Chapter 5
Chapter 5
yi masa na rodi? Ke ma ai ware rana za ki yi ki je ki tare Alhajin wata ki fanshe abin da aka yi miki. Yo ai daman bariki alelen gero ne duk wanda bai iya ba kwaɓe masa take yi, don haka kowacce ta gama harkokin gabanta a watse na kashe wannan case ɗin". Tsimi-tsimi na ga kowacce ta ja jikinta ta koma ɗakinta bayan an gama jefawa juna harara da kallon uku saura kwata. Ni ma koma ciki na zauna ina ta jiran na ji an yi ƙiran sallan zuhur amma shuru kamar an aike Bawa garinsu. Ganin wankin hula yana neman kai ni dare na dauki ɗayan pure watern da na ajiye na fito na yi alwala da shi na shiga na yi sallan zuhur ina zaune inda na yi sallan La'aniyatu ta shigo, muka sakarwa juna murmushi kafin ta ce"har ya tafi kenan?". "Waye fa?" "Aminu mana tauraro mai wutsiya ganin ki ba alkhairi ba". Na saki taƙaitaccen murmushi ba tare da na ce da ita komai ba. "Kin ga mutumin kusan rabi da kwatan matan gidan nan shi ya kawo su, kuma duk wanda suka kwanta da shi ya biya su sai an cire masa nasa kason mai tsoka a ciki. Wani zubin har ɗaukan su yake yi ya kai su wajen manyan mutane su yi haramtacciyar mu'amala, akan kuɗi babu abin da ba zai iya aikatawa ba. Kuma ke ma ina tabbatar miki da cewar duk wannan rawan ƙafa da ɗawainiyyar da yake yi a kanki zzi fanshe su tsaf har da riba". Na yi shuru na kasa cewa komai sai can na furta"Allah ya kyauta shi kuma Allah ya ganar da shi". Ba ta amsa ba illa taɓe bakin da ta yi tana ɗauke kanta gefe guda. "Tun ɗazu ina ta zaune a nan ina jiran ƙiran salla amma shuru". "Ƙiran salla dai? To ai ko za ki shekara a nan ba za ki taɓa jin ƙiran salla ba. Tun daga farkon layin nan har ƙarshenta babu masallaci, islamiyya ko kuma wani majalasin da ake koyar da faɗin Allah da Manzonsa. Ke in taƙaice miki bayani babu wani ɗan arzikin da yake biyo wa a layin nan don duk mutumci da kimarka idan aka ganka a layin daga ranar ba za a ƙara yi maka kallon mutumci ba. Idan kin ji ana faɗin layin jahannama to layin nan kenan". [12/3, 2:54 PM] Aeesher: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam _________________________________ Page 4️⃣3️⃣ Na sauƙe ƙatuwar ajiyar zuciya ina dafe ƙirjina da ya bugawa tamkar zai faso nama da fatana ya bayyano waje, ta kalle ni ta saki murmushi"mamaki kike yi ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta daman zarcewa da faɗin"indai mamaki kike yi to yanzu kika fara don sai an wayi gari watarana kin daina ma jin mamakin wasu abubuwan". "Allah ya kyauta". Na furta a taƙaice ba ta amsa mini ba har sai da na ƙara cewa"don Allah yanzu ƙarfe nawa ne?". "Fitowa na daga ɗaki dai ƙarfe huɗu saura". Na yi zumbur na miƙe ina tada iƙaman sallan asr, har na iddar da sallan tana zaune tana kallona na shafa addu'ar da na yi kana na fuskanto ta. "Don Allah ina neman wani taimako". "Faɗi kanki tsaye, matuƙar zan iya to kin same shi kin huta". "Ina so na zagaya cikin unguwan nan don kafin wa'adin da Aminu ya ɗebar mini na ciyar da ni ya cika. Ina so na tsaya da ƙafafuna ba tare da na bi hanyar da ragowar sauran mutanen gidan nan suka bi ba". "Za ki sha wahala ne kawai don a kaf unguwan ba na tunanin za ki sama aikin da za ki kare mutumcinki da shi. Idan har kin san cewar ba bariki kika fito yi ba me yasa tun farko kika baro gaban iyayenki?". Na ja dogon numfashi na fesar kafin na furta"wannan wani labari ne mai zaman kansa watarana zan ba ki labarina. Yanzu dai ina so na fita don na lura zama bai kama ni ba". "Bari na duba idan Ummanta ta yi bacci sai mu fita na raka ki". Ba ta jira abin da zancen ba ta tashi ta fita da sauri, babu jimawa ta dawo" mu yi sauri mu fita, ta yi bacci na san kuma ba za ta tashi ba wataƙila sai nan da zuwa dare. Don ta shawo ta yi tatil". Na yi sakeke ina kallonta ganin ba ni da niyyan motsawa ya sa ta jan hannuna ta jijjiga ni na dawo cikin hayyacina daga kogin mamakin da na faɗa, ta ɗauki ɗan makullin ta muka fito ta ja ƙofan ɗakin ta rufe da makulin muka fita a zaure muka yi kiciɓus da wasu samari su biyu suna shigowa. Kamar za mu gogi juna da su amma duk da hakan sun ƙi matsawa sai ma ƙara matso mu da suke yi. "Gambo ka ba ni hanya na wuce tun kafin na yi maka rashi mutumci mai wasali". Ya fashe da dariya"to ki yi mana wani dare ne jamage mai gani ba La'aniyatu? Ni fa babu wani nau'in rashin mutumcin da ban ga ni ba, to don kin yi na ki a matsayinki na ƙaramar ƴar bariki ma ai ba zai yi nasarar ɗaɗani da ƙasa ba". Ɗayan ya saki tsaki yana banka mana harara"ni wallahi na rasa abin da ka gani a jikin wannan ƙwailan yarinyar da ka ji ka nace mata. Na rantse da Sarkin dake busan numfashi ko a yau na yi niyyan kwanciya da yarinyar nan babu makawa sai na yi ko da amincewarta ko babu. Bar ganin wai uwarki tana ba ki tsaro da kariya yarinya". "Kanku ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wanka na nake yi". La'aniyatu ta yi zancen cikin matsanancin ɓacin ran tana jan hannuna muak raɓa ta gefensu muka wuce tun da muka fito ba ta ce da ni komai kuma ba mu fasa tafiya ba kamar yadda ba ta sanar da ni inda muka nufa ba. Sai da muka yi nisa kafin na ce"na ga kaman ranki ya ɓaci bisa abin da samarin can suka yi miki ko?". "Kar ki damu zan koya musu hankali ɗaya bayan ɗaya". Na saci kallonta kafin na ce"su waye ne su ɗin? Sannan me yasa suke cin irin wannan alwashin a kanki?". Ta ja dogon numfashi ta fesar sai da ta shafe wasu mintuna ba ta yi magana ba. "Ki yi haƙuri idan abin da na faɗa ya sosa miki rai ko kuma ba ki ji daɗinsa ba". "Kar ki damu babu komai. Ba kowa ba ne su ɗin face irin ƴan iskan garin da suke taruwa a cikin gidanmu, gani suke yi don kasancewata ƴar magajiyar karuwai da ƴan daudu shikenan ni ma ƴar iska ce ba su san cewar baƙar tukunya ta kan iya fitar da farin tuwo ba". Na jinjina kaina alamar gamsuwa da dukkan zantukanta"haka ne kam kin san lamarin mutane sai haƙuri". "Kin gan ni nan tun da na yi wayau na iya bambamce tsakanin launin fari da baƙi daidai da rana guda ban taɓa jin rayuwar da mahaifiyata take yi yana burge ni ba. Tun ina ƙarama na tashi da tsana da ƙyaman irin rayuwar da take yi, tun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98