Chapter 25
Chapter 25
karshe sai murna tae tace kafin ta dawo kowa ya ajiye mata gift dinta.Tare suka tai saida suka ajiye yasmin sannan suka isa makaranta. Suna kan hanya text din malik yashigo wayarta dubawa tayi da murmushi akan fuskarta . _INA FATAN MA,ABOCIYAR MURMUSHI TA TASHI LFY,I KNOW U ON UR WAY TO SCHOOL,ALLAH YA BADA SA,A IDAN KIN DAWO I WANT SEE._ Kallonta feea tayi tace"duk da ban sani ba kuma baki gaya man ba da alama dai fiyah tayi sabon kamu,kinsan kuwa maganar mu tana da nasaba da haka zanso nima kimun wannan hanyar." Kallon waje fiyah take tana sauraren kalamanta tana komarin dorasu bisa ma,auni amman iyakar tunaninta tagaza hasaso komi. *aradu nagaji sorry mu hafu gobe* Mrs bb ce Mom muhseen. [9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* *INA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA WANNAN LABARIN DA KUKA NISHAD'ANTU DASHI WATAU _ABIN CIKIN RUHINA_ TO KU MATSO KUJI GA WANI SABON SALON KONACE SABUWAR TAFIYA,KONACE TAKU NA BIYU ACIKIN WANNAN LABARIN WATAU CIGABAN ABIN CIKIN RUHINA MAI TAKEN _SANYIN IDANIYA_ SABODA IRIN KAUNAR DANAKE MAKU YASA BAZANSO WANNAN DAMAR TA WUCE KU BA,DON KUWA WANNAN KARON SAI KUNCE KHAIRAT DA AREEF BASU IYA KOMAI BA.DAURE KI FIDDA NAIRARKI DARI 200 KACAL DOMIN MALLAKAR NAKI,KUNSANI MOM MUHSEEN BATA LITTAFIN BANZA.INA KASA KUNNE DON SAURARENKU.* 🅿️..........19 Wani lungu ta samu ta shige tana haki,kirjinta d'agawa kurin yake saboda tention.silalewa tayi k'asa ta fashe da kuka kalamansa suna sake dawo mata ras ga kunne,babu abunda yayi bala,in kuntata mata zuciya irin yadda yakirara karuwa tana biyo maza har gida..........cikin kuka tace"Allah kana gani niba haka nake ba,wlh niba yar iska bace kaga zuciyata kaga abunda ke cikinta,kasan niyyata ban fara wannan aikin don kusanta kaina da malik balle shi,hasalima banda abunda nake k'yama kamarsa.Allah kasani bana kaunarsa wannan kalamin ya sake jefaman k'insa,natsani kalamr karuwa balle a alak'anta ni da ita,kaida Allah Nasser wlh sai Allah yasaka man.bazan yafe maka ba.......kuka take iyakar karfinta tana kallon yadda guyawunta duk suka guggurje,banda zafi da rad'ad'i babu abunda suke mata,wani hamami da ya nusar mata hanci shine ya tuna mata da giyar daya antaya mata ga fuska,runtse ido tayi tana jin zafin hakan har cikin ranta. Hawaye suka sake b'alle mata "d'an iska matsiyaci wlh Allah ya isana." Tashi tayi tana d'an gasa k'afar ta fito titi,wani shop ta gani ta gangara taje ta siyo ruwa ta wanke fuskarta tas,amman har lokacin tanajin warin giyar yana nusarta,har wani tashin zuciya takeji. Daker da taimakon mai wajen ta samu abun hawa,ganin yadda take bukatar taimako shiyasa yaga yadace ya taimaketa. Tana sauka tayi kokarin daidaita kanta amman ta kasa,ciwo raunikan suke mata duk ta tattare rigarta sama.d'alha ke mata magana bata tsaya saurarensa ba ta shiga gidan tana kuka..........gabaki daya suka yo kanta da tambayar lafiya,yesmin na ganin halin da take ciki ta rushe da kuka tana cewa. "Mama Adda taji ciwo zokigani wlh kafafunta duk sun gurje." Mama dake cikin kitchen tana shirya ma baba abincin dare ta fito da sauri jalal dake saka takalman kwallo yace"garin yaya haka fiyah." Kukan take tana jin inama ta sanar dashi abunda yafaru,amman tasan itace aciki inta sake wani yaji wannan labarin. "Yaya motar muce ta kife wani mai mashinne ya shigar mana gaba,yawancin sauran y'an cikin motar suna asibiti ganin ni ban jigata sosai ba yasa nace ni akawoni gida." Salati duk suke suna jajanta karyar data lafka masu,jalal yace "sannau aida anje dake anyi maki checkup ko kinji rauni k'ashinki." Girgiza kai tayi tace"Aa yaya banji ba kawai dai wannan ne." Sannu kawai suke jara mata tana ansawa daker. D'aki ta wuce ta cire kaya ta daura towel,ruwan zafi yesmin ta jona mata ga heater cikin d'akin tana ta mata sanni cikin tausayawa. Sai lokacin tace"yesmin ina baban yake,ban ganshi ba." Tace"Addana baba yafita kasancewar basuyi masa komi ba,yana gama cin abincin rana yatai wajen aikinsa." Girgiza kai fiyah tayi tace"baba bai ko hutawa cikin iyalinsa ya kwana biyu bamu hadu ba,amman daga fitowa ya fice wajen aiki,mutanen da ko cigiyarsa ba suzo ba kwana biyu mts!me ma akedasu marasa mutunci." Ruwan yana zafi ta juye mata ta had'a mata tace"Addana gashican kiyi wankan sai na tayaki shafa magani." Cikin kulawa tace"sannu yesmin ngd kinjiko." Murmushi tayi tana fita daga d'akin. Haka Allah yayisu suduka kowa yana son d'an uwansa,idan abu ya samu guda kamar shi ya sama,kulawa suke da junansu sosai kuma wannan duk tarbiyyar mama ne. 💞💞💞💞💞💞💞💞 Alfah yana ganin ta b'ace masa ya dunk'ule hannu ya kaiwa bango naushi nan take hannunsa ya fashe jini ta samu hanyar fita,amman saboda zafin da zuciyarsa take masa yasa ko ajikinsa.......malik ya fito afirgice yana kallonsa,baima lura da hannunsa dake zubar da jini,cikin b'acin ran da bai tab'a ganin malik aciki ba yace masa. "Abdoul wlh idan kasake wani abu yasamu yar mutane zaka sha mamakina,don wlh zan cire sanayya na yimaka rashin mutuncin da baka tab'a tunani........kai baka bin komi asannu,komi saika zafafashi idan ma karuwarce meya shafeka ne wajenka take zuwa.kai da kake zuwa club d'inka wani ya rik'eka kokuwa wani ya kiraka da d'an iska.......yarinya tana iyakar kokarinta duk don kai duk don kadawo cikin hayyacinka kagane daidai da ba daidai ba,amman naga alamar so kake ka nakasta yarinyar mutane." Kamar Abdoul yasamu tv haka yake kallon malik,cike da tsananin mamaki da rud'ani. Tunda Allah ya had'asu tsawon shekara tara kenan irin wannan tsawar da hargagin malik bai tab'a yiwa Alfah ba........kauda kai malik yayi ganin irin kallon da yake masa,cike da sassauta murya yace"inhar baka son musamu matsala karage wannan zafin ran,karage yiwa wannan yarinyar azaba kar tsotsai yasa ka nakasta ta." Har lokacin Alfah bai samu damar tankawa ba,binsa yake da kallo kurin kamar wani status. Har malik ya juya zai shige cikin gidan idonsa ya kai ga jinin da yake zuba ga hannunsa.......cikin tsananin tsoro da firgice ya dawo garesa yana niyyar rik'o hannunsa cikin wani irin sauri Abdoul ya kauce ya shige yabarsa nan,binsa yayi cike da tsoro yana kwala mashi kira amman bai juyo ba. Shigewa yayi bedroom dinsa ya banko k'ofa yama rasa mezaiyyi sai ya silale kasa yadafe kai,yanzu zafin ya zame masa uku gana ciwonsa gana maganganun yarinyar nan,ga kuma wad'anda malik ya gama jera masa duk akan wannan kidahumar yarinyar..........tashi yayi yajawo first aid box yazo ya fara bawa kanshi treatment,tunda bayan tsawon lokaci bai tabajin ciwo ya yi yunk'urin tai makon kansa ba sai yau,hasalima kullum kokarin neman abunda zai zubar masa da jini yake,amman yau saiya tsinci kansa da bawa kansa kulawa........amman har lokacin wannan xafin na cikin xuciyarsa bai barsa ba,yana gamawa ya nad'e da bandage ya canza kayansa dasuka b'aci da jinin,ya kalli agogo nan da minty arba,in jirginsa zai fashi yana gama shirywa ya dauko bakin glass da fesing cap ya saka,ya rufe fuskarsa wadda duk da rashin murmushin da baisa ba,hakan bai hana ruwan kyansa fitowa ba......muryar malik yaji cikin rauni da danasanin kalaman daya gaya masa yace. "Kayiwa girman Allah abdoul ka bud'e kofarnan wlh dressing kawai zan maka nasan maganganuna sun b'ata maka rai,kayi hkr ingama yimaka dressing din saimuyi magana............baigama rufe baki ba ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101