Chapter 56
Chapter 56
"Ya isa haka ya isa Amatullah". Hajiya Muhibbat ta dakatar da ni ba tare da na gama amaryar da zancen da yake kan harshena ba. "Mai zaman kanta? Kin san ma'anar wannan kalmar kuwa Amatullah? Kin ba ni mamaki matuƙar ina miki kallon mai hankali da nutsuwa wacce ba ruwanta ashe kallon biri nake yi miki ki na yi min na ayaba. A ƙananun shekarunki har kin san ki sanya ƙafa ki baro cikin gidan iyayenki ki zo inda ba ki san kowa ba kuma ba wanda ya san ki ki fara zaman kanki. Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Wace iriyar rayuwa ce muke rayuwa a cikin ta haka? Me yasa masifu da bala'i kala-kala ba za su baibaiye al'ummar mu ba?". Ta tsagaita tare da yarce ruwan ƙwalla da ya zubo daga idanunta kafin ta ɗaura daga inda ta tsaya. "Daga yau ba na son na ƙara ganin ki a kusa a gidan nan balle kuma ki tsaya a jikin gidan nan, na sallame ki ki ƙara gaba niyyar da taimakon da na yi Allah ya ba ni ladan niyya ke kuma idan mai shiryuwa ce Allah ya shirya ki. Ga kuɗin aikinki". Ta ƙare zancen tana zige jakarta ta ciro wasu kuɗaɗen da ko tsaya wa ƙidaya su ba ta yi ba, ta watso mini su a fuskana. Hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa dandamalin kuncina na cira kai na dube ta sai da na fizgo numfashina da yake maƙale mini a ƙirji kafin na sama zarafin magana. "Duk magangunin akan turban gaskiya kike amma ke ma ina son na sanar da ke wani abun da ba ki sani ba. Kamar yadda rayuwata take cikin hatsari haka ke ma ta ki rayuwar da ta ƴaƴanki take cikin hatsari sanadin yarda da amincin da kika ɗaura akan mutane guda biyu da kike ganin sun fi kowa kusanci da ke a cikin wannan duniyar". Na ƙara taku uku na matso kusa da ita sosai da tun da na soma maganar take bi na da kallo cike da maɗaukakin mamaki da ya haɗu da al'ajabi. Kafin na yi magana ta ri ga ni. "Wasu mutane biyu kike magana a kai?". Na saki wani bushashshiyan dariyar da ba ta da alaƙa ta kusa ko ta nisa da nishaɗi kafin na furta"mutum na farko shi ne mijinki wanda a tsakanin gobe da jibi zai shigo cikin ƙasar nan ba tare da saninki ba, kuma ina da tabbacin har ya zo ya koma ba zai nema inda kike ke da ƴaƴanki ba. Sannan mutum na biyu ba kowa ba ne face Altine ƴar aikin da kika riƙe tamkar ƴar uwa kika busa mata iskar ƴancin yayin da ita kuma take amfani da yardar da kika yi mata take cutar da ke, ke da ƴaƴanki". Na ƙare zancen ina yi mata nuni da Altine da ƴar manuniyar ƴatsata. Ban gama rufe bakina na ji sauƙar wani gigitaccen mari a bisa kuncina har sai da na soma ganin gilmawar baƙin duhu a cikin idanuna, na yi tangal-tangal zan faɗi da ƙyar na iya sarrafa kaina na tsaya akan ƙafafuna. Ta cakomo wuyar hijabina ta riƙe tamau. "Ke har me ye kika sani akan mijina da za ki faɗa wannan maganar akan sa? Sannan yaushe kika zo cikin gidan nan da za ki gaya min wace ce Altine? Babu wani halinta wanda ban sani ba ta kai ta kawo ko ba ta furta magana da bakinta ba ina ya fahimtar abin da take nufin. Ina kika sama ƙwarin gwiwar nan?". "Tabbas ban san mijinki amma a yanzu na san abubuwan da ke ma kanki ba ka sani ba game da halinsa. Idan ba ki yarda da abin da nake faɗa ba za ki iya samunsa ranar juma'a a babbn otel ɗin da ke cikin garin Abuja. Batun Altine kuma za ki iya tambayar ƴaƴan idan tsoro bai hana su faɗa ba". Mamakin furucina ya sanya sakar mini hijabina da ta riƙe. "Saifullah ka kawar min da yarinyar daga gabana, tun kafin zuciya ta ɗebe ni na lahanta ta na kashe banza na kashe wofi. Ba na son na buɗe idona na gan ta a gabana". Sai a lokacin Saif ya yi magana da tun ɗazu yake tsaye a wajen yana bin mu da kallo ba tare da ya ce uffan ba. "Anty don Allah ki kwantar da hankali, mu saurare abin da za ta ce wataƙila mu dace da wani ilmin da mu kanmu ba mu san shi ba". "Saif babu wani mahalukin da zai tsaya a gabana ya sanar da ni wani hali na Saddam wanda zai Muhibba ban san shi ba, a cikin tsawon zaman da muka yi da shi. Balle kuma Altine duk ranar duniya take muke kwana mu tashi a cikin gidan nan, ka fitar min da yarinyar nan daga cikin gida". Cikin in-i-na Altine ta ce"wallahi ƙarya ma take yi min ba ni da wani mummunan halin da na ke ɓoye miki shi". Cikin ba da umarni Saif ya ce"Altine ɗauki su Aryan ki shiga ciki da su". "To ranka ya daɗe". Ta amsa da shi cikin bin umarni da girmamawa, ta kwashe su Aryan suka yi cikin gida. Zai yi magana na tar numfashinsa. "Zan fita ba sai ka fitar da ni ba, Hajiya ko ba ki ce da ni kar na ƙara zuwa cikin gidanki ba ni ma daman ina da niyyar sallamar kaina daga wannan aikin, sai dai ina mai ba ki shawara da ki nutsu ki yi nazarin abubuwan da na sanar dake yanzu. Ko ba daɗe ko ba jima watarana za ki neme ni ki kuma gode mini". Tas na ji ta kuma ɗauke ni da wani marin mai matuƙar sauti a karo na biyu. Na kai hannuna na dafe kuncina ina cije leɓena sa boda zafin marin da ya ratsa har cikin ƙoƙon kaina ya kuma raunana ƙarfin jiki da zuciyata. "Na gode ranki ya daɗe, na gode bisa halin girma da karamcin da kika nuna mini". Ina dasa aya a nan na sunkuya na kwashe kuɗin da ta watsa mini don na san su ɗin haƙƙina, na raba biyu na ɗauki ɗaya na damƙa mata ɗayan. "Na ɗauki iya haƙƙina ga ragowar dukiyarki". Ban jira abin da za ta ce mini ba na fi tafiyata ina tafe hawaye duk yadda na so sarrafa kaina wajen ganin na tsayar da ruwan hawayen da yake kwaranya daga kurmin idanuna lamarin ya gagare ni. Na buɗe ƙaramar ƙofar jikin gate ɗin zan fita muryar Baba Mai Gadi ta tilasta mini dakatawa. "Ƴar nan kar ki tafi ba tare da kin warware min ƙullin zantukan da na ji ku na musayarsu ba. Shin da gaske ne abin da Altine ta faɗa akan ki? Da gaske ke ɗin karuwa ce kuma zaman kanki kike yi?". Sai da ya yarce hawaye da suke tsare-tsare a kuncina kana na ce"e Baba duk abin da ka ji haka yake, zaman kaina nake yi a garin nan sannan a cikin gidan karuwai nake rayuwata". Ina gama faɗin haka na fice daga cikin gida fita irin wacce ba na fatan ko a cikin mafarki na dawo, fita irin wacce babu waiwaye har abada balle dawowa. Fita ita wacce take datse ko wani irin alaƙa da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98