Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,281 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yafin abaya. Gaskoya yah jalal badai hidima ba Allah yayisa mai zuciyar nema. Don ko acan ba zaune yake ba yana noman rani acan,ga sim card dayake siyarwa yana samu babu laifi ga kuma albashinsa. Ranar mun yini cikin farin ciki da annnashuwa don yah jalal yana sake mamu,duk da shima wani lokacin kamar Anty yake. Baba daya dawo yaga wannan abun arxiki ya ringa saka mashi albarka,yana mashi addua masu kyau.bamu kwanta ba ranar sai sha biyu. Da asuba na kira malik saida na kaikaici yesmin tana bayi. "Yah malik na tasheka da sassafe ko." Gyara kwanciyar sa yayi baccin bayan sallar asuba daya dawo,muryarsa cike da bacci yace "kin cancanci tashina ai,ya kika kwana." "Lafiya lau yah malik,dama nace ina zan sameka zan fito karfe sha biyu." Murmushi yayi yace" gida zaki saman." Zaro ido tayi kamar yana ganinta tace"yah malik gida kuma?nidai aa kafito sai muje wani wajen gaskiya nidai ina tsoron wannan mutumen." Dariya yayi mata don ya cire mata tsoron zuwan yace"ai bainan yau na samu na turashi company." Ajiyar zuciya tayi tace"shikenan,amman ni gaskiya yah malik inajin tsoron sa karya mun wani abun don nasan wlh ya rik'e fuskata." "Karki damu babu abunda zai maki ai inanan." "Shikenan sai anjima." Kashe wayar tayi tana sauke ajiyar xuciya gabanta yana faduwa,tana tausansa tana tsoronsa kuma.sannan burin taimakonsa baixai gushe daga ranta ba har sai taga Abdoulnaseer ya dawo ainahin Abdoul din da kowa ya sani.yesmin ce ta tab'ota tace"Adda tunanin me kike nafito inata magana bakijini ba." Firgigi tayi yadawo natsuwarta "ba komi yesmin,ina tunanin test dina ta jiya kona rubuta ta da kyau gashi yau zai bada ita." "Kai Adda keda duk abunda kika rubuta kinsan kinci kimabar wani kokwanto,ke ai cinyedu ce wlh." Dariya tayi tace"ban son xiga fah,waya kaiki cinyewa keda yah jalal." Nan suka ringa maida magana har gari ya idasa wayewa sukan hau ayyukansu na yau da kullum. Bayan sun gama kalaci yesmin zata wuce makaranta tace ma mama"mama banga baba ba tunda na tashi,gashi zan ta makaranta karna makara." Mama dake shan kunun ta tace"wlh ankirashi ne tunda bayan asuba,har yanxu baidawo yayi kalaci ba,amman kije kisamu yayanku ya baki kudin taxi karki makara." Haka tayi masu sallama ta wuce itama fiyah bayan ta gama duk abunda zatai ta yi wankata kamar yadda ta saba,tasha kyau tsantsagoran sa don fadarsa ma b'ata bakine. Yah jalal ya bata kudin taxi don har lokaci baba baidawo ba. Tana isa k'ofar gidan kirjinta ya buga ta sallami mai taxi din ta shiga koran malik. "Kayo ka shigo dani wlh atsorace nake." Kashewa yayi ya fito yasha wanka malik badai gayu ba."wannan toron naki dole saikin barshi inhar kina son mucimma nasara,don idan yagane kina tsoronsa shikenan kin bani.don haka daure fuska zakiyi kisha mir kuma fuk maganar daya gaya maki kema kigaya mashi fiyeda wacce ya sanar dake,hakan da zakiyi shine zaizamo kamar makari daga zafin ransa akanki,don tabbas gamonki dashi dake nafarko nasan akwai dabi,kinsan randa kika fara zuwa nan gidan ashe yaganki,amman baimun magana ba sai jiya." Gabanta ya fad'i amman tasa dakiya ranta tace"meyace yah mali." Dariya yyi yace"cemun yayi ingayabmaki inhar yasake ganin fuskarki agidan nan saiya ka.......kafinmanyanidasa harta ruga ta koma wajen k'ofa. Mezaiyyi ba dariya ba binta yayi har waje yana dariya yace"kekuwa ya da rugawa karai kicemun kinfasa wlh fadane kurun yake aibazai iya kisaba kalmrce ke bshi nishadi idan yana fad'a don ya torataka.......zomuje don Allah yau nakeson na idasa maki lbr abunda yafaru ko kinyafe." Idonta yayi kwalkwal zatai kuka yadan sausauta dariyar yace"kinga wlh bazai iya yi maki wani abu ina nan ba nagaya maki ma baya nan ba yanzu zai dawo ba,karki damu kinko sofiyya." Badan taso ba ta sake binsa abaya amman fah zuciyarta zillo kurin take........... Mama nata hidimar sanwar rana dambu takeyi masu mai dadi na shinkafa,har ta dora hawan karshe saiga wasu mutane sunyi sallama gidan,abaya ta sanyo ta leko cikin zauren idinta na sauka kansu hankalinta yatashi cikin rudewa tace"jamiai lfy kodai b'atan kai kukai." Daya daga cikinsu yace"munzo sanar dake ne mininki yana police station,an kamashi ne da laifin rashin d'a,a ga Alh muazzam canji don haka karku sha wuyar nemansa don yana wajenmu,ba kuma zai fito don yanzunba mun barki lfy,amman karku sha hawalar zuwa belin sa don babu beli saiyaje yari." Silalewa tayi kasa cikin zauren ta fashe da kuka. Mrs bb ce Mom muhseen 09034722970. Muddin comment bai haura 70% ba *ABDOUL-NASEER ZAI KOMA NA KUDI KOKUMA NA DAINA TYPING HAR SAI NAGA CANJI DAGA GAREKU.* [9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........14 Wajen da ya sauketa wancen lokacin nan ya sake saukarta,bayan ta zauna yadan rusuna yace"hajiya me zakisha." Murmushi tayi tana waigen nayanta tace"rufan asiri kaganni ko airport ni ban tab'a zuwa ba,amman karka damu kanka wlh bana son komi nidai kayi ka idasa mun infece kafin wannan boss din naka ya dawo." Dariya yayi yana jan kujera ya zauna yace"kinga can gashi can cikin d'akin exercise yana ta faman G-ming kawai dai abunda zakiyi ya taimakeki fiyah shine jajircewa,da fitar sa tsoro acikin ranki koda kinajin tsoron karkibari ya fito kan fuskarki kisha mur kuma duk abunda ya fada maki kiyi kokarin maida mashi wadda ya gaya maki,koma fiye da haka ki fetsare idonki gabanshi,shine zaisa ya sassauta maki kuma hakan zai baki damar shiga jikinsa kuma duk abunda kika zomashi dashi zai yarda." Murmushi tayi tace"uhmmm yah malik kenan nidai ina jinka kawai aman ina ni ina mayarwa da wancen gagaren magana." Dariya yayi ya cigaba da sanar da ita cewa. "Alh kwangila ne yace ma Abbi Alh muazzam zaman wannan yaron cikin iyalinka masiface babba,kamar yadda hajiya umma tace ka korai tokuwa hakan yafi dacewa,ka rabashi da kai ka ahalinka wannan shine mafita inba haka ba............cikin zafin rai da kunan zuciya Alfah ya shak'oshi iyakar karfinsa,ya ringa naushi ga fuska har hakorinsa ya fita,kuka yake yana cewa muryarsa duk ta dishe don kuka karya kake munafuki wlh baka isa ba kana gudun na fallasa.......kafin ya idasa abunda yakeson fada Mutanen wajen suka ringa janshi suna raba shi da Alh kwangila,daker aka rabasu inkinga yadda kirjinsa yake d'agawa saikin zata xuciyarsa fitowa zatai.Abbi ne ya iso wajen yana huci ya fizgoshi bai diresa ko inaba sai gaban mami wadda sai lokacin ta samu hawayen yin kuka,cikin kakkausar murya yace"zan fad'a gaban kowa kuma gabanki,daga rana mai kamar ta yau babuni babu Abdoulnasser na yafeshi daga cikin zuria ta,na barshi har abadan abada sanan wlh wlh wlh duk wanda na kama cikin yaran gidannan yana muamala dashi aboye ko azahiri wlh zaibisa,yadda na korai shima haka zaibisa.ba ga yara ba harke ushe muddin kika bibiyesa ko awaya ko zahiri daga ranar abakin aurenki,kidauka koda ban gani ba to ranar zakibar gidana..........yanzu ba sai anjima ba nakeson ka tattara komatsanka da wancen yaron da ka kwaso ka kawo mun agida,waya sani koshine ya koya maka kufitar mun agida yanzu,kuma karka bari ink'arayin arba da bakaken fuskokin ku,inba haka ba wlh sawa zanyi adaureku har tsawon rayuwarku........bazan anshe duk abunda ka samu daga jikina ba don wannan nayi makane domin Allah da

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});