Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 86

Chapter 86

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,264 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ciwonsa na cikin ciki ya warke tas cikin kwana ashirin da dayan da aketa mashi treatment,xuciyarma kuma alhamdulillah bugunta ya daidaita don har yana farkawa yaci dan wani abu yasha magani,amman baya tankawa kowa maganarsa bata wuce eh,aa,yawwa ko idan zai gaida mami dasu Abbi zaice ina kwana atambayesa ya jikin zaice da sauki shikenan. Malik ne kurin yake dan mashi hira yana tankawa shima idan yagaji yayi mashi banza. Wani sabon miskilancine ya tsiro dashi aduk sanda yake sauraren maganar ta jiyake xuciyarsa tana kuna,har wata sa,in jikin ya rikice sai anmashi allurar bacci..........saida mami ta tusashi gaba da kuka tana ya sassautawa kanshi yaji tausayin kanshi da nasu,komi zaifaru yariga yafaru idan anhanashi safiyya bayana nufin karshen rayuwarsa ne yazo ba,akwai mata da dama Allah zai cire maka ita inhar ita din babu alkairin tare da ita,fada take mashi sosai har tasamu ya xubda kwalla ranar yini yayi baice komi ba,bayan kwana biyu kafin asallamesu dady da Abbi suka tai Nigeria saboda wani aiki daya taso anbar malik da su mami da ni,ima da zakiyya dai bayan sati biyu idan an basu sallama zasu dawo tare alokacin ne kuma Abdoul ya fara saukowa yana sakin jiki da yan uwansa zasuyi fira harda dariya shidai iyakarsa murmushi,ahakan ma sunajin dadi son da ai bama aiyin firar dashi. Yau shi kadaine su mami basu kai ga zuwa ba don gidan Abbi dake nan kasar suke zaune malik ne yake kwana dashi,idan safiya tai yaje gida yayi wanka yayo break. Xakiyya ce ta shigo da kwandon kalacinsa fuskarta da fara,a ganinsa zaune yana kallon tv dake cikin dakin nashi. Murmushin shima yayi mata ta ajiye kwandon bisa wani table tana dauko brush din sa ta matsa mashi maclean tace"yaya ina kwana" Muryarsa ta canza sosai tayi sanyi dakaji zaka san cewar yasha jinya. "Lafiya lau kiyya,yau manta wa dani kukai har shadaya saura babu wanda yazo" Murmushi tayi tace"wlh makara mukai yau,nice ma wai nai saurin fitowa sabida break dinka kayi hkr" "Yazanyi daku"ya mika hannu ta bashi brush din yafara kokarin saukowa hannunta ta bashi ya kaa saan ya sauko yana cewa"thank you" Murmushi tai tana bude mashi kofar bayin yashiga ta shiga tattara dakin tana gyara mashi gadin,duk dadai tun safe masu gyaran dakunan marasa lafiya suke shigowa su share. Freshner ta fesa dakin ya kama kamshi komi yayi lafiya lau sannan ta zuba mashi break din ta ajiye kafin ya fito. Kallon dakin yayi yajin jina kai kullum ita ke gayara mashi dakin yayita kamshi alamar jinjina yayi mata yace"kina kokari gaskiya da alama gidanku bazai kasance a datti ba ina taya abokina murna" Hararar wasa tai mashi tana juyar dakai tana murmushi. "Nidai bana so wlh" Zaro ido yayi yana zama kasa inda ta shimfida mashi darduma yace"abokin naune bakiso kome?" Itama zaro idontai tana rufe baki "nabani ni wlh ban ce ba karka jamun" Dariyar da yajima baiba yau yayi yana kallonta ita kuma ta boye fuskarta tana juya baya. Aransa yaji dadi da hakan ta faru,tabbas yasan duk wadda tasamu malik matsayin miji ta gama morewa,don shima gwanine wajen jawo hankalin mace akanshi,ya tabbata kokarinsa ne tasa har zakiyya take saurarensa kuma da alama tayi na,am da malik din. Shine ya shi go da fara,a yana kallon Abdoul din "alhamdulillah jiki yayi kyau wlh daman nagaji da zaman kasarnan haka gara katashi komunje muji inda tamu maganar ta kwana ko yakikace"yafada yana kallon zakiyya jitake kamar zata nitse awajen tsananin kunyarsu takeji mikewa tai zata fice Ya tare kofar yana leken fuskarta Abdoul murmushi yake masu yana break dinsa. "Ina zaki daga nayi magana shikenan tunda kunya kikeji na daina zoki zauna abunki,inkikatai ina zan iya zaman gadin wannan miskilin mutumen" Dawowa tai ta zauna suka cigaba da hirar su gwanin sha,awa. Har sadda su mami suka karaso. ************** *nigeria* Biki ya kankama don komi anriga da angama yiwa amaren,tundaga kan wani gyara da tsumi iyayen nasu sunyi bakin kokarinsu wajen yin hakan,idan kagansu zaka dauka cikin inji aka sasu aka wanke tass........damuwar da fiyah ke ciki itace ta shafi yesmin,duk yadda take murnar zata kasance da burin ranta idan ta tuna da cewar Addarta bata sanma mijin ba,saidai yakan kirata awaya shima bata taba dauka ba.kuma baya fushi zai sake kira saidai yesmin din ta dauka matsayin fiyar suyi firar ta kashe,tunda ance baya kasar sai karshen shekara yake xuwa amman yanzu da an daura auren zatabi jirgi ta sameshi can. Kwance take tana ta kallon no dinsa duk wasu moments dinsu dashi wanda tundaga kan haduwarsu ta farko da karshen haduwarsu saita fashe da kuka,kukan da tunda akafara hidimar bikin batai ba,don xuciyarta ta dunkule ta dake wanda takejin bata jin akwai abunda zai sake sata kuka ashe fadane kurin tai,haka taita kukan har yesmin ta shigo. "Haba Addata kiyiwa girman Allah kiyi hkr baki isa ki canza kaddararki ba,abunda Allah ya hukunta dole zaki ansheshi hannu bibbiyu,tabbas akwai ciwo akwai tashin hankali amman bamusan dalikin dayasa haka ta faru ba,kidauka Allah sonki yake dahar ya maki musaya da wani kila shine mafi alkairinki........."rungumeta tai tana cewa"yesmin nasani nasan dahaka amman taya zan cire shi daga cikin raina,yesmin yya Abdoul yayi reshe acikin xuciyata har ya fitar da tsiro,duk iyakar kokarina abun ya faskareni,yazanyi haka zanje gidan wani ina fama da wani cikin raina,ina jintsoron Allah ya kamani da wannan laifin" Kukan suke tare mama na baking kofa tanajinsu bata san sadda hawaye suka silalo mata ba,hakika Safiyya na cikin halin damuwa,kuma bata da yadda zatai da damuwar tata zata dai roka mata Allah yasa mata hkr da dangana. Yesmin har anje anmata jerenta unguwarsu Anty jamila,fiyah kuma kudin kayan dakinta baba ya danka mata ga hannunta yace tunda baza,a iya daukar kaya har kasar waje ba yaga bari yabata kudin tayi sana,a idan har mijin yabari acan ma saita karasa karatunta. Rungume baban tai tana kuka yana lallashinta tare daa mata albarka,nasiha yayi masu sosai don yasan ba lallai ya samu amar yi masu ba na da kwaa uku da yarage daurin aure. Dole fihay ta saka danaa dataga dai dagaske auren nan yinsa za,ai taroki allah yasa hakan shine alkairinsu ita dashi,shima allah ya bashi lafiya yakuma samashi juriya da dangana. Ta saduda kodan nasihar da baba yayi mata da kuma wacce yan hwanta suke mata,mama kam kullun ne saita bata baki tana bata labarin irin wadanda akaima aure irin nata da irin nasarar dasuka samu. Baba da Abbin Abdoul sun sasanta don har gaisawa suke yake mashi allah yasa alkairi,ai baisan biki za,ai gidan ba tunda shima baya zaune nan dai har ybashi gudun mawa mai yawa gaske haka dady ma. Tun dawowarsu Abbi yasa aka shiga hidimar gyaran gidanshi ba kama hannun yaro,don rana guda zai aurar da yara uku Amina da zuwairat da haulat.khadija yabarta said ni,ima ta samu miji sai ahadasu. Komi da komi aka canza ma gidan idan ka shigo unguwar bazaka gane shine ba. Sati biyu kacal aka dauka ana gyaran don komi yayi lafiya lau bazata yakeson yiwa su mami idan suka dawo duk da babu ranar dawowar bikin ma duk baifi saura wata guda ba. *Rana bata karya aidai uwar diya taji kunya* 😭😭😭😭ina tay Abdoul kishi tsakani a Allah mom banji di

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});