Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

Abdoul Nasser Alfa Book 1 Complete Hausa Novel 1,279 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tayi don cin Abinci yunwa takeji. Sallamar muhseen ce tasaka ta juya shikadai ne daga bayansa kuma saiga uncle ya shigo shima,hira suke ta kwallo sai muhawara suke shi uncle dan arsenal ne shikuma muhseen dan Manchester united ne,sai gardama suke. Anty ta fito tana cewa"aifa kun fara halinku ko,wai meyasa baku gama duk gardame gardamen ku acan waje sai dole kunshigo mun gida da hayaniya." Fiyah dai na kan dining tana tsakurar tuwon shinkafa da miyar agushi taji zallar naman kaza. Uncle bai kula Antyn ba sai muhseen ne yake bata ansa suna ta fadansu itada shi dasuka zaba, "Safiyya babu magana" Yake take tace"uncle naji aikuna ta magana ne sannuku." Muhseen najin ankira sunan ta yai saurin juyawa yana washe baki,cike da jin dadin ganinta barin Antyn yayi yana nufar wajen da fiyah take. "Aa ah ashe kina nan nazo da yamma bakinan" Ta na Kai cup din ruwa bakin ta tace cikin sanyin murya"ina wuni yaya muhseen" Murmushi yayi yana shafa kanshi yace"lafiya lau ya kike,nayi kewarki yau zuwana biyu bana samun ki" Idan dayasan yadda takeji yanzu dayake isarta da magana da ya kyaleta,amman bata son yaga tayi mashi wulakanci dole ta ke dannar xuciyarta take bashi ansa. Uncle yace ma Antyn"meyasamu safiyya ne?" Dariya Anty tayi har muhseen yana juyowa yace"kinga kina hana mu sakewa wallahi" Harararsa tayi tace"nan gida nane kabari sai kayi naka idan naje saika mun iko kajiko" Ta share sa tana bawa uncle ansa"waifa daga tayo na biyar isalamiyya shine take fushi,da kuka ma ta shigo gidan nan don ta sana yo na biyu ko na ukku anbata na biyar take ta fishu" Murmushi yayi yajiya ga fiyar daketa cin magani yace"safiyya haka abun hake ba kullum kake nasara ba,dole daman wata ran kaga juyin mulki badan hakan nanufin kasawa ko rashin maida hankali ba,aa hakan na nufin rabon wanine ba naki ba kiyi hkr next exams saiki dage ki dawo da position dinki" Murmushin dole tayi tace"nagode uncle insha Allah zan gyara" Muhseen yace"kice dai yar gidana akwai kokari ban result din in gani tawan" Batare dataji komi tace"yana gida na barsa wajen mama" Duk yadda yaso hirar tayi tsayi abun ya gagara don taki bashi hadin kai,tashi tayi ta yi masu saida safe ta wuce dakinta. Bata da natsuwar yin karatu amman ya ta iya dole zatayi saboda baifi saura kwana biyar sufara exams ba,haka ta runtse ido tanayi ba laifi kuma yana shiga don fiyah inhar tasa kanta abu ba kamar in kan karatu ne tofa ba dagaske yitake har saitaji ta gamsu da abunda ta karan ta. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Tunda ya kaita asibitin ya dawo resuption ya zauna ya dafe kanshi dake wata irin sarawa,wani irin juyawa kanshi hakeyi dashi zuciyarsa kaikomu kurin take,duk yabi ya gigice yarasa natsuwarsa. Malik ne yakira sa ya kasa daukar wayar saida yayi mashi kira uku sannan ya iya dauka. "Kana ina haka" Atakaice yace dashi"tarauni specialist hospital" Cikin tsoro malik yace"mekake yi awajen ne haka Alfah baka lafiya ne koko mekaje" "Kazo kasaman wajen" Yana gama fadar haka ya kashe wayar ya dafe kanshi dake cigaba da ciwo,baisan ma kalar tunanin dazai ba. Yanan zaune ya iso Allah yasa baisha wuyar ganin sa ba. "Lafiya Abdoul,bakada lafiya ne meke damunka." Idonsa jawur yace"zakiyya na kawo" Zaro idonsa malik yayi yana kallonsa cike da tsananin mamaki "zakiyya!!!,zakiyya fa kace kai ina ka gamu da zakiyyar kuma meyasameta" Cikin wani irin yanayi yayi mashi bayanin abunda yafaru atakaice............likitan dake dubata ne ya karo wajen yace"Alhamdulillah ansamu nasarar samunta,kozamuje office ne nayi maku bayani" Malik ake kallon sa yace "oky ba damuwa muje" Kamar bazai tashi ba haka ya tashi suka wuce office din likitan,rubutu yayi kafin yace"Am tayi sa,a sosai don an shak'a mata koken,Allah ne yasa abun yazo da sauki,don haka zata jima bata tashi ba zata iya kai gobe ma har yamma,mun mata allurai mun saka mata drip,zakuje wajen biya kubiya ga bill din ku" Ansa malik yayi yai mashi godiya suka fito. "Suwaye zasu yi mata haka?metayi masu ne" Abdoul ya daga kafada yace"karka tambayeni ban sani ba wata kila wannan yarinyar zata iya sani" Kallonsa Malik yayi yace"yarinya kuma,wai baka san sunan ta bane Abdoul?" Tsaki yaja yana zama saman wani benci malik ya isa wajen biyan kudin ya biya yadawo ya zauna kusa dashi yace"yanzu yazamuyi da ita" Kauda kai yayi Allah kadai yasan yadda xuciyarsa take ciwo,ba kuma dan karamin ciwo ba da wuya idan ba sai yasha magani ba. "Munyi mai wuyar don haka muwuce gida randa ta tashi saita kama gabanta ko" Kallonsa yake cike da nazarinsa "ba zai yuwu mubarta ita daya ba Abdoul,don haka ina ga zanje in samu likitan ya tura nurse guda ta zauna da ita,kafin zuwa goben" "Can matsalarka" Inji Alfah. Tashi Malik yayi ya nufi wajen likitan,yayi sa,a kuwa aka sanya nurse guda dazata kula da ita,sannan yadawo suka tafi. Tafiyar so silent babu Mai magana kowa da abunda yake sakawa cikin ransa,kallon Alfah malik yayi yace"fiyah fa fushi yake dakai,don ayadda ka gaya mun tabbas ka bata mata rai,kuma kowaye dole zaiji haushi ka kirata ka bata hkr" Jajayen idanunsa ya watsa ma malik yace cikin muryar sa da saika rantse dukan tsiya akai mashi"ta shekara dubu tanayi" Jinjina kai malik yayi yana murmushi yasan cikin bacin rai yake,amman tabbas yasan wannan ban hkr sai Alfah yayi shi,don daga jiya zuwa yau ya fahimci wasu abubuwa tsakaninsu. Koda sukaje gida shigewa yai yakulle kofarsa ya fada kan gado dafe da xuciyarsa,murgina kurin yake yana nishi shikadai yasan azabar dayakeji aciki,yau ciwonsa na shekara shidda ya dawo sabo,wani radadi yakeji cikin xuciyarsa.fadowa kasa yayi timm har malik dake falo saida yajiyo karar faduwarsa,gabansa ya fadi ya rugo ya banko kofar dayake ba sosai ya rufe ba saigata tabude..........asume ya yadda shi duk inda hankalin malik yake ya tashi ainun,ya rude sosai rabinda yaga Alfah cikin wannan halin bazai iya tuna wa ba..........yana kerma yana karkarwa ya dauko phone dinsa yashiga kiran dr Alfah din. Bakinsa yana rawa yake gaya mashi halin da ake ciki,yace gashinan zuwa insha Allah. Haka malik yaringa kwaraya ma Alfah ruwa Amman baifar fado ba saoda likitan yazo yashiga nemo numfashinsa yasha wuya ba karama ba, kafin Allah yasa numfashin dawowa,amman dole saidai karamin oxygen aka saka mashi yadda zai taimaka mashi wajen numfashin,dr yace"xuciyarsa ce ta halba dakarfi,wanda hakan yajawo sumar tashi da alama dai yana cikin damuwa da tsananin tashin hankali,meya faru ne?" Dafe kai malik yayi yana sauke ajiyar xuciya yace"yaga abunda ya tuna mashi rayuwar sa ta baya,bacin ransa na shekaru da yawa shine yadawo mashi sabo,ya kasa control din kansa har hakan tafaru." "Allah ya kyauta gaba,ka kula dashi gobe zan dawo na sake dubashi yanxu dai kabarshi yayita baccin har sanda zai tashi,na xuba allurai acikin ruwan drip din zaitaima ka mashi wajen samun arfin xuciyar" Rakashi yayi yadawo ya tusa Alfah gaba yana kallo kamar yasamu tv ,tausayinsa ne ya kamashi sosai dole zai shiga wannan haki don kuwa kana ganin rayuwa. Koma wa yayi daga can saman kujera ya kwanta yana kallonsa. Ya jima yana cikin tunani da sakawa da kwancewa,kafin ya dauki wayarsa yashiga kiran fiyah. Ta gama alwallar bacci kenan ta fito tajiyo rurin wayar,kallonta

Table of Contents

Chapters

101 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});