Chapter 73
Chapter 73
ƙarfi na ja fesar ina rarraba idanuna ko zan hango Anty Zulaihatu amma ban gan ta a cikin filin tsakar gidan, da hakan ya ba ni tabbacin in ba ta cikin zaure to tabbas ta fita. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta can ƙasan maƙoshina tare da runtse idanuna sa boda sautin da tarin da Umma take yi har yanzu babu ƙauƙautawa tamkar za ta shiɗe. Duniya ke nan juyi-juyi in ji kwaɗo da ya ji sa a cikin ruwan zafi tsamo-tsamo. Wai yau ruwan da Umma za ta ji ƙa maƙoshinta da shi ne yake neman gagararta, a lokutan bayan ko don gudun rigima da tijararta dole mutum ya kamfata ya ba ta ko da kuwa babu cikakken niyya sai ga shi yau reshe yana neman juyewa da mujiya. "Amatullahi mu je na ba ki ruwan sai ki kai mata ta sha". Idanuna cike da hawaye na ɗago kai ina kallon matar Ustazu Abdulwahab da take tsaye a gabana, ta amshi kofin hannuna ta je ta ciko mini shi da ruwa taf ta kawo mini na amsa, motsa leɓena nake yi da zummar son furzar da kalaman godiya gare ta sai dai na kasa. Fahimtar hakan ya sanya ta faɗin"ba damu ba sai kin gode min ba Amatullah, ki yi maza ki kai mata ta sha ga shi har yanzu tarin bai lafa ba". Kaina kawai na jinjina mata na juya da sauri na koma cikin ɗakinmu na ba wa Umma ruwa ta ɗan sha amma duk da haka tarin bai lafa ba. Jikina yana rawa na soma karanto wani yanki daga cikin yankokin Alqur'ani mai girma tofawa a cikin ruwan kana na ba ta sha. Kamar yankan wuƙa take tarin ya tsaya kamar an yi ruwa an ɗauke, na din ga jeranta mata sannu wani na bin wani tare da gyara mata zamanta tare da sanya mata matashi a bayanta ta yadda za ta ji daɗin zaman. "Umma haka tarin yake yi miki haka kamar zai raba ki da numfashinki?". Ta gyaɗa mini kanta ta na ƙoƙarin yalwata fuskarta da murmushin ƙarfin hali. "Umma dole mu tafi asibiti a duba ki, don a gano ainihin abin da yake damun ki. Zama haka ba zai yiyu ba bari na je na dubo Anty Zulaihatu ta zo ta". Na yi zancen ina miƙe wa tsaye zan fice ta riƙo hannuna hakan ya sa na waigo ina kallonta da ido ta yi mini alama akan na dawo na zauna na kuma yi kamar ta buƙata. "Amatullah ina ji a jikina wannan jinyar ba na tashi ba ne abokin tafiya ne, ki yafe min duk abubuwan da na yi miki, na san da cewar duk halin da kika faɗa ni ce sila DAFIN HARSHEna ne sila. Kaicona! Ba na tunanin akwai wani maganin da zan sha na sama sauƙi ko da kuwa na sama sauƙin ma to iya na gangar jikina ne, amma ciwon da yake cikin zuciyata yafiyarki gare ni kawai zai warkar da wannan gyambon". "Umma kin wuce komai a wajena haka zalika kin fin ƙarfin komai. Wallahi wani ne ya yi mini ba daidai ba ki ka ce na yafe masa to an gama maganar ke nan balle kuma ke da kanki. Umma na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki ɗaya amma don Allah ki bari a kai ki asibiti, a nema miki magani". Ina gama maganan na tashi na fita ina fitowa na hango Anty Zulaihatu tana shigo hannunta riƙe da baƙin leda. Na yi hanzarin isa gare ta"Anty Zulaihatu don Allah ki zo mu kai Umma asibiti". Da sauri muka isa cikin ɗakin, muka haɗa muka rawa mu tafi asibiti Umma ta ce ba za ta je ba har Yaya Alhassan muka ƙira a waya ya zo ya saka baki amma ta ƙeƙashe ƙasa ta ƙi yarda. Yaya Alhassan ya ce a bar ta zuwa gobe ko za ta sauƙo ko kuma a ƙira likitan ya duba ta a gida, tare da Anty Zulaihatu muka share ɗakin muka tsaftace ko'ina. Muka yi wa Umma wanka muka sauya mata kaya. Sai dab da magrib Anty Zulaihatu ta koma gida sa boda a ranar mijinta zai dawo. Haka na zauna na Umma na tisa ta a gaba na din ga karato mata karatun Alkur'ani da nufin ko za ta sama nutsuwa a cikin ranta. "Amatullah Allah ya miki albarka". Babu shiri na tsaya daga karatun da nake yi ba tare da na zo gaɓar da ya dace na tsaya a ƙa'idance ba. "Umma me ye ki ka ce?". "Ce wa na yi Allah ya yi miki albarka". Ban iya amsa wa da kalaman baki ba, illa jan jikin da na yi na isa kusa da ita, hawayen farin ciki da murna su na zuba daga idanuna, ba zan iya tuna ranar da Umma ta taɓa sa mini albarka a kaf cikin rayuwata ba. "Umma na gode, ke ma don Allah ki yafe mini kura-kuren da na yi miki". Ta sa hannu ta shafo kaina"ba ki taɓa ɓata min ba Amatullah, Allah ya raya ki". "Amin ya Allah". Na amsa da shi ina kwantar da kaina a bisa kafaɗunta ina ta sauƙe ajiyan zuciya tamkar wacce ta yi gudun ceton rai. Sanadin albarkan da Umma ta sanya mini na ji na manta da dukkan damuwata har na ji wani nutsuwa ya mamaye mini ruhina. Ina zaune a haka ban san lokacin da bacci ya sace ni ba. Muryar Umma shi ya yi silar farkar da ni daga baccin da ya ci idona. "Ki tashi ki rufe mana ƙofa, sanyi ya fara sauƙa". Firgitit! Na buɗe idanuna ina kallon cikin ɗakin da duhu ya mamaye ko'ina alamar dare ya daɗe da yi. Na lalumi wayar da yake wajena na kunna haskenta tare da duba lokaci da ya nuna mini ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare. "Subhanallahi! Umma kin ga har dare ta yi". Na yi zancen ina tashi na sassauƙe labulen tagogin sannan na rufe ƙofan ɗakin, na zo na zauna a nutse na soma faɗin"ni kuwa Umma ina kayan cikin falon suke na ga har cikin ɗakin babu komai. Daga tabarman nan fa sai ƙunshin kayan sakawanki". "Na sayar da komai da yake cikin ɗaki da falon nan, duk kuɗin su ƙare akan jinyata kafin Alhassan ya kawo min ɗauki. Amatullah tabbas Sawwama da ƴaƴanta su cika cikakkun masoya a gare mu, don ba kowa ba ne za a yi masa abin da na yi Alhassan kowa har ya dube ni da idon rahama a lokacin da nake buƙatar taimako daga gare sa". Kalamanta suka sanya jikina yin sanyi ƙalau na taƙaita zance ta hanyar gyara mata wajen da za ta kwanta na kwantar da ita bayan na yi mata alwala da ruwan goran da Yaya Alhassan ya kawo mana ɗazu da ya zo shi, na shafe mata jikinta da addu'a ni ma na kwanta a gefenta. Sai dai bacci ya ƙi ziyartar idanuna haka na yi ta tunani masu nauyi, kafin wasu hawayen tausayin kanmu da yadda rayuwa ta mayar da mu ya fara zuba daga idona. Ina ma wanda ya mutu yana dawowa tabbas da sai na bayar da duk wasu abubuwan da na mallaka a cikin duniya, don kawai Abba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98