Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,216 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ɗauke ki aiki idan har kin amince yanzu ma sai mu wuce gidan ki gani". Ta sauƙe tagwayen ajiyan zuciya tare da cewa"na amince na gode sosai Allah ya saka miki da alkhairi". "Amin ya Allah, to ni dai sunana Hajiya Muhibbat na yi aure shekaru biyar da suka wuce ina zaune da mijina cikin farin ciki da ƴaƴa biyu tagwaye. Ni ƴar kasuwa ce da take harkan sayar da atamfofi da haɗa kayan lefe, ina da manyan shaguna har guda uku a cikin ƙwaryar garin nan. Mijina yanzu haka ba ya ƙasan nan ina zaune ne tare da ƴaƴana da kuma ƙanin mijin nawa Saifullah". "Allah ya yi wa rayuwa albakar ya ƙara muku kwanciyan hankali da son junanku". "Amin ya Allah". Ta amsa cikin jin daɗin da ya bayyana har a bisa fuskanta daidai lokacin da muka iso bakin gate ɗin wani gida madaidaici sai dai tsarin ginin ya ƙawat matuƙar gaske, ta yi horn aka zo aka buɗe gate ɗin ta shiga ta yi parking ɗin motar a filin da aka tanada mussamman domin ajiye motoci. Ta fito tana gaba ina bin ta a baya har cikin gidan. Muka yada zango a falo ta zauna a bisa kujera yayin da na zauna a ƙasa ina sauraron abin da take faɗa. "To kin ga dai inda nake zaune nan ne gidan mijina wanda na riga na yi miki bayanin komai. Tagwayena suna gidanmu wajen mahaifiyata za su yi hutun ƙarshen mako a can, ƙanin mijina kuma Saifullah ya tafi wajen aiki, engineer ne amma yanzu haka yana harkar siye da siyen filayi da gidaje ne. Zan yi magana da mijina zuwa anjima da yamma sai ki dawo ki ji yadda muka yi da shi". "To ranki ya daɗe na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". "Amin ya Allah. Ɗauki wannan ledodin naki ne". Ban ce komai ba na ɗauki ledar maganin zan fita ta dakatar da ni"sauran ma dukka na ki". Zan yi magana ta ɗaga mini hannu"kin gan ni nan ba na magana biyu, a ke na saya don haka ki ɗauka domin ni ba na buƙatar su". "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi". Ba ta amsa ba illa murmushin da ta sakar mini na ɗauki ledodin na fita, duk nisan tafiyan da zafin da ƙafafuwa suke yi mini ban ji su dame ni ba saboda farin cikin samun aikin da na yi ta hanyar da ban taɓa tsammani ba balle zato. Na tarar da La'aniyatu ba ta nan amma ta ajiye mini makulli a kan taga na ɗauka na buɗe ɗakin na shiga na fito na yi alwala na shiga na yi sallan zuhur a nan inda na yi sallan na kwanta wani bacci mai nauyi ya ɗauke ni ban tashi ba sai can yamma na yi sallan asr kana na jawo ledodin da ta ce ni na buɗe su, kayan ƙwalam da maƙulashe ne burji a cikin ledan, ɗayan ledan kuma lemukan gora ne kala daban-daban. Na ɗeba wasu na soma ci sai da na gama na tashi na ajiye sauran na tashi zan fita kenan La'aniyatu ta shigo. Muka sakar wa juna murmushi yayin da take ƙariso wa cikin ɗakin. "Ina kika je ne na dawo ban same ki ba?". "Umma ce ta aike ni. Na ga kin tashi kamar ƙara fita za ki yi?". Na matso dab da ita"albishirinki". "Goro fari ƙal". "Na sama aiki yanzu ma can zan je na ji matsayina". Cike da farin ciki ta ce"a ina? Zauna mana ki ba da labari kafin ki tafi". Na jijjiga kaina"a'a ki bari sai na dawo sai ki ji komai, ga makullina nan idan kin fita ki rufe mini ƙofan". Ban tsaya jin abin da ta ci gaba da faɗi ba na fice da sauri. Sai da na iso ƙofar gidan na goge gumin da na haɗa kana na ƙwanƙwasa mai gadi ya fito ya buɗe mini na shiga ciki, na yi sallama aka amsa mini kana na shiga na iske wata mace zaune tare da wasu yara biyu masu tsananin kama da juna dukkan su maza sun yi shiga iri guda. Na tsuguna na gaishe ta ta amsa mini a taƙaice ta na bi na da kallo. "Hajiyar ta nan kuwa?". "Lafiya kike neman ta?". "Ita ta ce na zo". A wulaƙance ta ce"to sai ki jira ta ta fito". "To". Na amsa da shi a taƙaice zan zauna akan capet ta ce na sauƙa ƙasa, ban yi mata musu ba na yi kamar yadda ta ce. A ƙalla mun yi fiye da awa ɗaya zaune a wajen muna jira kafin ta fito tana fitowa yaran suka yi wajen ta da gudu suka rumgume ta. Ta riƙo hannunsu suka ƙariso suka zauna kafin ta ce"Altine ku da muka yi da ke za ku yi kwana biyu a can, ya ya kuma na gan ku yau?". Matar da ta ƙira da altine ta kaɗa baki ta ce"wohoho Hajiya ai Alhaji ƙarami ne ya je gidan gaida Hajiyarki dagan kuma ya ce a dawo da su, ko kuma shi ma ya haɗa kayansa ya koma can ayi hutun ƙarshen makon a shi". "Saifullah ke nan shi dai ba ƙaunar yaran nan su yi nisa da shi". "Ƙwarai kuwa Hajiya, ai ni tun da nake ban taɓa ganin ƙauna irin wannan ba. Hajiya ga baƙuwa nan kin yi. Sai a lokacin ta lura da kasantuwana a cikin falon ta kai idon ta kaina"ki ƙariso ki zauna mai kyau mana". Ban ce komai ba na tashi na iso gaban ta na zauna tare da gaishe ta ta amsa tare da zarce wa da faɗin"mun yi magana da shi ya kuma amince don haka za ki iya fara zuwa daga gobe, albashinki naira dubu ashirin ne duk wata sannan aikin da za ki na yi shi ne sharan cikin gida, mopping da kuma girki. Idan na yaba da tsaftan da kuma ƙarewarki akwai yiyuwar na ƙara miki albashi". Take na durƙusa ina ta jeranta mata godiya kamar zan yi aron baki ta nuna mini cewar babu komai. Ta ba ni naira ɗari biyar ta ce na yi kuɗi mota sai gobe na fara fitowa aiki lokacin har an fara ƙiraye-ƙirayen sallan magriba. Haka muka yi sallama raina fari ƙal kamar nono kindirmo ina ƙoƙarin fitowa daga falon na yi karo da mutum har sai da abin da yake hannunsa ya faɗi ƙasa. Waya ne da ya faɗi na tsuguna da sauri na ɗago na miƙa masa ina faɗin"ka yi haƙuri wallahi ban lura da kai ba ne.......". Miɗik na haɗiye ragowar zancen saboda firgitan da na yi. Na tsaya cak ina kallonsa tare da wassafo inda na taɓa ganin fuskarsa. Take na nufa inda na taɓa ganin sa shi ne wanda muka haɗu da shi yau da asuba har ya ba ni sallaya na yi salla a kai. [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 4️⃣7️⃣ "Ke ce? Me ya kawo ki nan?". Na rusunar da ƙwayoyin idanuna ƙasa saboda ba zan iya juran irin kallon da ya katse ni da shi da ya fi kama da na tuhuma ba. Kafin na kai ga ba shi amsa tagwayen yaran suka fito a guje har suna rige-rigen rumgumansa ya

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});