Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 87

Chapter 87

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,289 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba. 😂😉 Muhadu next page da sorry typing error [10/13, 5:31 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSEER* *(ALFAH)* WRITTEN BY MRS BB MOM MUHSEEN FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970 🅿️...........61 Kasancewar masallacin juma,a aka daura ba kofar gida ba bakowane yasan an daura ba,saida aka fara shigowa abokan baba sunayi ma mama Allah yasa alkairi,saitaji kwalla ta cika idonta haka take daurewa tana ansawa,su yesmin suna gidan Anty jamila labarin ya samesu saitaji duk dokinta na kasancewa da muhseen yakau,kewar mamanta da Addarta yasakata ta rushe da kuka,ga kawayensu nan wasu na lallashi wasu na mata dariya. Fiyah na fitowa daga wanka maiyi masu make up tazo ta fara gyareta tana mulketa da wasu arnayen turaruka da tunda akafara yimasu gyara dasu ake mulke masu jikinsu,shiyasa dasun gifta ka zakaji sun barka da tarin kamshin.komi suka rike saiya kamu da wannan kamshi,ana cikin kwallaiyar ne dayake tace kartayi mata heavy make up simple takeso,wata kawar yesmin ce ta shigo tace"Adda safiyyah ga yesmin can tana kuka dagajin an daura aure" Wani irin duka taji ga kirjinta,har saida taji sautin cikin kunnuwanta dan danan jikinta yadauki rawa dakarkarwa daker tace mata"don Allah salaha kilallasheta kafin inxo idan akwai masuyi mata dariya sudaina hakan zai tun xurata" Tace "to bari naje" Tana fita tacigaba dajin wanan dukan a kirjinta,tsawon lokaci tana haka kafin wasu zafafan hawaye su sulalo mata,cigaba da xuba sukai babu kakkautawa mai kwalliyar ta dakata tana kallonta cikin murmushi. "Kema kukan kike,to inkekinayi ya za,ai ita tadaina.kuyi hkr kowace mace da haka ta saba agidan mijinta,kuma kugodema Allah wasu nacan neman mazan dazasu auresu suke sun rasa,amman kuganku ku da kananun shekarunku kunyi aurenku kun huta,kuyi hkr daman dole wataran duk shakuwarku da yan gidanku dole zaka barsu,ni kinga burgeni kuke wlh shekarata goma da gama secondary har yau Allah bai ban mijin ba,ba kuma don banda masu sona ba aa lokacine Allah bai kawo ba." Goge kwallarta fiyah tai tana shanken majina tayi murmushi na karfin hali tace"na gode Anty,insha Allah zandaina kuka itama zan lallasheta,kuma insha Allah zaki samu miji wanda baki taba tsammani ba" Murmushi tai tana jin dadin Adduarta cigaba da kwalliyar sukai tana janta da fira,don ganin har lokacin tana cikin damuwa. Bakomi take tunawa ba illa Abdoul,yanzu shekanan ta zama ta wani,duk wahalar dasuka sha akan juna daman bazasu rayu tare ba,wannan abunne idan ta tuna yake sata jin kirjinta yana zafi fiye dakima. Haka aka gama ta tayata shiryawa cikin wasu dankareren less na cikin lefenta da aka kawo akwati shabiyu,harda gwal aciki da xinarai abunda yafi dakar ma masu kallon lefen hankali irin jewelrys din da aka saka tsalatsala da daukar ido,hakika anma fiyah lefe na nuna ma sa,a haka yesmin ma akwatunanta goma ras,masu shegen kyau. Sunsha saka albarka wajen dangi da abokan arxiki,qawayen fiyah uku kacal ta gaya mawa daga feea sai yan class dinsu su biyu zuhra da ziyada. Zanso kuga yadda fiyah ta dauki kyau,hotuna mai kwalliyar tayi mata da wayar fiyah tana janta wai ta nuna ma angonta idan ta isa kasar,don karfe takwas na dare jirginsu zai tashi.yan rakiyarta duk mutun ukune daga yakumbo hajara yayar baba sai inna balaraba da Anty jamila saifa hasana diyar inna balaraba.yesmin ana gama sallar la,asar za,a mikata. Shiyasa tunda suka kulle kansu daki ita da fiyah basu bar juna ba,kuka kurin suke ita fiyah abun ya hade mata goma da ashrin,ga rashin masoyi ga rashi iyaye ga na yar uwarta rabin jikinta,tunda suka xo duniya basayin nisa da juna irin haka saigashi yau aure zai rabasu don dole. Motace akazo da ita ta abokin yaya jalal zai dauki amaren akaisu gida aimasu fada za,akai yesmin nata gidan. Ai jisukai kamar ance za,akaisu makabarta kuka kamar zasu mutu,Inna balaraba ce da Anty jamila suka jasu suka sasu motar sanan suka tai,gidan acike da mutane mama kokadan batai tunanin yan unguwar zasu shigo mata ba,bacin momin su feea. Saigashi har mutanen da batai tunani ba sunxo kuma ta samu abun arxiki sosai,dakin baba aka ajesu fura mai kindurmo aka dama masu harda xuma akasaka,don cikinsu babu wace tasaka ko ruwa aciki ta tun safiyar yau. Baban da kanshi ya tsaresu saida sukasha furar sosai,sanan shida baffa ubaidullah kanensa da yayansa baffa kalil suka sasu gaba da nasiha sosai,har jikinsu yayi sanyi suka daina kukan. Sannan yan uwan mama ma suka zo suka dora nasu,yinayi bari nabari ta rabaki da kowa tsafta,biyayya,ladabi,girmamawa da girmama iyauensa yan uwansa da duk wanda ya kawo.sune ke saka kiga miji yana bin matarsa,yana mata duk abunda takeso shike sawa har ace masa mijintace,idan kin tsare wadannan kin zama sarauniya kuma gimbiya agidanki,babu boka babu malam zaki kame mijinki kihanashi kallon wasu sai ke,idan har kin dauki duk abunda ake gaya maku ina mai tabbatar maku zakusha mamaki." Cewar goggo ladidi diyar wansu mama. "Hakuri shine jigon zaman aure,kiji kikiji kigani kikigani,ki kawar da idonki akan komi kiringa wa mijinki uziri komi kike idan har yashigo gida ajiye ki kula dashi,wannan na daya daga cikin abunda yasa maza da dama basa son dawowa gidansu kan lokaci.inhar kikai hkr dashi ananma xakici riba ba yar karama ba,sannan ki rike mashi amana kirike sirrinki kedashi kunyi karatun addini kunsan hukuncin mai tona sirrin ta tsakaninta da mijinta,don haka kurike sirrinsa kowane irine,sannan ku kula da dukiyarsu kuzama masu taka tsantsan da duk abun daya mallaka,karki zama mai saka mashi ido kan lamarranshi." Haka sukaita basu shawarwari da nasihu da kalamai kala kala da zasu natsu su zauna gidajensu. Har abokan muhseen suka iso da motoci dan daukar amarya,mota ashirin ce cif kowa dakeson xuwa saida ya samu waje. Harda fiya aka tafi raka yesmin kafin lokacin tashin nasu jirgin yayi. Motarsu guda da yesmin suna makale da juna,sai inna balaraba jusa dasu sai Anty agaba,dayake uncle yahya ne kejan motar. Gaskiya gidan yesmin yayi babu karya,don gudane na kere sa,a giane dan gaske wanda tawon rayuwarta bata taba kawo cewar zatai aure aciki ba,tana ganinsu unguwanni masu hali amman bata taba saka hakan aranta cewar wataran zata mallakeshi ba. Kowa idan yashigo saiya yi magana ana ta saka mata albarka,da fatan dorewa acikinsa har iyakar rayuwarsu,bed room dinta uku amman guda biyu baba da mama sukai kokarin cika mata da kaya,sai falukanta biyu suma acike da kaya na zamani masu kyau. Kawayenta harda hotuna daya daga cikin dakunan aka sauketa ita da Addarta,can suka shige kowa ya buga tagumin sabuwar rayuwar dasuka shigo,wanda tazo masu abazata don kokusa fiya bata kawo aurenta nan da shekara mai xuwa ba na balle wata uku.sunsha addua ga Mutane kafin suka fara ragewa ahankali ahankali har ya rage daga su sai inna balaraba da hasana saint feea da ziyada sai Antyn. Hira akeyi yadda abubuwan suka kasance inna na sake jawo hankulansu tana kwantar masu dashi,har yesmin ta dan fara dayayewa. Amman fiyah sauraren bugun kirjinta kurin take,zata so tayi ido biyu da wannan mai karfin halin daya aureta,taya zata fara rayuwa da wani namiji bacin ba wanda taje tsara rayuwarta dashi bane........sai hawaye tayi kukanta mai isarta ta hkr. Anayin magruba kawayen duk suka watse sai kawayen yesmin su biyu da zasu jirayi anguna kafin sutai,don baza,a kwana ba gaskiya. Babane ya kira Anty yace tayi maza tazo ta hada kayan

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});