Chapter 7
Chapter 7
zaka daga kazamin hanunka ka mari y'ata,idan iyayenka da kayiwa sun kyaleka to kuwa banga ubanda ya isa ya hanani kulleka ba wlh,muddin ba hkr kabayar ba." Feea dake bayansa idonta yaraina fata don ganin yadda fuskar Alfah tayi babu rahma ko kadan,kiris yake jira yajuye tirar dake cinsa. "Abba kabari wlh nidai dayayi wa na yafe,na hakura kazo mutai." Zare mata ido yayi yace wa DPO "ku kullesa har sai nina bada damar fiddoshi"aguje malik ya iso wajen yana tare Alfah agigice yace"baza su sake kullesan ba wlh,sannan kushiga taitayinku zaku yi dana sani akan hakan." Alhaji kwangila shima cikin bala,i yace"ubansa kadai zaizo nan na hakura kuma bazai tab'a zuwaba domin kuwa wannan dan iskan yaron ya riga yafita daga cikin zuriar su,kunsan kuwa abunda yayi kunsan irin bala,in dayayi har iyayensa suka korai to bari kuji wannan dakuke gani,matar.............jikake tas tatas Alfah ne tsaye gaban Alhaji kwangila ya wankesa da kyawawan maruka har uku. idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,dai-dai sadda wani babban mutun yashigo station din wada tacika da mutane,cikin shakewar murya da ta dishe saboda tsananin bacin rai "wlh kasake furta magana marar dadi akaina saina kasheka,saina fiddo yan hanjinka don ubanka katon banza katon wofi,b'arawon gwamnati baka iya komi ba sai yad'a karya da sharri.........kai *Abdoul-nasser* kul akul nace in ka sake magana saina sasab'a maka awajen nan." Wannan babban mutumen daya shigo yanzu yake fad'ar haka. Ajiye hannunsa yayi da yake nunnuna Alhaji kwangila dashi kamar zai kaimashi naushi,huci yake fiddawa yanajin kamar yadunga dukan bango kozai huce haushinsa......yace"Daddykabarni na koya mai hankali,kabarni na keta mashi rashin mutunci.ni....ni..zai....wulak'anta.......sai wasu zafafan hawaye suka shiga zarya kan kuncinsa. Malik kanshi hawayen yake na tausayin amininsa kuma dan uwansa. Mutumen yace"nadai ce karka sake magana idan ba haka ba zaka ga b'acin raina. tunda ya shigo duk aka k'ame ana sara mai,saboda shine comissioner of police. kallon su yake shima fuskarsa babu walwala ya kalli Alhaji kwangila yace" kagani ko,u see i tall u last time ka guji tun karar shi kar watarana ya baka kunya,Abdoul ba kunya ce ta isheshiba tun wancen karon balle yanzu da yasake firgicewa baijin kunyar yaga maka rigar mutunci,gashi kuma hakan akai bacin malik yaje ya kirani da banson iyakar abunda zai maka ba wlh awajen nan." Zufa yake share wa yana jinjina kai duk ya gigice,feea na gefe na kuka ganin yadda aka wanke ubanta da mafi,wanda yafi nata. fiyah kuwa kamar kazar da aka tsamota daga cikin ruwan zafi,duk ta firgice. Cikin taushin murya Alhaji kwangila yace ma mutumen daya ke magana "nagane hakan Alh maude,zan kiyaye." Alh ya kalli Alfah dake huci kamar tukunyar da aka gama sanwa da ita yace mashi. "Abdoul." Kallonsa yayi ido jawur batare da yace komi ba,yace"wuce kutai gida zanzo in sameku,malik idan yayi wani misbehave tell me." Jinjina kai malik yayi yana cewa"thank u Daddy." Jinjina kai yayi kurin yana cewa Alhaji kwangila "kana iya koma wa ga aikin ka,amman ka kiyaye don wataran abunda yafi haka zai maka,kekuma kiyi hkr kiyiwa Abdoul uziri ba halinsa bane." Feea dake hawaye tace"wlh ni daman nace mashi nayi hkr shine yace sai ya kullesa." Girgiza kai Alh maude yayi yace "uhm shikenan kawai kuna iya tafiya zanje namasa nasiha anjima." Kamar kububuwa Haka Alfah yafito daga station d'in,malik binsan yake cikin sauri don yasan wannan fushin sai yayi kwana uku yana yinsa,inbai samu wanda yajuye haushin sa akai ba. Tuni fiyah ta yanki hanyarta,don tace ma feea bazata bisu ba akwai inda zata bata d burin daya wuce tasan waye wannan guy d'in,ita sai take ganin kamar yana mata kama da yaran gidan *ALH MU'AZZAM CANJI* amman zuciyarta ta kasa yardar mata da haka,saboda in d'an gidanne mezai fiddoshi daga gidan yazo yana irin wannan rayuwar,girgiza kai tayi tanajin matukar tsananin tausayinsa na cika zuciyarta. Hango malik tayi ya tare masu taxi gudu-gudu sauri-sauri haka take had'awa har ta samu ta tari itama taxi d'in tace mai yabisu baya,binsu yake har k'ofar gidansu tace yayi parking daga nesa, Azafafe ya bude kofar motar yafito, sai soka hannunsa yake cikin kansa yana ya mutsa kyakkyawar sumarsa kamar ta larabawa,isa yayi bakin get din gidan nasu yana jiran malik dazai sallami mai taxi,dora hannunsa yayi ga bango sannan ya aza kanshi sama,daka kallai kasan yana cikin wani irin hali. Hawaye taji sun sulalo mata bata ma sani ba. malik ya iso inda yake yana bude masu karamar kofar shiga,yana mashi magana amman bazata iya juyo abunda yake cemai ba.saida taga shigarsu sannan tace ma mai taxin ya kaita maitama estate. Don lectures din da zata koma tayi anriga angama,kuma daman ita kadai ta rage mata. Har taje gida tana hawaye,ganin sun kusa isa yasa ta goge kwallarta tana daidaita natsuwarta,sallamarsa tayi ta wuto zata shiga gidan, ganin buta tayi bakin shagonsu ta dauka ta wanke fuskarta,yadda baza,ai mata tambayar kukan me tayi ba. "Sofiyya yau ba magana." Maitsaron shagonne yayi mata maganar,watau dalha cousin dinsu ne ta wajen mahaifiyarsu,sadda aka gama had'a shagon ta je har rimi ta daukoshi don daman zaman banza yake acan. Rimi garine cikin katsina Cikin rashi kuzari ta juyo tana yak'e tace"ayya d'alha wlh nagaji ina sauri inshiga gida,sannu da aiki ya kasuwar." Murmushi yayi yace"da godiya,maza hanzarta kar acinye babu ke." Murmushi mai kyau tayi ta shige tabarsa. Sallama tayi yesmin dake kwashe shanya ta ansa mata. "Sannu Adda kin shawo rana." Jinjina kai tayi ba ta bata ansa ba,bin bayanta tayi da kallo cike da nazarinta,da alama Adda na cikin damuwa. Mamace tafito daga cikin daki tace"kamar sallamar fiyah naji ko." Yesmin dake linke zane tace cikin rashin jin dadin ganin yayar tata haka "itace mama,amman kamar bata da lfiya tashige d'aki." "Subhanallahi,bari inje inji." D'akin nasu ta shiga tana kiranta,bata cikin dakin amman jiyo karar ruwa cikin bayinsu yasa tajuya, tabarta ta fito. Haka Allah ya yi sofiyya da daukar damuwar wani ta zama tata,mace ce mai tsananin tausayi abu kadan zai karya mata zuciya,duk da halayenta sunda yawa amman abu mafi bayyana tare da ita shine,san yinta kafin kaga zafin ta zaka jima sannan akwai zurfin ciki sosai,tana da shanye damuwa abu zai jima yana damunta bata bayyana shi ba. Wankan ta fito tana shafa amman yanayin fuskarsa take hangowa,da zafafan kalaman da abban feea yake gaya mai,runtse ido tayi hango yadda idonsa yayi jajawur gwananin ban tsoro........haka ta gama murza man ta saka kaya marasa nauyi tayi sallar azahar da la,asar sannan ta fito tsakar gidan. Mama da yesmin nata hira tazo ta zauna,ta dora kanta bisa cinyar maman tana shagwabe fuska. "Mama yunwa nakeji." Shafa kanta take tace"yesmin dauko wa Addarki d'anwakenta yau mutumen ki akai zakici ko." Daga kai tayi tana sake narkewa daman fiyah badai shagwaba ba,ajiye mata yesmin tayi tana cewa"Adda d'azun ina magana baki tanka niba." Murmushi tayi mata mai sanyi tace"sorry my little,ban cikin natsuwa ne kiyi hkr kinjiko." Tana murmushi tace "bakomi Adda nayafe maki,kinje gidan Antyn." D'an waken take ci cikin rashin kuzari,har yanxu amon muryarsa takeji sadda yake mayar wa da Abban feea magama cikin,kunci da bayyana bakin cikin da yake ciki.kamar bazata tan ka ba tace"banje ba yesmin,ban samu time ba kilan sai gobe." Ko kwatar dan waken bata ciba ta ajiye tace "na k'oshi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101