Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 70

Chapter 70

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

"Wallahi Anty ko daidai da rana guda ban taɓa aikata abin da kike zargina da shi ba. Ko karuwan da muka zauna da su cikin gida ɗaya za su ba da wannan shaidan a kaina cewar ban taɓa keɓewa da wani ɗa na miji ba". Ta ɗan yi jim kafin can ta ce"Amatullah Amir fa ya sanar da mu duk yadda aka yi da kuma irin dambarwan da aka yi da Magajiyar gidan Karuwan da kike zaune a ciki, kafin har suka iya samun daman tahowa da ke. Babban abin baƙin cikinmu ma shi ne a ranar da suke je neman ki a ba ka kwana a cikin gidan ba hasalima a ɗakin otel kika kwana". Cikin ƙarfin halin ta ƙare zancen sa boda kukan da ita ma ya karyo mata, kasa magana na yi illa jijjiga kaina da kawai nake yi yayin da zuciyata ta yi mini nauyin gaske yayin da na kasa samun damar harhaɗa kalaman da zan kare kaina a gare ta. Haka muka ci gaba da kukan ni da ita har izuwa lokacin da Umar ya shigo ya ce wai mu fito mu ci abinci sai da ta taimaka mini kafin na iya miƙe wa akan ƙafana muka fito falon, muka iske kowa yana zauna da Yaya Alhassan muka fara haɗa ido na ga ya wurga mini wani mungun hararan da ya hautsina kayan cikina, muka zauna tare da Anty Zulaihatu ta soma zuba abincin ga kowa yayin da dukkanmu muka yi shuru kowa da irin tunanin da yake saƙawa a cikin ruhinsa, juya cokalin kawai nake yi a cikin abincin don ni kam ba na tunanin ko na saka abincin akan harshena zan iya haɗiye wa har ya wuce ta cikin maƙoƙarona da ya bushe tamkar ƙasar sahara a cikin tsananin zafin rana. "Ki ci abincin mana". Na tsinkayo muryar Anty Sawwama ta sauƙa a cikin kunnuwana. Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina ɗan gyara zama na buɗe bakina zan yi magana kenan na ji wani kuka ya ƙwace mini mai matuƙar sauti, da ya jawo hankulansu gare ni na kifa kaina akan gwiwoyina ina rera kukan daga can ƙasan zuciyata. "Wannan kukan kuma na mene ne Amatullah?". Anty Sawwama ta jefo mini tambayar cikin tsananin kulawa yayin da take ɗago kaina da na kifa shi tana share mini hawayen fuskana. "Ya kamata ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi tun da sanda kika shigo cikin gidan nan fa, kuka kawai kike yi ko daidai da minti guda ba ki bar idanunkin sun huta ba. Ya kamata ki tausaya wa kanki". Numfashi mai zafi na ja na fesar daga baki kafin na sama damar cewar"Anty don Allah ku yarda da ni wallahi tun da sa ƙafata na fita daga cikin gidan nan, ban taɓa aikata wani abun da na san cewa Allah ya haramta sa da gangan ba, na yi iya ƙoƙarin kiyaye kaina daga faɗawa cikin halaka da fushin Ubangijina". Ta ɗaga mini hannu alamar maganar ya isa haka dole na ja bakina na yi masa linzami. "Mu gama cin abincin sai mu yi magana". Ban iya ce mata komai ba illa jinjina kaina da na yi, haka aka ci gaba da cin abincin sai dai ni kam ina ci ne kawai ba wai don ina jin ɗanɗanon abincin a bisa harshena ba, haka nan ba don ina son cin abincin haka na ci gaba da tuttura abin cin har muka gama ci. Muka tattare wajen tare da Anty Zulaihatu muka wanke kwanukan, na dawo na zauna a ɗaki ina ta tsammanin ko Anty Sawwama za ta aiko a ƙira ni ta ba ni damar fayyace musu komai amma ba ta yi hakan ba, haka muka kwana ba tare da wani ya ce mini ci kanki ba na yanki dare na yi kuka mai tsanani har sai da na ji numfashina yana cushewa waje guda kafin na tsagaita, na tashi na fita na ɗauro alwala na zo na fuskanci alƙibla na tada kabbara. Raka'a biyu na yi a fashe wa Ubangiji da kuka a cikin sujjadata na ƙarshe. Daren ranar ban iya runtsawa ba hakan ya sa ni washe gari na tashi da wani irin matsanancin zazzaɓi mai dafa jiki. Ina kwance a ɗakin Umar ya shigo ya iske ni a haka ya ruga ya je ya sanar da Anty Sawwama ta zo ta ɗago ni ta ji jikina ya ɗauki zafi gau. Ta sa Umar ya riƙa Yaya Alhassan ya zo shi ta ce ya kai ni asibiti yayin da ta umarce Anty Zulaihatu ta raka ni sa boda a gidan ta kwana, don a daren jiya na ji tana waya da mijinta yana shaida mata yau zai dawo daga tafiyar da ya yi. Hijabina na saka na tashi tsaye yayin da Anty Zulaihatu ta riƙe mini hannuna sa boda yadda jiri yake ta faman kai ni ƙasa. "Alhassan idan kun je ayi mata dukkanin gwaje-gwajen da suka kamata". Ciken rashin fahimtar inda zantukan natan suka nufo ya ce"wasu irin gwaje-gwaje ke nan Umma? Na yi tunanin ai zazzaɓi ne kawai". "A yi mata gwajin dukkanin cututtuka ciki har da na cuta mai karya garkuwan jiki da kuma gwajin ciki". Take na ji ƙirjina ya buga kwatankwacin irin bugun da maƙeri yake yi wa ƙarfi da dukkan ƙarfinsa. Kalaman Anty Sawwama suka karyar mini da zuciya tare da haifar da wasi-wasi a cikin zuciyata, mamaki ya cika mini raina sai dai na gaza juyowa na kalle ta kamar yadda na kasa ɗaga ƙafana na bar wajen. Sai da Anty Zulaihatu ta ja hannuna muka bar wajen kafin na dawo cikin hayyacina haka muka fita muka nema adaidaita muka shiga zuwa asibitin. Mu na zuwa aka ƙarbe ni aka yi mini duk wasu gwaje-gwajen da suka dace ciki kuwa har ta waɗanda Anty Sawwama ta lissafa. Tunin magunguna aka rubuta mini cikin har da ƙarin ruwa sun so su ba ni gado Yaya Alhassan ya ce su rubuta mini magani kawai. Haka muka saya magungunan jimgim muka koma gida a yadda muka iske Anty Sawwama ta na ta faman safa da marwa a tsakar gidan ya tabbatar mini da cewar duk da muka fita daga cikin gidan ruhinta bai huta ba hakan nan zuciyanta bai daina saƙa mata abubuwa ba. Sai da muka shiga cikin falo muka zauna sannan Yaya Alhassan ya tabbatar mata da cewar babu ciki a jikina kuma likitoci sun tabbatar da cewar ko cutar sanyi ba na ɗauke da ita balle cuta mai karya garkuwa jiki watau siga. Silalewa daga kan kujerar da take Anty Sawwama ta yi ta yi sujudul shukur tana gode wa Ubangijnta Sarkin da bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Ta daɗe kafin ta ɗago ta koma mazauninta ta yi alama da idon akan na zo kusa da ita na zauna. Kamar yadda ta buƙata haka na yi na je kusa da ita na zauna na sadda kaina ƙasa yayin da ta riƙo hannayena ta sanya cikin nata ta na murzawa a hankali ta ce"Uwata ɗago idanunki ki kalle ni" a hankali na ɗago idona ina kallon fuskarta da ta washe da annuri. "Ba wai ina tantama akan tarbiyyanki ba ne amma shin da gaske ne tun da kika saka ƙafa kika fita daga cikin

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});