Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,301 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jiya zuwa yau sukace zasu aiwatar.inajin tsoron abunda umma dasu zuwairat da yaya mamman zasu aikata,yaya malik duk yadda kake zaton rashin imanin umma ya wuce nan,inhar akan kudine zasu iya yin komi wlh.yanzun haka kusan shekara guda kenan umma tayi yadda tayi Abbi baya kula Ammi,ko inda part dinta yake baya zuwa,suna cikin wani hali itada ni,ima.hakan yasa naje na sanar da dady halkn da ake ciki mafarin kenan yake hidima dasu,duk abu da suke so yake yi masu." Hankalin malik yayi masifar tashi,dajin abunda zakiyyar take fada saurin rarumo wayarsa yayi yana no layin Daddy. "Assalamu alaikum,daddy kana gida inason ganinka emergancy ne" "Malik,akwai matsala yanzun haka ina nan asibiti Abbinku ne baida lafiya ankawo mashi harine,Allah yakawo mashi mai taimakonsa mahaifin safiyya shine ya taimakesa,ta dalilin haka mahaifin safiyyar suka halbesa ga kafa shima ayanzu gashi nan asibitin." Cikin tashin hankali yace"baban safiyya dadyy,innalillahi wa inna ilaihir ra,ju un" Silalewa malik yayi kasa yana jin xuciyarsa kamar zata fito waje "daddy wane asibitinne,fatan suna lafiya babu dai wanda yarasa ransa cikinsu ko." "Anci sa,a Allah baibasu nasara ba Amman baban safiyya yafi Abbinku jinjiki gaskiya" Kashe wayar yayi duk ya gigice. Haka zakiyya kukanta yadawo sabo fil,duk abunda sukeyi Abdoul yana bakin kofa bai bar wajen ba yana jinsu,wata xuface take wanke mashi fuska da jikinsa,mahaifinsa da mahaifin safiyyah. Soyake kar abun hadamai soyake ya yakice tashin hankalin dayake ciki,amman ina abun ya ci tura abun ya gagaresa. Idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,mezaiyyi meya kamata yayi? Aa babu abunda zan mashi ko addua bazan mashi ba,bai dace da samun addua ta ba koma mai zai fatu dashi yaje yayita faruwa bai damai ba. Fitowarsu kenan suka hanhi shigewarsa cikin part din malik, Ayadda ya fahimci tafoyarsa tabbas yaji komi bazai iya gane wane irin hali yake ciki ba. Shida zakiyya suka shiga mota suka bar gida xuwa asibitin. Badai editing kuyi hkr da typing error. Don't share it pls i beg. Bcos its for sale inkina bukata ki tuntubi wannan number. 09034722970. [9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞 *ABDOUL-NASSER* *(ALFAH)* WRITING BY. MRS BB MOM MUHSEEN. WATTPAD NAME HUMAIRA7531. *DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS* 🅿️.........37 "Mama kune,banji tsayiwarku ba" Kallonta mamar keyi cike da tuhuma yayinda fiyah cikinta ya duru ruwa,tashiga ukunta inhar mama taji abunda take gaya ma ni,imah. "Mike gaya mata har yasata kuka safiyya?ke rayuwarki yan shige shige ya maki yawa,da kinga mutun na cikin damuwa saiki shishshige mashi,ina ruwanki da ita dake nake kinmun xuru da ido,mekikai mata" Kamar zata fashe da kuka tace"nikuwa mama mezan mata,daga na mata yamaijiki mungode da abinci,shine ta fashe da kuka tana cewa da badan baba ba da shima Abbin nasu sun rasashi kamar yadda suka raya yayansu,shinefa nake lallashinta" Harararta mamar tai tana nuna hanya "wuce muje,banson wannan shishshigin na gaya maki,ga dalha can zai kwana dashi muje kidauki takadda kicigaba da karatu tunda kinsan gobe iwar haka kin dawo daga jarabawar" Tafiya sukai gida don basai ma sun kawo masu abinci ba wanda ni,ima ta kawo ya wadacesu. 💕💕💕💕💕💕💕💕💕 Suna dawowa daga asibitin falon sukai ma tsinke,wanda suna shiga sukai kicibis da Abdoul xube kasa ya sankare.......aguje suka isa gareshi suna jijjigashi,Amman baisan sunayi ba. Tuni zakiyya ta rushe da kuka jikin malik har rawa yake ya lalubo wayarsa yashiga kiran dr............"babu lokacin gaisuwa kazo gida babu lafiya Abdoul ya suma ban san ma tun lokacin da yake ahaka ba." Tusashi gaba sukai harda malik din suna kuka,ita harda kara shine dai yake kwallah.tausayin alfah ya kamashi tabbas bayan tafiyarsu yashiga tention ba karami ba,dama ba idasa warkewa yayi ba daga wancen kwanciyar da yayi. Cikin kankanen lokaci saiga dr yazo yashiga dubashi,yafi awa akansa amman babu numfashin Alfah babu labarinsa. Cire abun awon yayi yana dafe goshi yace ma malik. "Malik saimun dangana da asibiti,abun babbane amman insha Allah bazata gagaraba" Daukoshi sukai sukasa shi mota zakiyya kamar zata haukace don kuka. Malik yace ta zauna gida fitarta hadarine ga rayuwarta.dole fa dawo ta dasa sabon babin kukan,saida dr yayo gayyar wasu likitocin suka dafkaka kanshi suna dubashi,kafin Allah yasa su iya gane matsalar.numfashinsa ya fara daidaita amman ciwon dake cikin cikinsa shine yajawo hakan,hanyar da zasuyi mashi maganin ciwo suke nema,koya farka zai iya sake sumar don ciwon ne aka fama. Fitowa dr yayi yana share gumi hankalinsa atashe,meyaja har ciwon yayi girma haka zuwansu na farko yaga ciwon karamine,wanda har yace ma malik inhar yabar shan giyar zai warke tas,daker idan nan gaba Alfah ba ai mashi aiki ba don ciwon ya kusan zama wost koma yace yakai. "Dr lafiya ya jikin nashi,Allah yasa babu wata matsala." Malik ne hake fada cikin rudu da rikicewa. Dafa kadarsa yayi yana riko hannunsa yace "cool down malik,insha Allah babu abunda zai faru kawai dai tambaya zan maka,daman ya jima da wannan ciwon ne kuma wane irin magani yake sha,don da alamar yana shan magani sanan yasha abunda ya tada ciwon.don raunin baya son cool water or heat,cikin biyu akwai daya." Kan malik ya kulle wane ciwo yake magana akai,a iyakar saninsa alfah bashida wanj ciwo,to ya kai dr yake mashi maganr ciwo.? "Kaga dr,nifa bansan Alfah da wani ciwo ba bai gaya mun ba,bacin ciwon xuciyarsa basan komai ba,wane irin ciwone yasamai don girman Allah dr karka bari narasa shi,bazan iya wata rayuwa mai dadi babu shi ba,dr kuyi iyakar kokarinku don girman Allah wlh ko nawane za,a biya" Girgiza kai yayi yace mashi"malik kwantar da hankalinka Abdoul zaitashi da iznin Allah,amman dole sai munsan magnin dayake sha akan ciwon,ta iya yuwuwa kaine baigaya ma wa ba,dole sai munsan sa sannan musan abunyi,kaje gida dakinsa kayi bincike sosai ka natsu kaduba bazaka rasa maganin dayake sha ba,saika kawo mana shi.kuma kabar batun kudi Malik ni xan dauki nauyin hidimar rashin lafiyarsa,bazan mance da alkairin sa gareni ba koza,a shekara dubu don haka karka damu maza kaje kadawo." _anan ina son jawo hankalinmu,yan uwa mu zama masu hallaci shi Alkairi abune mai kyau,duk wanda ya maka shi muddin kai dan halak ne,kuma mai rike amana dole wannan abun zai tsaya ranka,har kaima kaiyi burin mayar da wani alkairin bisa ga wanda akai maka,muguji mayar da sharri kan Alkairi wani zaimaka abun alheri,kaikuma zuciyarka babu Allah Aciki saika kudiri mayar mashi da sharri,wannan ba daidai bane akwai abunda za,ai maka duk kudinka da wadatarka zakaji dadi,mu zama masu amana da rike alkawari,duk wanda ya maka alkairi kokarta kaima ka saka mashi da makamancinsa,Allah yasa mufi karfin xukatanmu Allah ya tsare xuciyoyimu da aikata badaidai ba_ Haka malik ya juya ya nufi gida babu natsuwa kokadan,shiyasa ma yahau taxi don bazai iya driving ba. Dakin alfah yayi ma tsinke duk wata drower dake dakin yaringa haukacesu yana dube dube,duk kankantar takarda saiya dubata duk ya gigice gani yake kafin yaje za,ace mashi Alfahn ya mutu.xufa yake hadawa yana hwaye,Allah yasani yana son abdoul bayason rasashi abdoul yasha wuyar rayuwa bai cancanci mutuwa yanxu ba. Yafi minty talatin yana dubawa bai samu komi ba,ya tashi ya bude wadrop dinsa nan ma yayi mashi watsa watsa da kaya,daker da jibin goshi yasamu wasu kwayoyi cikin wata leda.daukosu yayi yana kallo bazai iya tantance ko namiye ba,don haka aljihu yasasu ya fice kamar walkiya. Zakiyya ma

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});