Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,290 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cika fiddo dariya ba sai ta kama,gira daya ya daga mata ta dalla mashi harara. Ta gama xubawar ta ajiye mashi gefensa tana tattara wanke wanken wanda zatayi yanzu. Matsowa yayi kusa da ita kamar zai rungumeta muryarsa kasa kasa yace"I'm very sorry kiyya,nasan laifina yasa har yau kike fushi ko?"daskarewa tai awajen don gabaki daya jikinta ya dau wani sanyi,don abun yazo mata abazata. "Idan nadawo zamuyi magana oky" Daga kai kurin tayi yadauko abincin yafice sai lokacin ta sauke wani gauron numfashi. ************ Bayan fiyah ta dawo daga jarabawa yau wajen karfe shidda harda wani abu ma,tana shigowa gida akafara kiran sallar magruba. Baba bai dawo ba saida aka gama sallar yesmin na kitchen yau ita ke shirya abincin dare,tuwon shinkafane miyar agushi baba ya siyo naman rago an xuba aciki (harnaji miyauna ya tsinke🤭) Tunda fiyah ta dawo tana daki bata jin dadi ko kadan,don har wata masassara takeji.tana cikin tsananin kewarsa tana kan nadamar abunda yafaru,jitake inama ta fada mashi cewar soyayyarsa itace weakness dinta,itace farin cikinta da bakin cikinta.rashinsa gareta wani babban bigirene da bazata iya misalta shi da komi ba. Mamace ta shigo dakin don yesmin tace mata tana daki kwance. "Safiyyah lafiya kike kuwa" "Bandai jin dadi ne mama kamar xanyi xaxxabi" "Subhanallahi,ainace ku daura net kun kiya badole sauro ya cije kuba,bari dalha taxo saiya siyo maki ACT,kifito kici abinci harda yunwa ma kilan" Babane yashigo yasa mama ta fita tana ansa sallamarsa. Take gaya mashi abunda ke damun safiyyar,yaje shima ya dubata yace ta fito yasa mata tabarma tasha iska,saitaci abincin tasha magani. Gaba daya suke cin abincin a tire guda,sun hirar su gwanin ba sha,awa,kallon safiyya baban yayi yace"bayan masassara akwai abunda yake damun ki uwata ko?" Yake tayi tace"aa baba babu komi bayan ita,hada gajiya kullum ina kan hanya babu hutu shiyasa ma kila ta saukomun" "Allah ya baki lafiya,muhseen ya kiraki kuwa" Kanta yana kasa tace"eh ya kirani ina cikin jarabawa saida nafito na yasake kiraa" Jinjina kai baban yayi yace"idan ya sake kira ka safe,kice ina son ganinsa idan ya samu lokaci" Da to kurin ta bishi,tana jin dadin abunda zaifarun don tasan maganar yesmin zai mashi. Dalha ya shigo da maganin nasha yafita,bai jimaba ya dawo yace ana sallama dani. "Waye" Inji baban. "Kanen uncle yahya ne yazo" "Kace ya shigo batajin dadi bazata iya fitowa ba" Dadi ya kamani don kona fitar bansan me xance mashi ba. Yesmin naga ta shige daki tana jin ance haka,murmushi nai nace araina makira tasan ta samu abunda takeso. Sallama yayi mama ta ansa mashi baba na nuna mashi tabarmar dayakai. "Bisnillah anan dana zauna" Ya na murmushinsa na gado ya zauna yana gaidasu cikin girmamawa,hakika muhseen mijin aurene kawai dai ni banda ra,ayinsa ne shie kawai. "Yaya muhseen ina wuni" "Lafiya lau safiyya ashe bakiji dadi ba sannu Allah ya sawake" Tace"ameen nagode" Baba ya kalleta yace jeki ciki zamuyi magana dashi,kekuma mamansu xubo mashi tuwo karkace ka koshi zan dauka baka daukemu iyayeba" "Zanci baba kayi hkr" Mama tatashi taje ta xubo mashi ta kawo ta ajiye tana samun waje daga gefe itama ta zauna,yana ci baban yana janshi da hira kadan kadan har yaci dayawa yana ajiye spoon din. "Na koshi mama ya isan haka nagode sosai kuma tuwo yayi dadi ba kamar tuwon jawaheer ba" (kanwarsu dake bi mashi agida) Dariya mama tai baban yana tayata tace"kadai raina nata ne amman ba dadine babu ba" "Wlh mama karma ki hada da wanan nakin,don ita tuwonta kamar talge haka yake,kanaci zai ka nemesa karasa" Dariya suke ita baba ta GB wuce ta kai kwanonin kitchen baban yace"wannan din kuma da kake yabawa qanwarka yesmin tayi ai" Zaro ido yayi"dagaske,gaskiya ta yi kokari sosai zan turo jawaheer ta ringa koya wajenta. Gyaran murya baba yayi yace "muhseen" Jin yadda baban ya kirashi yasan maganace mai matukar muhimmanci,yadago yace"na,am baba" "Magana zamuyi dakai mai muhimmanci,ina fatan zaka fahimce mu kuma xaka dauki abunda muke nufi da kai" Jinjinakai yayi yace"insha Allah baba xanyi duk yadda kace" Gyara zama baban yayi yace"ammm muhseen alokacin dana ansa maka kan maganar uwata ashe munyi kuskure kadan,wanda har hakan yake son kawo damuwa. Inason nabaka hkr abisa abunda xance maka,don Allah ka hkr da safiyya ka nemi qanwarta yesmin.wasu dalilai suka nace haka saboda ganin cewar uwata batayi na,am da maganar ka ba kuma bata fadi cewar bata so ba,sainaga wannan zai iya kawo cikas ga zaman takewar ku maimakon kuji dadin zama da juna ana iya zamun akasin haka,saboda kaunar danake maka yasa naga bazan iya kyaleka ban maka tayin auren yesmin ba,ko ita za a mu dace amman idan kanaso bazan ta kuraka ba don bazan so wani ya cutu ba ya kagani,inbaka lokaci kaje kayi shawara agida kokuwa." Ajiyar xuciya yasauke yana jin wani dan ciwo kasan ransa,hakika babu abunda yakai kaso akika amman kuma hakan yafiye mashi sauki daya aureta bata sonsa,bazaiji dadin zama da ita ba koda kau ta danne ta nuna bakomi,amma ita ai abun zai cutar da ita,sannan itama yesmin din baida tabbacin zata soshi balle har yayi saurin na am da maganar baban,hakika yana son safiyya so marar iyaka,amman hakan bazai sakashi yaso kanshi ba don haka ya hkr da ita maganar yesmin kuma itama dole yasan idan ita tanuna tana ra,ayinsa shikuma zayyi alkawarin kulawa da ita fiye da tunani kuma zai yi iyakar bakin kokarinsa wajen sakata cikin xuciyarsa,har Allah yasa mashi sonta. "Kayi shiru muhseen,idan kaga akwai takura wlh babu tilasci kafafi ra,ayinka naji" Ya sake sadda kanshi yace"baba hakika na fahimce ka kuma abunda ka fada gaskiyane,ban boye maka ba tun wancen lokacin inason safiyya,amman sonta bazai saka na cutar da ita ba,don haka na hakura da ita Allah ya bata wanda takeso nagari wanda yafini,sannan maganar yesmin. Baba karku tilasta mata bazamu san meke ranta ba,kar axo ayi abunda zai kawo damuwa inhat yesmin bata da ra,ayina baba don Allah ayi hkr da maganar nan Allah xai bani wata makamanciyar safiyya" Tausayinsa ya kama baba da mama,baban baiso fallasa yarsa ba baiso sanar dashi son da take mai ba,amman ya xama dole kodan ya samu kwarin guiwa,don harga Allag yana son yaron yanason sake hafa xuria da ahalinsu.suna da kirki da daddatako. "Muhseen karka damu inhar akan haka ne,yesmin ta nuna mana kai takeso mafarin kenan uwata tazowa mamansu da maganar daba don haka ba,har ayi bikinku bazamu san bata sonka ba,kuma kaima nai imanin baxata nuna maka ba.amman saboda ta gano yar uwarta tana cikin wani hali akanka yasa ta yanke shawarar sanar damu,kaji dalilin zamanmu dakai.don haka kaje kayi shawara da mamanka ko dan uwanka,duk abunda sukace saikayi aiki dashi." Murmushi muhseen yayi yana tuna wasu abubuwa dasuka faru ranar dayaje gano baba asibiti,da lokacin daya daukosu daga asibitin,sai randa ta biyosa ya kawo mama gida sanda fiyah bata lafiya,hakika tana da hankali da wayau tana sonsa bata bashi wata dama dazai gane ba,saidai zata ringa janshi da labari na ban sha,awa da dariya.bazaka taba ganewa ba,tabbas da matan wannan zamanin ne damarta tafarko data samu sanda ya daukota bayan sun ajiye mama alokacin zata barje kolinta ta gaya mashi,amman tana da kunya da kawaici ta danne saidai aka gane amman badai ita ta furta ba. Murmushin

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});