Chapter 87
Chapter 87
game da Altine wanda hakan ya faru ne ta dalilinki. Amatullah kin zama silar bayyanar haske a cikin rayuwarmu kin cuce rayuwar su Ayan daga zalunci, cutarwa da kuma ha'incin da Atline ta daɗe tana aikatawa gare su ta ƙarƙashin ƙasa. Tabbas idan abubuwa ya daidaita ma Anty Muhibbat za ta zo da kanta ta yi miki godiya har gida sai dai a yanzu ta ce kunyarki take yi". "Wani irin kunya ke nan?". "Kunyan abubuwan da ta yi miki mana". Na saki taƙaitaccen murmushin da ya tsaya iya kan leɓena kafin na ce"don Allah ka sanar da ita cewar tarin alkhairan ta gare ni sun shafe komai. Ta riƙe n bisa gaskiya da kuma zuciya ɗaya ba ta taɓa yi mini wani abun cutarwa ba don haka bai kamata ta ji kunyata ba". Da alama ya ji daɗin zantukan da na jero don ina jin yadda yake ta sauƙe ajiyan zuciya wani na bin wani. "In sha Allah zan sanar da saƙonki a kumnuwanta". "Amma da san da cewa ka na zuwa gidanmu?". Cike da ƙwarin gwiwa ya mai do mini da amsa"ƙwarai kuwa hasalima ita ta ba ni ƙwarin gwiwan tunkaranki don ita ma kanta ta yaba da nutsuwa, hankali da kuma riƙon amananki". Lamau na yi tamkar mai bacci har sai da na ji ya ci gaba da maganan"amma ko zan iya sanin dalilin ƙiran da ake yi min na gaggawa kafin goben?". "Me kake ci na ba ka na zuba? Allah dai kawai ya kai mu goben ko ma mene ne ai za ka ji". "Haka ne kam". Mun ɗan taɓa hira kafin muka yi sallama da wuri na kwanta, don ina so na tashi na yi sallan dare kamar yadda na saba. Washe gari ban sanar da kowa zancen zuwan Saifullah sai dai kawai ina zaune a ɗaki Anty Sawwama ta ɗago labulen ɗakin. "Sai ki fito ki na baƙi". Gabaɗaya na manta da cewar mun yi magana da Saifullah mussamman da na ji ta ce baƙi maimakon ta ce baƙo. "Wasu baƙi kuwa? Ba wasu baƙin da muka yi da su za su waje na yau". "In ki ka fito ai za ki gan su, a nan ne za ki gane kin san da zuwansu ko akasin haka". Ta dasa aya a nan ta saki labulen ta yi ficewar ta, ta bar ni saƙa da warwara a cikin raina. Haka na tashi na saka hijabina na fito ina saka ƙafana a cikin falon Ayan da Aryan suka rugo da gudu har suna karo da juna suka rungume ƙafafuna. Tsugunawa na yi a gabansu ina shafa fuskokinsu don tabbas Allah ya jarabce ni da wani irin zafafan ƙaunar yaran wanda hakan ya samu asali daga soyayyar da nake yi wa duk wasu ƴan biyu musamman masu kama iri kwabo da kwabo ɗin nan. "Yaushe ku ka zo?". "Ba mu daɗe da zuwa ba, tare da Uncle Saif muka zo mu. Kuma Umminma ta ce in mun zo mu gaishe da ke sosai sosai". Aryan ya yi zancen har yana kwaikwayon muryar Umminsu. "Ina amsa wa ni ma in kun koma ku ce ina gaishe ta". Kansu suka gyaɗa mini alamar sun ji da hakan ya sa ni tashi tsaye na riƙon hannunsu muka ƙarisa cikin falon, Yaya Alhassan ne da Umar sai kuma Anty Sawwama yayin da gefe guda kuma Saif ne zaune Muhammad Taufik yana kusa da shi suke ke nan a cikin falon. Sai da na zauna na gaishe su suka amsa take na ji tausayi da tunanin halin da Muhammad Taufik zai shirga bayan na aikata abin da zuciyata take ingiza ni na yi. A zahiri hankalina yana kan su Ayan da suke ta zuba mini suturu sai dai hankalina yana kan hirar da su Yaya Alhassan suke yi, har zuwa lokacin da Saif ya ce zai je ya kai Muhammad Taukif filin jirgi don jirgin ƙarfe goma sha ɗayan rana zai bi zuwa cikin Abuja. Ya yi sallama da Anty Sawwama yayin take ta sa masa albarka da yi masa addu'ar Allah ya sauƙe shi lafiya. A nutse muyarta can ƙasan maƙoshina na furta"Allah ya sauƙe ku lafiya mun gode da ziyara". Caraf idanuna suka sauƙa cikin na Muhammad Taukif, shi ya fara janye na sa idanun ya na amsa da kalmar Amir yayin da suke fice wa daga cikin falon. Na kwashe su Ayan muka shige cikin ɗakin har muka fito na ɗaura girkin rana na gama na yi alwalan sallan zuhur na yi sallan, ina zaune kan sallayan yayin da su Ayan suke gefe na suka cin abincin da na saka musu. Na ji wayata ta soma ruri na yi hanzarin ɗauka tare da ɗaga ƙiran, maimakon amsa sallamar da na yi sai ji na yi an sauƙe ajiyar numfashi mai ƙarfin sauti. "Ina ga dai matar nan kin manta da cewar ki na da baƙo ko?". Na dafe goshina kafin na ce"afuwan na ji tunanin ba ka dawo ba ne ai". "Na dawo ina ƙofan gida ina jiranki za ki fito ne ko kuma na shigo?". Da sauri na ce"A'a ka tsaya a nan zan fito". Sai da na yi maganan sai kuma ni da kaina na ji kunya na katse ƙiran na tashi na je wajen ajiye kayana na ɗauko jakar da na sanya memory card ɗin nan a cikin na ɗauka. "Ku zauna a nan ba ri yanzu na je na dawo kun ji". "To". Suka haɗe baki wajen amsa wa da hakan ya ba ni damar fita, ban iske kowa a falo ba hakan ya ba ni salama da nutsuwar fice wa wajen kaina tsaye. Ina fitowa na hango shi tsaye a jikin motarsa yana latsa wayarsa. Da sallama ɗauke a bakina ya amsa mini yana ɗago kai tare da kafe ni da ido bayan ya mayar da wayan cikin aljihunsa. "Ki bar Bawan Allah Saifullahi marayan Allah yana ta jiranki a cikin rana". Na sadda kaina ƙasa"ai ka dawo da ka shigo ciki". "Kayya! Wallahi kunyar Anty nake yi shi yasa kawai na tsaya a nan, yanzu dai ina sauraronki don jiya na kwana cikin zaƙuwa". Na ɗan tsagaita kafin na miƙa masa memory card ɗin da yake hannuna ya karɓa yana jujjuya shi a hannunsa. "Wannan fa na mene ne?". "Ina so idan ka je gida ka nutsu ka saurare abin da yake cikinsa da zaran ka gama saurara sai ka ƙira ni mu yi magana". Shuru ya yi kallona kamar mai nazari ko kuma son gano wani abu, sai can ya ce"to shi ke nan ba matsala". Ya ƙare zancen yana cira wa a cikin aljihunsa. "Yanzu za ku wuce ne?". Ya waro idanununsa tar a kaina"to fa! Kora da hali ake yi mana ke nan? To shiga ki kwaso min su mu wuce". Kunya ya lulluɓe ni har sai da na rufe fuskana da tafukan hannayena. "Ba fa haka nake nufi ba, na ga su Ayan abinci suke ci ne shi yasa na tambaya". "Su sun sama karramawa ke nan tun da har girki aka yi musu. Saɓanin ni ɗan marayan Allah da aka shanya ni a tsakiyar rana aka manta da kashi na". "Wallahi Yaya Saif ba haka ba ne ban san ka dawo ba ne.....". Ban ƙarisa zancen ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98