Chapter 58
Chapter 58
baban?" Bata san sanda muryarta take komawa yar karama ba tace"yana samun sauki,may be gobe musamu asallamesa" "Okay" Jin muryarta yake kamar yau yafara jinta,tundaga yatsansa na kafa yajin wani yanayi har cikin kansa,shirun itama tayi tana kwance kamar zata tsaga katifar tashige cikinta. "Ina zakiyya?" Bude idonsa yayi yabin hanyar dakinta da kallo,sai yasamu kansa cewa"gata nan kusa dani" Wani kullutune yazo mata wuya ya tsaya,duk miyan da take hadiyewa yaki wucewa,shiru tayi shikuma yasake anfani da yin shirunta yace"yana mun firane inasamu bacci,taje ta hado mun tea insha idan ta dawo zan baki saiku gaisa" Runtse idonta tai tana damkar zanen gado tare da sauke wani wahalellen nishi,mai tafe da hawaye.saurin rufe bakinta tai don ba wuya kukan na iya tahowa. "Are u on the line" Shiru tayi tana sake rufe bakinta,tana kukanta ahankali can kasa sosai. Natsuwa yayi don fahimtar yanayin ta,ahankali yakejin numfashinta yana sauka da sauri,yanayin kukanta yana shiga kunnensa. Tsikar jikinsa ce tatashi don kukan ta yatada mashi hankali ainun. Kin nuna mata yayi badan hakan baya taba shi ba,aa yana tabashi har cikin ransa amman dole zai bita ahaka badan yaso ba. *"sofiyyerh"* Ahankali cikin voice dinta data sha kuka tace"naam" Runtse ido yayi yana damke hannunsa jiyake kamar tana tafiya da numfashinsa,muryarsa silently so sweet yace"kina kuka ne" Daker tace "uh uh" "To menene?bakison zakiyya na mun firane" Ajiyar xuciya ta sauke tace"ina ruwana da hirar da take maka,meye nawa idan nace kar ta maka fira,kunfi kusa ai karka sake sani cikin batunku pls" Murmushin da bai shirya ba yayi har tana jin sautinsa yace"oky don't worry baza asake ba,hope kinyi exams lafiya" Kin bashi ansa tai tace"zanyi bacci saida safe" Lauya muryar yayi yace"oh sorry to kiyi baccin ki mana,zan so haka ma" Tsaki taja kasa kasa tace"kashe wayarka" "Kekika kirani ashe?" "Ban Sani na malam karka mun gori ai ban roki kakira ni ba balle ka raina mun hankali," Dariya tafara cinsa wadda bazaice ga lokaci. Daya yita ba. "Masifatu kurin,karki sake ki mun rashin kuya wlh har nan kan gadon naki zanzo na baki punishment,wanda nasan zai ladaftar dake." Yafada da wata irin murya hade da salo wanda nan take ya idasa kashe bakin fiyar. Shirunta dayaji yasa yayi murmushi don yasan sakon yaje,dariya yayi ta burgewa yace"matsoraciya,har kin tsorata da wuri tun kafin ma inzo,uhmm kinsan hukuncin naki ashe shiyasa kikai shiru." Ahankali kamar mai koyon magana tace"angaya maka ni Allahn musuruce dallah can saida safe karka sake kirana" "Okay Zane ringa kiranki sau uku arana,yayi maki ko" Tsaki taja tace cikin masifa"dalla cewa nai karka sake kirana" "Oh yayi maki kadan sau ukun,kenan sau biyar zan kira din." Batasan dariya ta kubce mata ba,don yadda yake juya mata magana abun ma saiya bata dariya. Shima taya ta yayi da murmushi mai tsada wanda da agabanta yake saita kusan suma don yadda zai daukar mata hankali. "Angaya maka ina bukatar kiranka?to inkakira ni mezan maka kokuma meza kaimun" Kamar yana rada yace"wai in ringa ladabtar da bakin nan naki mai rashin kunya" Babu shiri tayanke wayar don yama shirin kaita inda bata da mai maidota. Wanna dare dai xukatan mutun uku basu huta ba,zakiyya sabon son Abdoul dinne yayi mata dirar mikiya,jitake kamar yanzu ne tafara sosan bata da wani fata da burin taga sun june har takaisu ga mallakar juna,amman tasan akwai kalubale sosai don Abdoul hankalinsa baya kanta ahalin yanxu,ya zatai ta dawo da soyayuarta sabuwa cikin ransa. *SOFIYYAH* wata xuciyar ta anbata mata tabbas zata iya daidaita su har ma kilan sudawo sufi da son juna,zata nemota itace kurin hope dinta. Abdul kuwa saida yayi dagaske sannan ya samu bacci don kwata kwata xuciyarsa babu komi ciki sai shaukin son kasamcewa da wannan yarinya mai daukar hankali,gabaki daya baisan yadda zai misalta yadda yakeji ba,shidai yasan yana shan wuyar kewarta na kwana biyunnan. Haka yake ga fiya murje murje taitayi agado xuciyarta tana saka mata tana kwance mata,amman kishin zakiyya yaddane duk wani feelings dinta akanshi,hakika yadda takeji ga xuciyarta bazata iya shiga tsakaninsa da zakiyya ba,don ita masaniya gareta akan soyayyarsu.koda xuciyarta tayi kokarin ganin ta kaita inda bata dace da wajen ba,ita zata janye kanta.don bata iya daukar rebel sai goshin asuba bacci ya dauketa. Washe gari da wuri tatai school don eight sukeda exams yau sai shidda zasu dawo gida,don ko break bata tsaya ba feea na xuwa suka wuce yau da mota tafito. Mama tace idan tataso tayo gida kurin don da rana zasu sallamesa suyo gida. Malik saida yaje store yaduba yadda abubuwan suke tafiya sannan yaje company shima yarage wasu ayyukan kafin yakira dady don yaji yaushe yake zaune su idasa sauraren wannan Audio din. "Malik kabari sai dare yanzu haka ma ban garin,amman immediately dana dawo zan kiraka" "To daddy Allah yadawo dakai lafiya,ni sonake ma muzo da Abdoul yaji komi" "Aa karka zodashi yanzu bayada lafiya,tattalinsa ake idan har yaji ayanzu komi zai iya faruwa,kabari ya kara samun lafiya inso samune lokacin sun daidaita da safiyya abun zaifi sauki,duk yadda yahau zata iya sassauto dashi kagane menake nufi ko" Malik yace"hakane kuma dady shikenan Allah ya dawo dakai lafiya" Sukai sallama ya cigaba da aikinsa yana ganawa da costomers daga kasashe daban badan,kullum kamfaninsu kara cigaba yake yanzu haka yaga wasu schedule da Abdoul din ya rubuta cewar zai bude reshen kasuwancinsa can Australia,sannan zai ake fadada store dinsa zai sake hude wani wanda yafishi kayan nagartattau kuma masu kyau.amman baikai ga sanar da malik din ba shine dai yaga takardar cikin drower dinsa na adana muhimman abubuwansa. An sallami baba jikinsa alhamdulillah,yana dan taka kafar amma ba sosai ba,sun bashi yar sandar dazai ringa dogarawa har xuwa sanda zai take dakansa. Muhseen ne yazo daidai sanda zasu tafi gida,mafarin kenan ya daukesu amotarshi suka taho gida,yesmin keta mashi surutu duk da kasancewarta ba mai magama ba sosai amman saita samu kanta da yiwa muhseen din labari,har saida mama ta kwatseta sannan ta bari. Dariya muhseen din yayi yace"mama kibarta inajin dadin hirar,munada irinta gida ai ba takura man tai ba," baba yace ta kyalesu. Dole mama ta samasu ido tsayawa yayi yayi musu siyayya mai sunan siyayya,ledoji uku manya babu wanda ya damu don basusan cewar nasu bane da tun wajen baba yayi fada. Muhseen kau ya kudiri yau bazai tai ba saiyayi ma baba maganar fiyah,don yagaji da dakon kaunarta bacin ita bata shi tae a,hakan dazai mata shine zaisa dole ta kulashi ahankali tasoshi ga baya. Cefane ne leda guda sai dankalin turawa tiya uku sai naman miya na dubu biyar,sai fruits cike da wata leda ayaba ce kankana ce gwandace da abarba harda apple. Saida sukaga yana shigo dasu yesmin nataya shi sannan suka san ashe su yasiya mawa nan fa aba yayita fada yana cewa ya dauke yakai can gidansu meyaa zaiyyi dawainiya dasu har haka. Mama dai shiru tayi don ranta yabata wani abu,amman babu kyau zargi tabari maganar tafasu sannan. Anan muhseen yadade har akai sallar la,asar bayan yadawone yashiga zaima baba sallama yadurkusa yana sosa kai yace"baba zan tai ubangiji ya sa kaffarane Allah kuma ya kiyaue gaba" Sosai baban yaji dadi yaringa saka mashi albarka tare da mashi addua mai kyau,kasa tashi yayi bakinsa kuma sai yayi nauyi,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101