Chapter 97
Chapter 97
ɗayyaba. Sai da ya haɗa mini da magiya da lallashi kafin na iya cin kazar amarcin da ya shigo da ita, jikina gau ya ɗau zafi sa boda zazzaɓin da ya rufe ni ga shi dare ya yi balle ya je ya sayo mini magana, amma duk da hakan bai saduda ba ya ɗaga waya wai zai ƙira wani abokinsa mai chemist in bai rufe ba ya je ya karɓo mini magana. Da ƙyar na hana sa fita ta hanyar muna masa cewa na ji sauƙi haka muka kwanta washe gari shi ya tashe ni sallan asubahi nan inda na yi sallan na kwanta baccin huce gajiyan da na kwasa ban tashi ba har sai da gari ya yi haske wannan ɗin ma shi ya tashi ni ya ce na je na wanka na zo na ci abinci sai na sha magani don har ya fita ya amso mini. Kunya ya mamaye ni matuƙar don ni gabaɗaya ma na mance da cewar yanzu ni matar aure ce shi yasa na kwanta na sha baccina hankali kwance. Tashi na yi na wanka da ruwan zafin da ya sanya mini na zo muka ci abincin da ya girka kana na sha maganin bai fita har sai da dangi da ƴan uwa suka fara zuwa gidan nan ma sai da ya Amira da Anty Zulaihatu sun zo kana ya fita bayan ya shaida musu cewar ku kula da ni don ba na jin daɗi. Nan fa suka haɗe kai suka din ga yi mini tsiya zolaya kam babu irin wanda ba su yi mini ba. Sai da suka yi sallan magrib suka tafi bayan sun yi mini nasiha mai ratsa jiki da kashe zuciya, shawarwari kuwa sun ba ni shi daidai gwargwado sun kuma ɗaura ni akan hanyar da ta dace. Haka har na cika sati a cikin gidan aure Yaya Alhassan ne yake yi mana girkin safe duk yadda zan tashi da wuri don na yi aikina to fa sai ya riga ni, sai dai mu yi aikin tare, haka tun ina jin kunyarsa har na saki jikina mussamman da na ga yadda yake ta faɗi tashi wajen ganin ya kyautata mini ba dare ba rana, dole ni ma na yi azaman faranta masa na watsar da komai na rumgumi mijina da kuma laluman hanyar da zan bi in faranta masa rai. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya kwanciyar hankali da nutsuwa suka tabbata a gare ni, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci na yi ƙiba na murmure fatana ta yi kyau har wani sheƙi nake yi kamar bayan kifi. Duk da ba nida haske amma fatata ta yi farau ta washe. Zuciya babu wani damuwa haka nan raina fari ƙal tamkar zaiba. Ranar da na cika sati huɗu muka yi baƙi Saifullah da Muhammad Taufik suka zo wani abun mamakin har da Sheik Dawood sun wuni suna tattaunawa da Yaya Alhassan, ni kam kunya ta hana ni sakat tun da na fito muka gaisa ban ƙara koda wullagawa ta cikin falon sai da za su tafi Yaya Alhassan ya zo ƙira ni. Tabbas ba na buƙatar sai an faɗa mini da kalmomin baki idanuna kawai sun nuna mini cewar Sheik ya sauya don mun sha ruwan addu'o'i da albarka daga gare sa, ya ɗauki Naira dubu asiri ya ba ni da za su tafi. Haƙiƙa Yaya Alhassan ya cika mijin marainiyan da ya ambata kuma ya cika dukkanin alƙawarin da ya yi mini a darenmu na farko, ya inganta rayuwata matuƙa da kuɗin sadakina na shiga harkan kasuwanci atamfofi nake sayar wa da duk wasu nau'in kayan sawan mata, likkafa ta ci gaba don har lefe nake haɗawa mai rai da motsi na fita kunya. Kan ka ce kwabo rayuwa ta sauya jin daɗi ya zauna mana ni da mijina ba mu da wani burin da ya wuce faranta wa juna, na ƙara waye wa da samun ilmin zaman duniya da kuma mu'amala mutanen cikinta. Ranar ina zaune kwatsam sai ga Hajiya Muhibbat a cikin gidana tsabar farin ciki sai da na rasa inda zan tsoma ta mun sha hiran yaushe gamo da ita, tare da ba wa juna labarin bayan rabuwa nan take shaida mini cewar mijinta Saddam zai ƙara aure kuma Zinariya ce matar da zai aura, don ita da kanta ma ta shige masa gaba wajen neman auren, don ta fahimci suna don junansu kuma ba za su iya rabu wa, sannan Saifullah ma zai angwance da babbar jika a gun Sheik Dawood, na yi musu murna matuƙa da lokacin auren ya yi Yaya Alhassan da su Amir suka je su domin shaida ɗaurin auren. Sati ɗaya tsakani Amira ta haihu sai dai ɗiyar ba ta zo da raina ba. Ni kam haihuwar ta yi jinkiri don sai na shekara ɗaya da rabi a gidan aure kafin na haifi ɗa na miji santalele da shi, da sati ya gayayo ya ci sunan Abbana ana yi masa alkunya da Abul-khair watansa biyar a duniya aka yi bikin Amir da ya angwance da ƙanwar mijin Anty Zulaihatu mun sha biki don tare wa na yi a gidan Anty Sawwama, haka Yaya Alhassan ya gama fushinsa har ya sauƙo don kansa, a rage saura Umar kawai wanda kullum nake yi masa tsiya da cewar sai mun daina ba shi abinci. Lokacin auren Muhammad Taufik gayya muka yi muka je mu bikin iyalan Sheikh suka karrama mu matuƙa har muka je muka dawo mu na jinjina halin girma da dattaku irin na su. Na zamo abar alfahari ga mijina iyayen da kuma ƴan uwa har ma da matan cikin unguwan da nake, a ko a kan hanya nake tafiya na ga uwa tana furta munanan furuci ga ɗanta, sai na dakata na sanar da ita illar hakan a wasu lokatan har na kan yanko wani sashi na cikin tarihi don hakan ya sama iznina a gare su. Don tabbas na ishe kowa misali cewar DAFIN HARSHE mussamman na uwa akan ƴaƴanta ya fi dafin maciji illa don shi kassara rayuwa yake yi gabaɗaya. Har gida Saifullah da Muhammad Taufik suka kawo mini matanyensu, Zinariya ma sa ta rikiɗa ta koma sunanta na yanka watau Maryam ta kawo mini mun sha kuka ni da ita, mussamman da ta labarta mini cikin tsananin da ta fuskata da barazana daga wajen Hajiya Babba a yayin da ta yi ƙoƙarin sauya rayuwa, ta ce da ni har hauka sai da ta sa ta yi hauka tuburan har sai an ɗaure ta da mari don in ta bazama ta fice daga cikin gida to fa sai lokacin da Allah ya nufa. Da taimakon Allah da kuma addu'o'i ta sama sauƙi har hankalinta ya dawo jikinta. Ranar wata juma'a mun dawo daga gidan Anty Sawwama da muka kai mata wuni, ina gaba Yaya Alhassan yana baya yayin da yake riƙe da Abul-khair a hannunsa, na zaro makullin daga cikin jakata na buɗe ƙofar falon muka shiga ciki a nan cikin falon muka yada zango. Na amshi Abul-khair da ya fara bacci na je na kwantar da shi kana na dawo. Kusa da shi na zauna na tisa shi a gaba ina kallonsa har sai ya yi magana. "Ke lafiyanki kuwa wannan kallon kamar za ki cinye ni?". Taƙaitaccen murmushi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98