Chapter 26
Chapter 26
ji yabud'e k'ofar yafiro rataye da jikarsa,dayan hannun kima jaye da trolley sa bai kula sa ba yayi gaba sannan yace"inkana iya kaini airport bismillah inkuma baka iya wa naje na hau taxi." Yana gama fadar haka ya wucesa zuwa waje. Mamaki ya daskarar da malik,ganin sabon canjin Abdoul daya zo dashi yanzu.yajima kafin wani kayataccen murmushi ya kubce masa,yana daka tsalle yace "yesssss,wlh anfara nasara gaskiya ngd sofiyyah,wlh aikinki yana kyau." Ficewa yayi da sauri yaje ya samai amota. Har sukaje filin jirgi malik sai surutu yake masa cike da jin dadi,kuma yauce ranar da Alfah bai dakatar dashi daga surutun da yake masa ba,da dane cikin tawa zaice ko kamun shiru kona bar maka motar. Har jirginsu ya tashi Alfah bai takama malik ba,sai kalma guda daya ce masa da ta sake jefashi cikin farinciki. Cewar da yayi..... _TAKE CARE FOR UR SELF_ koda Alfah ya zauna babu abunda yake sai tunani,kalaman yarinyar suke ta mashi amsa kuwwa cikin kunne, duk sanda yajisu sai yaji wata suka cikin kirjinsa....... _macuci azzalumi mak'etaci baka san komi ba sari zallar cuta da shaye shaye,taya zakaji feeling din tausayi cikin ranka ai bana tantama inkace zakai kisan kai,don kuwa y'an shaye shaye kamarka babu abunda basa yi,wannan la,anannar giyar babu abunda bata sawa.wani ma saboda ita uwarsa yayi wa fyade._ Runtse idonsa yayi yana karairaya glass din dake hannunsa,jiyake kamar ya fashe.......... _wannan la,anannanr giyar babu abunda bata sawa. wani ma saboda ita uwarsa yayi wa fyade._ Ya sakejin kalaman suna sauka acikin kunnensa......duk'ewa yayi yana dafe kunnensa,wata dake bayansa ta lura da halin dayake ciki ta d'an tab'osa kad'an. Afirgice ya d'ago kamar wani tab'ab'b'e ya zuba mata dara daran idonsa,babu arxiki tayi saurin koma wa inda take. Durk'ushewar yasake yi yana jin kamar ya kurma ihu ko zaiji saukin masifar dake addabarsa cikin rai. *kuyi hkr yau ban yi posting kan lokaci ba wlh bamu samu wuta ba shiyasa,kuma kuyi maleji dashi wlh banda time ne.* Mrs bb ce Mom muhseen 09034722970. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........20 Malik ya kasa samun natsuwa saboda farincikin da yake ciki,so yake yasamu wani yayi sharing feelings dinsa dashi,fiyah ce ta fado masa ya lumshe ido yana murmushi mai kyau......zama yayi yana cigaba da murmushin,kafin tausayinta ya cika masa xuciya yasan tana can cikin halin ciwo wayarsa ya lalubo gaban aljihun rigarsa yana dailing no dinta,ta jima tana ringing ba adauka ba yabari bayan sallar isha,i ya sake kira. Tashi yayi ya nufi masallaci don baisan rasa jam,I yana son ya sake rok'on Allah daya cigaba da basu sa,a akan Abdoul.don wannan nasarar tayau tayi tsananin sakashi cikin nishad'i inama zaisamu damar yin waya da mami ya bata labarin halin da d'anta mafi soyuwa agareta yakeciki,amman yaji kashedin Abbi bazai so yayi silar barinta wannan gidan ba bayan duk wadannan k'alubalen dasuka faru. 💞💞💞💞💞 Yau suna cikin farin ciki don gaba ki dayansu suna kan tabarma tsakar gida suna hirar da suka jima basuyi na kwana biyi da babu baba. Kowa ka kalla zaka gansa cikin Annashuwa da farinciki,amman fuskar fiyah da saukin walwala,duk motsin da zatai bak'ak'en kalaman Abdoul suke dawo mata cikin kanta,saidai ta fakaici idonsu ta goge kwalla,har baban ya lura yace"halan sofiyyah rigimarce ta motsa,meke damunki naga kwata kwata hankalinki baya nan." Danne kwalarta tayi tace"aa baba ciwukan nne suke man zafi,inakuma son in kwanta." Cikin tausayawa yace"Ayya sannu to,anshi paracitomal kisha ga mamanki zaki samu sauki saikije ki kwanta tunda kinci abinci." Kamar jira take ta tashi ta shiga d'akin mamar ta dauko maganin tasha sannan tayi masu saida safe ta shige d'aki. Koda taga misscall din malik bata bisa ba,don shima haushin sa takeji inbacin shi aida haka bata sameta ba,baida abun sanar da ita yasata tazo wannan marar imanin yakusan kasheta.......hawaye ta share tana jin wata zuciyar tana bata shawara akan ta rabu da wannam wahalar,ina dalili kana niyyar taimakon mutum shikuma baida aiki saina kashe kashe da neman makasarka.,bayi ta wuce tayo Alwallah daker tayi shafa,i da wutri sannan tatashi karatun kur ani tayi kadan,sannan ta ajiye tana jin kewar isalamiya na damunta,don lectures dinsu yanzu duk na yamma ne su suka hanata zuwa. Kwanciyarta kenan malik ya sake kira dogon tsaki taja tana danne wayar da fillow,amman zuciyarta na son dauka don gani take tayi masa wulakanci........bayarda ta iya ta daga filon ta dauko wayar,daidai sanda ya sake kira.dagawa tayi tana kangawa ga kunne hawayenta kuma sunata zuba,cikin shashshekar kuka tace"nidai yaya malik wlh nagaji,nagaji hakanan da wannan masifar,Allah ya sani niba yar iska bace ban san ma me ake nufi da kalmar ba,amman zai ringa aibatani yana cewa inyi yawo tsirara." .......sai kuka ya kubce mata duk yabi ya d'imauce ya ma rasa mezaice mata cikin kermar murya yace"kinga fiyah kiyi hkr don Allah kiyi hkr wlh Abdoul bai kyauta ba,kuma nima saida nai mashi fad'a bazai sake kwatanta maki irin haka ba,amman ki cire batun cewa kin gaji Ai daman inhar kana aikin lada dole zakasha wuya,kiyi hkr ladarki tana wajen Allah amman karkice kingaji karma zuciyarki ta sama ki fasa niyyarki." Tana share kwalla tace cikin raunin murya"yaya malik baka ga fa yadda ya saka kafafuna su kai ba,kilama ban iya sake tafiya"ta sake rushewa da kuka......dafe kai yayi yana murmushi lallai akwai shagwab'a nan wajen,danne dariyarsa yayi yace cikin tausaya wa. "Ayya y'ar kanwar malik,ya zakice haka kinga kidaina insha Allah babu abunda zai samu kafarki,kindai sha magani ko." Cikin kuka k'asa-k'asa tace"uhm" Ajiyar xuciya ya sauke yace"duk kin rud'ani wlh,nakiraki ina murna da d'okin samar dake wani labari kuma sai najiki ahaka." Dandanan ta wartsake tana goge sauran kwallarta tace"gaya man menene." Cire wayar yayi daga kunnensa yayi dariyar san ronsa sannan ya mayar yace"akan mutumenki ne." "Mts!nikadai na ban son ma ni ko sunan sa inji." Dariya yayi yace"sorry mana ansafiyya na,kiyi hkr kiyafe mashi kinjiko watarana da kanshi zaibaki hkr." Zaro ido tayi kamar yana ganinta tace"wannan dan zafin kan lallai! kaima yaya malik ka fad'a don tsokana." Dariya yayi yace"am serious kiyi ta mashi Addua zakisha mamaki,yanzufa yau abunda yayi ya ban mamaki sosai." Yabata lbr abunda yafaru d'azun. Itama tasha mamaki hartake jin ai yanzu ma ta ska k'afa cikin rayuwarsa har sai inda karfinta yakare,saita ga abunda ya turewa buxu nad'insa cikin jin dadi tace "Ashe abunda nake har zai iya canza sa zuwa haka yaya malik." Cikin tabbatar wa yace"sosai ma kuwa yar kanwata,kisake dagewa inyadawo sai kidora daga inda kika tsaya,idan da halima kicanza salo." Dariya tayi tace"kai yaya malik wai incanza salo uhm,zanyi dai bakin kokarina amman katabbatar da bazai sake shak'eni na." Dariya yake sosai yace"bazai kara ba aiyau nai masa fad'a sosai wanda ban tab'a masa ba kuma baiyyi fushiba,don da yayi ba zai mun magama ba." Tace"insha Allah i will try my best." Sunjima yana janta da hira har saidantaji yasmin zata shigo ta latse wayar tayi adduo inta kamar kullum suka kwanta. 💞 *Australia*💞 jirginsu yana sauka mutanen sa suka zo suka d'auke shi zuwa hotel d'in da zai sauka,don saukar dare yayi zuwa safe aroud 9:00 zasu fara abunda ya kawosu. Bin garin yake da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101