m.card din Daddare ya shirya yace ma Alfah zaije wajen dady yadawo,da ido kurin yabishi don gabaki daya yarasa natsuwarsa,rashin yarinyar na kwana biyu duk ya rikita mashi tunani,matakin da ta dauka akan su baimashi dadi ba,jiyake kamar yatuge wannan shege drip din ya je gidansu,amman yasan bazai iya zuwa ko da kofar get din ba,balle har yashiga ya dauki alkawarin shida maitama har abadan abada. Malik har gida ya iske dady suka gaisa da matarsa mai tsananin kirki,itace ma tai mashi iso ga dadyn har babban falonsa,aka kawo mashi kayan sha da ci amman ba tasu yake ba,soyake akawo karshen komi dake faruwa cikin rayuwar Abdoul,abun ya isa haka yana cikin kewa da mararin ganawa da mahaifansa,amman wannan babban ginshikin yatare komi,ya hana komi tfiya yadda ya kamata. "Malik sannu da zuwa ya hanya" Ya na zaune kasa ya sadda kai yace "lafiya lau dadyy,ya nasameku" "Angode Allah,ya jikin Abdoul din fatan yana samun sauki sosai,naso nazo dazun nasake dubashi sao aka kirani office,amman dasafe zamuzo da yara harda mamansu mudubashi" "Allah ya Kai mu dady,dayake ma goben ake saka ran sallamarsa ai" "Masha Allah Alan ya sa iyakar wahakar kenan,da alama dai akwai magana ko,to inajinka" Muskutawa yai ya ciro wannan m.card din daga cikin aljihun rigarsa,ya nadesa cikin wata takadda ya warwaresa yana cewa"dady wannan shine kedauke da duk wasu abubuwa damuke son sani game da makarkashiyar da aka shirya ma Abdoul,kuma anan ne zamu san suwaye suka hada wannan abun,musan kuma dalilin dayasa sukai hakan idan kayarje man zan sashi ga system din danazo dashi mu saurara." Jin jin jinakai dady yayi yace"naji dadin wannan magana malik,kuma hakika kaida wannan yarinya safiyya Allah ne zai biyaku,domin kunyi abunda za,a yaba maku Allah yayi maku Albarka,amman ina kta safiyyar ba kace tare zaku zo ba" Cikin jimami yayiwa dadyn bayani ataikaice shima ya fahimceta yace "babu damuwa ai tariga ta gama komi sai fatan Allah ya biyata,yabata miji nagari wanda zai kula da ita har karshen rayuwarsu.ni da nai zaton ma kana sonta Abdoulmalik,har nafara murna ta samu miji na kwarai." Murmushi yayi yana sosa kai yace"ai dady da nasotan,kuma naita fatan daburin na zama mijin nata,saidai duba da wasu abubuwa danai naga bani ne nadace da ita ba, ABDOUL-NASSER yafini bukatar samun mata kamarta,domin shine koda yaushe rayuwarsa take cikin hadari,koda yaushe ake neman kassarashi,sainaga safiyya yarinyace mai hankali da natsuwa tanada wasu abubuwan da zaka nemesu ga mata dayawa baka samesu ba,ga ilimin addini tana da wayau da dubara komi zatai saita yi nazarinsa ta lakancesa kafin ta aiwatar,haka zalika tana da juriya sosai ga uwa uba hkrinta shiyasa naga gara na hkr wata kila silar sadaukarwar danai Allah yaban makamanciyarta.shiyasa nai iyakar kokarina wajen ganin nahada su da juna,har saida naga nayi nasara don ina kyautata zaton suduka suna son juna Allah ne bai basu ikon furtawa ba,yanzun haka yana can cikin damuwar rashin ta kwana nan." Jinjina kai dady yayi yace"kayi tunani maikyau malim,kuma insha Allah Allah bazai barka haka ba,hakika zai maka tanadi na musanman.naji dadin jin wannan labarin don haka kasaurari kyautata daga gareni insha Allah." Dariya yayi yace"to godiya nake dady,zamu iya kunna wa duba da lokaci" Dadyn yace "mezai hana bismilla nima na zaku danajin abunda kefaruwa don akwai wani zargi cikin raina" Malik yasaka wannan m.card ga system dinsa yashiga yana uploading dinsa har yahau yashiga cikinsa yana dubawa,recording ne kashi uku guda daya kuma vidion ne. Kuyi hkr jiya nayi alkawari na saba,wlh ban dawo da wuri ba shiyasa kuyi manage dashi plsss *don't share it plss I beg* [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........41 Sanda yaje har anrubuta sallamar dr yana sake nanata masu kiyaye dokokin dasuka gindaya ma Abdoul din,na daina shan abu mai zafi sosai ko mai sanyi sosai,daga yadda malik yake Abdoul yasan ba yacikin mood mai dadi.kallonsa yayi tayi suna tafiya zuwa gida,hardai ya kasa jurewa yace masa"malik kana lafiya kuwa?" Ba tare da ya kallai ba yace cikin sanyin murya"kaina keciwo shiyasa" Shiru Abdoul yayi amman badan yayarda da abunda yafada mashin ba,baisake tambayarsa ba don yasan ba fada mashin zai ba.lumshe idonsa yayi yana sauraren xuciyarsa dake ta dawo mashi da moments dinsu nabaya shida safiyyah,wani yayi murmushi wani ya jinjina kai yana nadamar wasu kalamansa na baya da yake jifarta dasu,harta hkr batai fushi ba tacigaba da taimakonsa.yayi bincike bai hango yarinya kamarta mai irin wannan hankalin da hkr da tarbiyya ba,ga natsuwa idan zai kwana yana lissafa halayyarta kilan bazai gama ba,don yalura kullum da wasu sabbin halayen zai sameta.ahankali yafurta "mijinki ya More" jiyai kirjinsa yayi masa nauyi saboda abunda ya furta,kenan wani duk zai samu wadannan abubuwan gareta,wata xuciyar take kitsa mashi inka yarda kana sonta maizai hana kafito kabayyana hakan,girgiza kai yayi shikadai malik na ganin yanayinsa baice mashi komi ba,don shima danashi kason tunanin kilaman saiyafi nashi rudani da rikitarwa.har sukaje gida babu mai magana suna yin parking zakiyya tafito aguje tana zare ido.idonta ga Abdoul tana kallonsa,malik yadaure yayi mata murmushi yace"kekadai gidan ko,gashi babu abun ci gidan Allah yasa ko tea kinsha" Kwalla cike da idonta tace"aa bazan iya saka komi acikina ba yaya malik,hankalina duk baya kaina yana wajen ku ina tunanin ko yajikin sa." Abdoul yazo yara b'ata yawuce baice mata cikanki ba,duk suka bisa dakallo. Malik yace"yaji sauki sosai,aikin gani ko." Sadda kaitai kasa yace"karki damu kanki akansa zai warware zaku daidaita,bari nayi waya akawo mana take away kije ki kwantar dahankalin ki karma kisama kanki damuwarsa zai waiwayeki ne" Juyawa sukai suka wuce cikin apartment din babban wanda keda different part's acikinsa. Zube yake kan kujera ya rufe ido still tunani yake. "Daka sassauta ma ranka don gudun abunda zai sameka,kasaurari xuciyarka abunda kaga ta yanke maka akai maikyau sai kayi anfani dashi,amman dogon nazarin bashida anfani amman idan kaji shawarata." Ya wuce dakinsa habarsa da zakiyya daketa hawaye ita kogajiya batayi,tsaye take gefensa takasa mashi magana gani take kamar zai mata tsawa. "Kin tsaya bisa kaina plss move" Silently yayi maganar matsawa tai ta dawo gabansa tana zama tare da tankwashe kafafunta tace"yaya Abdoul yajikin naka" Batare daya kalleta ba idonsa yana kallon rufin falon yace"da sauki" Shiru tai ta cigaba da alwallar kuda kamar taza rushe da kuka tace"yaya Abdoul na gaza samun hanyar dazan fuskance ka da batutuwan dake bakina,bansan dame zan fara ba saboda nasan nidin mai laifice wajen ka,amman yaya Abdoul ka fahimceni duk abunda nai nayisa ne bisa dalilai da yawa kaban dama na warware maka dukullin dake faruwa." Malik ne yafito yanajin abunda take cewa yace"kyaleshi zakiyya bayanzu ba,akwai lokaci yana xuwa tashi kije ki shirya ga abinci nan ankawo.tashi tai tatafi kamar wadda kwai ya fashewa acikinta. 💕💕💕💕💕💕💕💕💕 Jikin baba yayi sauki sosai yana samun kulawar likitocin yadda ya kamata,har ansallami Alh muazzam amman kullin sai yazo ya duba jikin baban,mama dai ba dadin hakan takeji ba amman baba ya hanata nunawa,anty jamila ma sun sake xuwa ita da uncle harda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101