Chapter 31
Chapter 31
mini ido kawai na ce da ke, na fahimci wani abu guda cewar in dan har ba ka tashi ka nema wa kanka ƴanci ba haka za ka dawwama a cikin ƙasƙanci". Da alama mamaki da al'ajabi ne ya hana ta cewa komai illa kallon da take bi na da shi na sakar mata da murmushi ina miƙe wa tsaye ina ƙoƙarin mayar da hijabina na ce"bari ki ga na yi salla don ina da babban baƙo. Har ya zo ban gama kimtsa wa". Ba ta ce da ni uffan ba har na yi sallan na iddar na shafa dogon addu'ar da na yi, na waigo ina kallonta ta yi jigum da ita kamar majinyaciya. "Ba ki tambaye ni gidan aikina ba?". Ta sauƙe numfashi mai ƙarfi da har sai da na jiyo sautin sa a cikin kunnuwana kafin ta furta"ina kuwa zan iya tambayanki bayan kin gama shayar da ni giyan mamaki. Ba ni labari me ya faru don na ga kin ma dawo da wuri ai". Na fesar da zazzafan iska mai ɗumi daga bakina kafin na juye mata duk abin da ya faru. "To yanzu wani shawara kika yanke barin aikin ke nan za ki yi, ko kuma ya ya za ki yi?". "Da farko na yi tunanin na haƙura da aikin amma tun daga lokacin da Baba Mai gari ya sanar da ni wace ce Altine, da kuma salon nau'in munafurcinta sai na ji na ƙara son aikin a cikin raina, zan shiga cikin Hajiya sosai har sai na fahimtar da ita wace ce Altine na kuma fito da ainihin halinta kowa ya gani. To daga wannan ranar zan bar aikin". "Tabbas kin yi tunani mai kyau". Kafin na ba ta amsa wata budurwa ta shigo cikin ɗakin ta jefo miji baƙin ledar dake hannunta. "Ga shi in ji Hajiya kayan sakawa ne ta ce ki saka su. Don baƙonki yana hanya". Na tsaki wani murmushin da ba shi da haɗi da nishaɗi kafin na ce"to ina godiya saƙo ya iso. Tabbas Hajiya tana ƙoƙarin sangarta ni a cikin gidan nan, har kaya take saya mini". Na ƙare zancen ina bin budurwar da kallo da take ta cika ta na batsewa da tun a tashin farko na fahimci a cikin biyu dole akwai ɗaya. Ko dai baƙon da zai zo musamman domin ni take baƙin ciki da zuwansa ko kuma kayan da Hajiya ta ba ni ne ya baƙanta mata rai. Tsaki ta tsirtar mai dogon zango tare da faɗin"har ina abin yake wai maye ya ci jajiri? Ke kar kin sa ki shiga sahun matan da Hajiya take ji da su a cikin gidan nan? Ko da yake ai an ce na kwance bai ga gari ba". Ta na gama zancen ta juya ta fice na taka ta da dariya da ina da tabbacin hakan ya ƙara ƙular da ita matuƙa. Na ɗaga muryata na ce"a sauƙa lafiya". "Ke Amatullah wai ke ce kuwa?". Furucin La'aniyatu ya sa ni waigo wa ina kallonta. "Me ye kika gani?" "Na ga kin tsiri wasu ɗabi'un da ba na ki ba kin lafawa kanki". "Yanayi ne yake sauya wasu abubuwan La'aniyatu. Wani lokacin mutum ya kan sauya na tare da shi kansa ya fahimci hakan ba". A raunane na yi zancen ina jin ruwan hawaye suna ciko mini kurmin idaniyata. "Bari na bar ki ki shirya". Tana zancen tana miƙe wa ta bar cikin ɗakin a ƙalla na ɓata mintuna talatin zaune a wajen ban motsa ba, kafin na zazzage ledar ina kallon kayan ciki. Doguwar riga ce irin da aka watsa mata duwatsu masu ƙyalla da haske sai kuma mayafinta da ba shi da girma wanda bai zarce girman kallabin da yake kaina ba. Sai kuma turare su kenan a cikin ledar na ɗaga rigar ina kallo tare da sauƙe tagwayen ajiyan numfashi. Na saka rigar na ga ya kama mini jikina sosai har da ƙyar nake numfashi, duk wata surar jikina ta bayyana musamman ƙirjina. Na ɗaura kyallen a kaina na saka hijabina don na ba zan iya fita haka ba, feshi biyu na yi a turaren na ajiye don ya yi ƙarfi da yawa har yana hawa kai. Ɗakin Hajiya Babba na nufa na shaida mata na shirya ta bi ni da wani irin kallo har na zauna. "Wannan hijabin fa?". "Hajiya ba zan iya fita da wannan kayan ba ne, shi yasa na sanya hijabin". Za ta yi magana wayarta ta soma ruri ta ɗaga na ji ta tana ba da umarnin shigowa. Tana ajiye wayar wani mutum ya shigo cikin falon ya sha manyan kaya shadda fara tas mai ɗaukar hankali ya murza hula zanna bukar ga ƙamshin da yake tashi a jikinsa tamkar an yi ɓarin durum ɗin turare a jikinsa. Ya zauna a kujerar da yake kusa da wanda Hajiya take zaune a kansa suka gaisha kafin ya ce"Hajiya Allah ya sa wannan ce wacce aka ajiye min ɗin. Don tun da na shigo na ji ta sama matsuguni a cikin raina". Ta saki shewa"me kake ci na baka na zuba Alhaji Manga? Ai dai duk saurin ungozama za ta jira a haihu". "Fara ba ni amsar tambayata tukunnan ita ce ko ba ita ba ce?". "Ita ce sai aka yi ya ya?". Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe su yana cewa"ba ki taɓa zaɓo min wacce ta dace kamar wannan ba dole na ninka abin da na saba biya sau biyar. Sai dai kuma yanzu akwai meeting ɗin da za mu yi da abokan sana'ata a cikin daren nan. Don haka gobe zan dawo sai na ɗauke ta hakan ya yi?". "Ai duk yadda ka ce haka za a yi ranka ya daɗe, ina godiya". "Da kin gaya min irin wannan surar zan zo na tarar ai da na aika wani ya wakilce ni a wajen meeting ɗin. Amma yanzu ma dai bai ɓaci ba zan dawo ko na aiko a zo a ɗauke ta, yarinya ya ya sunanki?". Muryata a shaƙe na ce"sunana Amatullah". "Amatullah Amatullahi baiwar Allah. Ni kuma sunana Alhaji Manga, yanzu za mu je da ke waje ki karɓo saƙo ki kawo wa Hajiya". Na gyaɗa masa kaina ina satan kallon Hajiya na ga ta ɗage mini gira alamar na bi shi. Suka yi sallama ya fita na bi shi a baya, tun da muka fito daga ɗakin ƴan matan gidan suke ta kai masa gaisuwa yana ɗaga musu hannu. Muka fita waje inda ya ajiye motarsa ya buɗe gidan baya ya ɗauko wasu baƙaƙen ledodi guda biyu ya miƙo mini. "Wannan ta ki ce ɗayar kuma na Hajiya ne sai ki kai mata. Kafin na zo goben ko ban zo ba ma zan yi aike". "Mun gode". Na furta a gajarce. "Ki saki jikinki da yarinya kin ji ko?". Na gyaɗa masa kaina da hakan ya ba shi damar shiga cikin motar ya ja ya tafi. Na sauƙe ɓoyayyar ajiyar zuciya ina bin ledar da ya ba shi da kallo. "Har kin sallame shi kenan?". Na yi figigi na ɗago kaina don gani mamallakin muryar, sai da na firgita don ban yi tsammanin ganinsa a nan kuma a irin wannan lokacin ba. "Saifullah kuma?". Na furta a cikin zuciyata ina jin ƙirjina yana tsananta bugu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98