Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,287 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

muhseen,wanda dandanan sabo yashiga tsakaninsa da baban saboda yadda yakeda faranfaran da barkwanci,bayada bakunta kokadan.koda fiyah ta isa ma bai jima da tafiya ba,ta samu sai labarin suke gabanta yafadi badai muhseen ta nan yabiyo ba? Har dare suna tare da baba saida tara tai sannan suka tafi cike da mashi Adduar warkewa da wuri yadawo gida don suna kewarsa,yaya jalal gobe yana bisa hanya sunyi waya da baba. Koda sukaje gida fiyah wanka tai ta saka kayan bacci daman sunci abinci dare can asibitin,wanda mami ta aiko driver dashi yayi dadi sosai ga nama zuku zuku aciki,da lemu. Yesmin yauma tana wajen mama goma nayi suka rufe gida daman dalha shagon kofar gida yake kwana. Karatun ta take na exam duka da daman tariga duk ta rage yawanshi sai wasu wurare da basuda yawa,gajiya tai don duk maimaice take yi tariga ta haddace su tas. Hamma takeyi ta ajiye hand out din gefe da asuba tasake bita,har yanxu xuciyarta bata jin dadinta,wata irin kewa takeji jitake kamar ita daya take yawo acikin sararin samaniya.kwanciyatai tana yin lamo badan bacci ba,kamar wasa tajiyo rurin wayarta xunbur tayi tatashi tana rarumota,sunan malik taga ana yawo akan wayar tatashi sosai tana daga wayar "Assalamu alaikum yaya malik ina wuni" Shiru taji anyi ta duba wayar taga har lokacin wayar tana tafiya,sake magana tai. "Yaya malik inata magana lafiya kuwa" Ahankali taji wani sauti daya jefa xuciyarta cikin wani mugun shauki,taji gabaki daya duk wani karfi najikinta yana macewa,wata kasala na zuwa tana lillibeta bata san sadda idonta suka lumshe ba,wani abu yana bin duk ilahirin jikinata. Jitai yasake cewa. *"safiyyah"* Kadan ya hana bata yi sumar wucin gadi ba. Sorry Muhadu gobe at this time.don sanyin idaniya kurin zanyi dasafe alfah sai kamar yanzu. Don't share it plz I beg u Bcos its for sale. 300 naira only [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........40 Nuna ma dadyn yayi yace"gasunan dady zamu fara da videon ne ko mu gama sauraren audion sannan" Bayan ya duba yace "kunna audion muji" Jikin malik na rawa ya ja aro din computer zuwa wajen audio ya yi double click dinsa,dan danan yafara loading zai bude.sudukan gabansu ke faduwa don basu san me zasu saurara ba,yadauki almost 3mint sannan ya bude muryace tafara magana,wadda nan take suka dago ko murya waye. Watau muryar umma tana cewa"kwangila ina cikin tashin hankali,bacin tsana da kiyyar danake yiwa Yaron nan Abdoul nasser ya sake jefa kanshi cikin wani bala,in domin kuwa ajiya ina mai tabbatar maka da cewar ya gannmu sadda muke aikata son ranmu,idona idonsa bakin window wlh har ihun da kake yi akan kunnensa har saida yatoshe kunnensa,yajinjina kai yayi kwana yabar wajen.duk da nasan bazai gaya makowa ba dole ne mudauki mataki akansa,don kuwa zai zamemana barazana ga zamanmu dagani har kai" Alh kwangila ya sauke numfashi yana share gumi yace"innalillahi nashiga uku wane irin bakin labari kike gaya mun,har kice bazai sanar dakowa ba taya kikasan haka,to gaskiya niba zan dauki lokaci waje ganin mun kubuta tunda bacin shi babu wanda yasan ina zuwa wajenki muna muamala dajuna,kuma bacin haka mariya banajin akwai wanda xai dakatar dani daga muamala dake,kin sani tun kuna farkon xuwa unguwar nan nazama mijinki na biyu,kina mun dadin da matana bata taimun,don haka dolene zai dauki mummuna mataki akansa,kinga hanyar dakike nema wajen ganin kin kawar dashi daga gidan,domin kisamu damar tattare komi kafin plan B ya fara aiki ko" Dariya suka kwashe suduka harda sautin kashewa dasukai dajuna,tace"in maka na turawa zat wai ai lobiyu"suka sake kwashe wa da dariya kamar mahaukata. Yace"yanzu kina da wata dubara kowata shawarar yadda zamufara bulloma lamarin ko kinbar komi hannuna." Jim tayi tana nazari tace"abunda nake so kwangila wani tuggu nakeson ahada mashi,wanda bama mutanen cikin gidanna kadai ba har jama,ar gari kowa yatsanesa incusa tsanarsa cikin ran mahaifinsa ta yadda zai mashi mummunan kalamin da koxuciyar kare garai bazai sake tako kafarsa hanyar unguwar nan ba,ta haka zan saka mamman ya maye gurbinsa mumallake abunda nake hari shekara talatin tun ranar da aka haifeshi shegen yaro yazo da arxikin da shikanshi uban baiyyi tunanin zai samesa ba.shegiyar uwarsa daman ni bana kallonta wata matsalata da zaran na kora dan nata itakuma nasan ta inda zan biyo mata." "Kinata surutu baki gaya mun yadda plan din zai kasan ce ba" Murmushi tayi tace mekake ci na baka na xuba,zakaji amman saina gama tsara komi kasan zakiyyata suke soyayya,da har nafara daukar mataki akai sai yanzu kuma wani tunani yazo mun,don haka dole da zakiyya zanyi anfani,katashi katai kafin yarana sudawo su sameka don kosu ban bari sunsan ina bin mazan waje ba" "Mariya kice bani kadai nake nitso cikin fadamarki ba,har wasu kike bi awaje" Tsaki taja tace"to meye kaidinma ai bani kadai kake ma aiki ba,ansha gaya mun kana xuwa hotal kana shanawarka da yan shilan yara,to donme zan zauna dakai kaidaya kamar rai,mijina ma ban zauna dashi shikadai ba saikai,nimubar wannan maganar katashi katai zan sake tunani kafin na nemeka,nasan ma kafin na nemonka kai kakawo kanka maye kawai,kai mace bata taba isarka." Dariya yayi yace"inma zaki karaman wlh so nake don waccen dusar yadda kikasan hanyar da babu titi haka take," "Nibanson wulakanci,matarka mace mai kirki da tsafta da kiyaye wa amman karinga cin amanarta wlh sai Allah yasaka mata,amman dai shikenan tashi kabi ta baya kafece kafin aganka" "Shikenan saina sake zuwa" Daidainan audio guda ya kare. Shiru sukai kowa yana saka wa yana warwarwwa cikin ransa,dady yajima yakasa magana don wallahi daman zargin dayake kenan,amman bai taba kawo cewar suna neman juna ba kawai dai yasan cewar umma da Alh kwangila akwai saka hannunsa cikin wannana lamarin. Malik daskarewa yai yaka sa motsawa,maganganun sunyi masifar daure mashi kai,har rashin imanin umma yakai haka. Wata xuciyar tace bakaji komi na sai ka gama saurarar sauran. Ajiyar xuciya yaja yana kallon agogonsa yadago daker yace"dady zanje na duba jikin Abdoul wata kila ansallamesa yanzu,zuwa gobe insha Allah sai mu idasa sauraren sauran,zanbar computer anan saboda tsaro." Dady bai iya magana ba saidaga kai dayai,malik yafice daga falon yanajin kafafunsa suna mashi nauyi. *kuyi hkr da wannan insha Allah zan baku na dare* Don't share it plss Bcos its for sale 300 naira ne gamai bukata.ya tuntubi wannan no din. 09034722970 [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........42 "Naam" Can kasan makoshi ta ansa kiran da yayi mata Shiru suka sakeyi sai musayar numfashi dasuke,dan maxewa tayi muryarta kamar daga frig aka fiddota tace"wake magana,nai tunanin yaya malik ne sai naji ba muryarsa bane,who is on d line" Idonsa dake lumshe ya budesu akan malik dake kallon news,sannan yabude baki daker yace"malik kai take nema" Gabanta yafadi badai ajiye wayar zai ba yabarta da wannan kullellen mikin dake cin ranta,malik yace "ba nema na take ba kaidain dai take nema kasake saurare kaji" Taji abunda malik din yafada ras tayi murmushi kasa kasa tasake kwanciya tace"oh sorry yaya Abdoul ne ashe ina wuni,ya karfin jiki Allah yasa kaffarane" Ajiyar xuciya yasauke yana cewa"nagode,yajikin

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});