Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 38

Chapter 38

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,293 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Anty bazaki ji komi ba saidai kihau dukanta,ai ko bakiji bayanin ta ba bakin daki babbar budurwa irin wannan ba,ta wuce bugu ai" Hararasa tayi tana cewa"tare mata zakai,kigaya man gidan ubanda kika tsaya daman kin tsaranine don kitai yawonki ko,to wlh baruwana dadai irin haka gara ki koma gida yafiye mun kwanciyar hankali." Uncle yahya yashigo yasamu tana ta balbalin masifa fiyah banda kuka babu abunda take,don bayan bakincikin Alfah ga wani nan tana kwankwada,meyasa anty bata da uxiri koda yaushe. "Dadina dake bakya da hkr,ko halin data shigo ai kinduba kitambayi lafiya,amman zaki tusata da masifa haba jamila yarinya namaki abun kirki kina neman kureta,safiyya faba yarinya bace tasan kata tanada hankali,bazatayi abunda tasan ranta danaku zaibaci ba.haba wlh banson wannan halin." Muhseen cikin jin haushin bata ma sahibarsa rai da akai yace"dafa marinta zatai da ban tare ba." "Mari!jamila saifiyyar zaki mara,lallai kin kyauta ai" Tashi fiyah tayi tabar wajen cike da bakin ciki tana jiyo muhseen yana mata bayanin abunda yafaru. Bata tsaya jin abunda antyn za tace ba ta shige ta kulle kofarta,ta kudurci da sassafe zata bar mata gidanta ai hakurinta ya kure,Anty jamila bata da uziri kokadan,indai kayi abu bata jiran bayani zata hau balbalin bala i.to tunkan ta koreni nizan kori kaina,ainaga mata moriya tunda gobe suna ko." Wannan dare safiyya bata runtsa shi yadda ya kamata ba,kamar yadda Abdoul ya kwana yana cikin wani yanayi na tunani,sunanta yazauna daram cikin ransa.amman zafin kalamanta sun hana sunan yin tasiri aransa,ko kallon malik bai sake ba tun daya dawo. Sai yakoma ainahin Alfah dinsa na kwanakin baya,wani bangare na zuciyarsa yana tuno masa da wani sashe daya riga ya binne tun shekara shidda baya,saiyakejin kamar feelings na kauna da shauki na soyayya atare dashi,bawai yana yiwa wataba aa yanajinsa atare dashi yana bukatar wadda zai sharing wannan feelings din da ita amman wacece?kenan har xuciyarsa tayi sanyin da zai iya kallon mace da sunan kauna?Aa impossible nayi bikin binne soyayya shekara shidda baya,yana ma mace kallon namiji rabonda dayaji yana son mace kusadashi ko yaji yana bukatar kasancewarta garesa tun wancen lokacin,wanda yakejin kansa koda yaushe cikin shauki da mararin zamanta cikin rayuwarsa. Yau lamarin ya canza masa,kasancewarta gefensa,kukanta sautin muryarta kalamanta sun ja hankalinsa ainun wajen juyoda lamarinsa baya,wani shauki daya danne tsawon lokaci yake niyyar tasowa,duk da yadda tariga ta bata ransa ta cusa haushinta hakan bai hana wannan abun tasiri akansa ba. Mirginawa yayi yana runtse idonsa yanajin wani yanayi kamar zaiyyi kuka,amman ba kukan bane yanajin kamar yayi dariya amma ba dariyar bace,yanajin dukan jikinsa yana macewa,sannan tsikar jikinsa tana tashi salon numfashinsa yana canzawa. Filo ya rarumo ya makalkaleshi yana jan numfashi,ya tattare jikinsa ya dunkulesa waje guda,jujjuya kansa yake yana jiyo wasu kalamai da suka shude suna mashi ansa kuwwa cikin kunne,baiyyi auneba yaji hawayensa suna silalowa suna bin kuncinsa idonsa arufe amman hawayen basu fasa fitanba. Bakinsa ne yake kerma kamar zaifurta wani abu,amman kirjinsa yayi masa nauyi rubdaciki ya koma yana murtsike murtsike kamar mai ciwon ciki,saida bakinsa ya furta wannan suna ya samu sukuni. *"ZAKIYYAH!!!"* wani gauron numfashi ya sauke yana tashi zaune kansa yasa cikin kafafunsa yana zubar da kwallah. Tun bayan barinsa gida yacireta aransa,daidai da rana guda baiyi tunaninta ba bai tuno komi nata ba,baya kallon mace balle ta tuna mashi da ita,shiyasa ya yiwa mata wata irin tsana.wadda har yau yakejin baidaina tsanar suba,don sune silar jefa rayuwarsa cikin garari da damuwa. Amman yau anwayi gari shine yake magana da wata,yake hada jikinsa da wata yake daukar wata cikin motarsa.tsawon zamansa hakan bata taba faruwaba,ko dacan zakiyya kurin yake dauka duk da tarin bataliyar matan dake binsa.kusancinsa da yarinyar nan yau yasaka yaji komi na zakiyya yana dawo mashi..........cikin muryar kuka yace"why zakiya,why why me???." Wannan dare dai Abdoul haka yagansa baisamu sukuni ba saida ya karanta qur ani,sannan yasamu salama har bacci ya daukeshi. Itako fiyah kiri da muzu baccin yace baisan haka ba,tasha kukanta ta gode waAllah.don gabaki daya tarasa inda natsuwarta ta nufa,duk irin Abunda Abdoul yayi mata yau maimakon taji haushinsa kamar yadda ta dawo da abun,amman abun sai yagagareta data hangoshi sanda yake sunkuyowa yana bude mata kofa zataji gabaki daya hankalinta ya tashi,har lokacin tanajin gashinsa ga fuskarta..........mulmula kurin take agefe guda ga hirarta da zakiyya da irin alkawarin data daukar mata cewar zata mallaka mata Abdoul dinta zata dawo mata da soyayyarta.to taya?ta tanbayi kanta wata xuciyar tace ta yadda kika ansa mata ta haka zaki yi kihadasu ki sasanta su. Ga haushin Anty ga na Alfah amman jitake na Alfah baikai na Anty girma ba,duk da kalamansa sun take na antyn girma da munu aman ta kasa ganin bakinsu ayanxu,sabanin lokacin dayake gaya mata su. Tun daren fiyah ta gama hada akwatinta,don data gama abunda xatai saidai ta nemeta ta rasa shikuma wancen muhseen din ya gaji yabarta,inma don yabata wayace aiba rokonsa tayi ba bakuma zata bayar ba,kwata kwata baya cikin shirginta. Zuciyarta tace mata"to saiwa yake cikin shirginki?badai Abdoul din dakika gama yiwa wata alkawarin hadasu ba?" "Mtss mezan da dangiya nikau safiyyah,ai inajin ko maza sukenan shida muhseen bana son su bana aurensu gara na mutu ahaka." Still xuciyarta tace"inkince Abdoul dan giya ne shikuma muhseen mezai hana kisoshi?" Dirkowa tai daga kan gadon tana cewa"ohh ina ruwanki ne kirabu dani don Allah." (🤣🤣🤣) Zaman dirshen tayi kasa tana tagumi. Tunani ta shiga yi daga sanda ya fito daga mota dawowar da yayi daga office,shigarsa tayi kyau rubutun rigarsa ya dauki hankalinta *ME&YOU* lumshe ido tayi tana silalewa kasa ta kwanta bia tayils din dakin. "Nida kai ko,uhmmm saidai idan kaida zakiyya" Idonta alumshe tana tuna sanda yake tsane mata hawayenta,kamshin turatensa mai shegen shiga kwalwa ya kasa barin hancinta.komi nashi mai tsadane. _kuma duk dan iskan kwartonki daya biyoki nan gidan saina guntile mashi kafa alqur,an_ Ta tuna maganarsa sanda tace bazata bisa amotar sa ba, "Wanan Kalmar ta kwartanci tana mata ciwo,wai shi baya ganewa ne meyasa zaimun wannan zargin,wlh Abdoul niba yar iska bace ban shigo rayuwarka don komiba saidon ina tausayinka,saidan na taimakeka ka koma cikin ahalinka,amman meyasa ka kasa fahimta. kenan da haka zaka saka mun.koda yake bana bukatar sakayyarka ladata tana wajen Allah,kuma duk abunda kayimun na yafe maka Allah yasani bana gaya maka wadansu maganganun don karan kaina kaine kakeja,kuma duk don in nuna maka cewar abunda kake babu kyau ba halin kirki bane shan kayan maye,addinin mu yayi hani,Haramunne akwai zunubi mai yawa ina maka fatan shiriya Allah yasa wahalata bata tashi abanza ba." Afili duk take fadar haka kwallah na mata zarya afuska,ta rasa dalilin zubarsu.abunda tasani kawai shine tana tausaya mashi hakan rashin uwa da rashin uba da yan uwa dayake ciki,kowa daya sansa baya mashi kallon mutumen kirki. Shafa kuncinta tayi inda ya mareta dazun cikin mota, Lumshe idonta tayi amman kwata kwata bataji zafin marin ba,cigaba tayi da shafa wajen tana jin haushinsa yana bajewa cikin xuciyarta tausayinsa yana maye gurbin haushin nasa.duk ta duka takare tunda nayi alkarin bazan sake xuwa gidanku ba zangani idan inda rana kokuma banda ita. Shin rashin ganina zai dameka ko bazai dameka ba tsaki taja jin wata xuciyar tana cewa "ke awa zai damu don bakizo bakenan kin saka wani

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});