Chapter 68
Chapter 68
jeka ga waye,karka barkowaye mamman,kakira abokan aikinka kowaye bance ko ragar masa ba muddin asirin mu yatonu kaikanka bazan kyaleka ba." Dagudu ya fita daga dakin........daidai karewar video kenan. Malik kansa akasa yana jin kofafin kansa suna toshewa,wace irin macece ita metake nema ta rasa cikin wannan gidan,wace irin hatsabibiya ce ita harta ke iya aikata irin wadanan abubuwan..........tunawa yayi da irin bakar rayuwar da Alfah yayi,da irin yadda ta bata mashi suna,duk mutanen dake ganinsa da kima da mutunci sun daina,ana mashi kallon dan iska wanda yarasa wadda zai nema sai matar ubansa,yadda rayuwarsa tashiga hadari baisan sanda kuka ya kubce mashi ba mai sauti,wanda rabon dayayi wannan kukan tun sadda yarasa gatan iyaye da danginsa,tunda kuma Abdoul-nasser alfah yashigo rayuwarsa duk wani kuka da kunci yayaye mashi,haske da farin ciki ya maye gurbin bakin cikinsa,amman kwatsam rayuwa tazo ta juya masu baya wannan la,anannar mata tajefa mashi abokinsa amininsa dan uwansa wanda yakejin bayada kamarsa ahalin yanxu,idan baiyyi kuka ba mezaiyyi.........lallashinsa dady yake wanda shima yaji kwallar sa tana cika idonsa. "Karka sare dana,duk wani tsanani yanada sauki,kuma kadauka daman kaddararkuce tazo ta hannunta,hakika hajiya mariya babu shaidaniya irinta,kuma ta daukowa kanfa babban bala,i don nayi alkawari kozan karar dakomi nawa sainaga na sadata da gidanzaman ta na har abada." Haka malik yayita kuka dady yana lallashinsa,daker yayi shiru yace yaje gida zai san yadda yayi yanemi ganin Abbi. Haka malik yafito jikinsa amugun mace daker ma yake jan motar,gabaki daya tsoron duniya da rudin shaidan yashigeshi,mutane suna kai kansu halaka saboda son duniya da abun da ke cikinta. Har yaje gida bai iya dawo wa daidai ba,ayadda ya hango dakin Abdoul idonsa biyu,agogo ya kalla shabiyu da minty goma. Kome yake bai bacci ba da alama dai akwai damuwar data hanashi runtsewa,kallon bedroom din da zakiyya take kwana yayi shima akwai haske,itama batai bacci ba,to meke damun su suduka haka. Baida natsuwar dazai fuskanci koguda acikinsu shiyasa ya wuce shima yayi wanka da sallar isha,i yasha ruwan tea ya kwanta yana sakawa yana kwancewa. 💞💞💞💞💞 Fiyah ce zaune gaban baba tayi shirin fita exam don yau suna da peper. Tare ma suke karya wa mama dan wake tai masu sanan aka dama kunun gyada,suna ci suna hira gwanin sha,awa yesmin na gefe itama ida mama kwanon su guda. Ganin yadda fiyah ta sake take ta annashuwa hakan yayiwa baba dadi,yaga damace daya kamata yayi anfani da ita wajen yi mata zamcen yaron nan muhseen. Cikin jan hankali da natsuwa baban yace"uwata wannan jarabawar itace ta karshen gama aji daya ko?" Tana kurbar kunan gyadar tace"eh baba itace,amman sai munje hutu munkoma mun sake wani karatun munyi wata jarabawar sannan mushiga aji biyu" Jinjina kai yayi yace"masha Allah kinga daman burina biyune akanku kullum keda yesmin," Kallonsa tai tace"baba wane irin buri kake dashi akanmu" Murmushi yayi yace"inason inga kun fadada iliminku bayan na secondary,inga kuma daidai gwargwado ban tauyeku ba kuma kun samu ilimin da zai taimakeku agobenku,bayan nan uwata kullum fata nake da burin Allah ya fiddo maku da mazajenku nagari wadanda zasu rikemun ku cikin amana da mutunci kamar dai yadda uncle dinku hake rike da antynku cikin kwanciyar hankali babu maijin kansu" Gabanta yafadi sosai har ta kasa kai dan waken dake hannunta cikin bakinta tace"baba ai banfa gama karatunba,duk fa ko rabi banba akwai aiki gabanmu sosai" Murmushin yayi yace"ai uwata shi aure baya hana karatu,haka karatu baya hana aure aduk sanda kasamu damar yin guda inhar anyarje maka saikaga kayishi cikin kwanciyar hankali," Gabaki daya ta rude dajin kalaman baba meyake nufi da ita,innalillahi Allah kasa ba wannan shegen muhseen din yazo ma baba da wata magana ba,wlh van sonsa bana sonsa.....idonta yadan caza tace"baba ai babu wanda nake kulawa tunda karatu nake in wani yazo saina gabatar dashi wajenka" Mama kallonta tai ta fahimci wani abu game da diyar tata,idan batai kuskureba tasan maganar da baban ke shirin yi mata,wanda yasa take kakkaucewa. "Ai kwantar da hankalinki uwata,Allah yana sonki don ya kawo maki miji har gida kuma wanda nake maki fatansa da kwadayinsa,badan abun hannunsa ba ko don kudin magabatansa,aa nagartarsa naduba da hankalinsa da natsuwarsa yasa banyi shawara dake ba nai na,am da maganarsa don haka kowane lokaci zaki iya ganinsa yazo wajenki." Bata son fiddo kwallarta gabasan yasa ta sadda kai tana kokowa da kwallar cikin kermar murya tace"waye baba,ni banda wani wanda nakeso kuma ban turo kowa ba wlh" Duk yadda taso karya gane rudewarta saida ya gane yace"kwantar da hankalinki ki natsu uwata,muhseen ne kanen uncle dinku.kema kinsan bashida wata matsala karkiyo tunanin komi,cancanta ce yasa nabashi ke kuma inada yakinin zai kula dake yadda yakamata ahankali zaki fahimceshi kuma har kisoshi." Idan tace zatai magana kukanta bayyana zaiyyi shiru tai tana zare hannunta daga cikin kwanan dan waken,amman kafin ma tatashi yesmin ta rigata ta fice tana tari da alama kware tai. Ahankali kamar wadda kwai ya fashe wa aciki take fita daga dakin,kallon yesmin take durkushe gaban maguji tana kuskure bakinta,idan ba gizo idonta yake ba kwallace ke fita daga idonta,tana gogewa kasa kasa tsura mata ido tai harta wanke fuskarta ta shige dakinsu bata kula fiyah ba. Jinjina kai tayi tana godewa Allah data kawo mata wannan damar,don kuwa bazata iya musawa baba cewa bata son muhseen ba,amman idan ta fahimtar dasu cewar yar uwarta naso hakan zaija hankalinsu su duba maganar. Wajen dalha taje ta anshi kudin taxi tabar unguwar xuciyarta cike da abubuwa. 💞💞💞💞💞 Wayar da akaimashi can caji office yasa ya tashi don bai niyyar fita ko ina ba yau,shiryawa yayi yanayin sa kwata kwata yau ahargitse yake.neman wanda zai juyewa masifar shi yake. Har zaifita idonsa akan jikkar fiya. Dawowa yayi ya dauketa yafifa,ko kallon kitchen baiba inda yake jiyo mktsin mutun yasan zakiyya ce,don har yanzu akuke yake da ita. Driver sa dasuke fita office ne yazo yace"yallabai yau babu office ne" Cikin shan kanshi yace"eh" Juyawa yayi yabarsa don yaga kamar cikin fushi yake. Yadda ya figi motar kasan kiris yake jira,gudu yake don yaje da wuri dpo din yace mashi ga yallabai nan ya sake dawowa neman belin su. Shikuma duk bala,in da za ai da masifar da za,ai bazai bari su kubutaba yau zaifuskanceshi bayan tsawon shekaru,yadda yake nuna mashi shidin ba dansa bane shima zai rufe ido ya nuna baima taba sanin sa ba,idan ma kotu za,axaje akan maganar ashirye yake. Go slow ya tsayar dashi idonsa ya sauka kanta tana cikin taxi,kanta kasa kamar tana duba wani abu. Saurin dauko bag din yayi zaifita saikuma ya fasa,yana son ganinta akebance wannan damace da zaije gidansu anjima. Koma wa yayi yana cigaba da kallonta jiyayi duk wani kuncinsa ya na yayewa,xuciyarsa tana sauka sabanin yadda yakejin wata irin temper tana taso mashi. Kamar kar yatafi yakeji amman babu halin hakan yana gani suka wuce shi shima ya wuce inda zashi. Malik bai tashi da wuri ba sai kusan shadaya wanka yayi yafito yayi break zakiyya ta gaidashi ta shige daki,binta da kallo yayi yana mamakinta to aibashi ya kashe xomun ba. Waya sukai da dady yake tambayarsa Andoul na gida. "Wlh daddy baya nan,yafita tun safe amman bari akirasa aji," "Aa kyalesa nasan inda zaije yana station kan case din safiyyah yana can shida
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101