Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 94

Chapter 94

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kin ga yadda Allah ya yi da mu ko? Aure tsakanina da ke ba zai yiyuwa. Ƙaddara ta shata mana layi a tsakaninmu ta yi mana katanga daga cika burinmu na mallakan juna a matsayin ma'aurata. Sai dai daman kullum a cikin roƙon Allah muke yi ya yi mana zaɓi mafi zama alkhairi a gare mu, tun da hakan ya wanzu a tsakaninmu sai mu ɗauka cewar hakan ne alkhairi a gare mu bakiɗaya da mu da iyayenmu har ma da al'umma". Ya ɗan tsagaita kafin ya ci gaba daga inda ya tsaya"Allah ne shaida cewan na so ki tsananin son da ban taɓa zato ko tunanin zan iya yi wa wata ɗiya mace ba, na yi burin aurenki na yi ɗamarar kasacewa da ke har ƙarshen rayuwa amma Allah bai nufa faruwan hakan ba, ina yi miki fata da addu'ar samun miji na gari wanda ya fi ni komai da komai wanda zai kula da ke ya riƙe ki amana kuma bisa adalci. Idan ki ka sama wanda zai zo ki ya ƙaunace ki domin Allah tabbas zan kasance cikin kwanciyar hankali a duk inda nake, wataƙila wannan shi ne zuwa na a ƙarshe cikin gidan nan da zummar zuwa wajen ki mu yi hirar saurayi da budurwa, sai dai na zo a matsayin wanda ya zo ziyara da kuma sada zumunci". Sai a lokacin hawaye suka zubo daga idanuna sa'ilin da na ga ya miƙe na kuma tabbatar da cewa da gaske tafiyan zan yi, tafiyan da yake daidai da tarwatsewar tubalin ginin da na yi wa rayuwa. "Shi kenan tafiya za ka yi? Shi ke nan komai ya zo ƙarshe a tsakaninmu? Daman haka soyayyar take? Da na san haka ne da ban fara da na san hakan zafin rabuwan yake da ban saki jiki mun saba da kai ba Saif. Sai dai haka Allah ya ƙaddara yadda kake yi mini fatan alkhairi ni ma ina yi maka irin wannan fatan". Sai da na miƙe tsaye na zo gabansa na tsaya mu na kallon juna kana na ci gaba da maganar cikin zubar da hawayen da nake jin sauƙar su a bisa fatan fuskana kamar ana watsa mini garwashin wuta. "Tabbas na shaida cewar kai ɗin mutumin kirki kuma mutumin ƙwarai, ka sama matsayi a cikin zuciyata irin matsayin da babu wani ɗa na mijin da ya taɓa samun irinsa. Saifullah ina sonka amma ƙaddara ta tsara dole mu haƙura da juna". Kukan da ya gama cin ƙarfina ya tursass mini yin shuru ba don na rasa abin faɗa ba. "Wallahi Amatullah da akwai wani hanyar da mu iya yin aure tabbas da zai na bi wannan hanyar, amma dole mu haƙura sa boda maslahan rayuwarmu da kuma ƴaƴan da za mu haifa har ma da kwanciyar hankali iyaye da ƴan uwanmu. Kar mu bari soyayya da burin mallakan junanmu ya rufe mana idanuna har mun jefa rayuwar ƴaƴan da za mu haifa cikin garari, wallahi cutar nan cuta ce mai matuƙar wahala ga kuma ɗawainiyya. Ina sonki wannan dalilin ya sanya ba zan iya jefa rayuwarki cikin ƙuncin ba, Amatullah ba don ba na sonki zan tafi sai don maslahan rayuwarmu kuma ina fatan Anty ma ta fahimci hakan. Allah ya ba ki miji na gari wanda zai ƙauna ce ki domin Allah". Yana dasa aya a nan ya juya ya fice daga cikin falon da kallo na bi shi har ya fita kafin na durƙushe akan gwiwoyina ina wani irin azababben kuka mai ciwo. Har sai da Anty Zulaihatu ta fito ta same ni a wajen ita kuka ni kuka haka muka mayar da gidan tamkar gidan mutuwa, sai bayan sallan magrib Yaya Alhassan da Amir suka dawo Anty Zulaihatu ta shaida musu abin da yake faru, lamarin ya jijjiga su ainun don da aka sanar da su zancen Yaya Alhassan sai da ya nema wajen ya zauna sa boda jirin da yake ɗibansa. Sai da suka yi da gaske kafin suka fahimtar da Anty Sawwama illolin da yake tattare da duk wani aure da aka gina shi akan irin wanan turban, daren ranar mun sha kuka har sai da muka goge wa Allah, Anty Sawwama ta ce tun da haka ya kasance Yaya Alhassan ya ƙira gobe gobe su zo su amshi kayansu da suka kawo. Haka kuwa aka yi aka mayar musu da kayan. Ranar Amira da Mansur suka zo muka wuni muna jajantawa juna lamarin sai bayan sallan magri suka tafi, na shiga damuwa matuƙa mussamman idan na ɗaga wayata ban iske ƙiran Saif sai na ji duk duniyar ta yi mini zafi har na rasa inda zan tsoma kaina na yi salama. Haka zan zagaya na shiga banɗaki na yi kuka na gode wa Allah na wanke fuskana kana na fito. Tun bayan faruwan lamarin ba ma yin dogon magana da Saif sau ɗaya muke yin waya da shi a wuni shi ma da safe ne sai ƙira ni, mu gaisa ya ce daman ya ƙira don ya ji lafiyata shi kenan kuma sai washe gari, Hajiya Muhibbat ma ta ƙira muka jajanta lamarin sosai har da kukanmu shaɓe-shaɓe tamkar waɗanda aka yi wa wani gagarumin rasuwa. Haka aka yi sati biyu da faruwar lamarin lokacin da Allah ya nufa saura sati ɗaya a yi bikin, a daren wani ranan juma'a Anty Sawwama ta tara mu a falo gabaɗayanmu bayan sallan magrib har da mijin Anty Zulaihatu da ya zo ɗaukan ta kasancewar ranar ta wuni a gida. Amir ne ya buɗe taron da addu'a kafin Anty Sawwama ta soma amayar da dalilin da ya sa ta tara mu duka a wajen. "Na tara ku a nan ne gabaɗaya sa boda na sanar da ku hukuncin da na yanke wanda nake tunani da hashashe zai zamo alkhairi gare mu ba ki ɗaya. Amatullah amana ce a gare ni sannan zan ƙara jadadda muku ko bayan raina ku riƙe ta amana ku yi dukkan abin da zai faranta mata rai don neman rahamar Allah kasacewarta marainiya. Ko a iya rashin iyayenta aka tsaya haƙiƙa Amatu ta shiga jarabawar rayuwa balle kuma a haɗa da ragowar jarabawan da ta faɗa a cikin rayuwarta, ina so na yanke hukuncin da nake da yaƙinin cewar ba zai cutar da ɗaya daga cikin mu, ina so lokacin da aka sanya auren Amatullah kar a ɗaga shi". "Auren Amatullah kuma? Ta sama wani mijin ne?". Amir ya yi zancen cikin tsagwaron mamakin da ya bayyana har a cikin furucinsa. Anty Zulaihatu ma ta amshe zancen"Umma aure yanzu kam sai dai mu yi addu'ar Allah ya kawo mata miji na gari". "Ni ma dai haka nake gani, in sha Allah miji ɗaya dai kam Allah ba zai hana ta ba". Yaya Mu'azzam ya sanya baki cikin maganan a karo na farko, Yaya Alhassan k bai iya cewa komai illa ƙasa da ya yi da kansa har zuwa lokacin da Anty Sawwama ta ɗaura da zancen. "Ina so a cikin daren nan a ɗaura auren Alhassan da Amatullah bayan an an iddar da sallan isha'i. Alla ba shi sai ta tare a lokacin da aka sanya bikin watau sati mai zuwa". Ina da yaƙinin duk cikinmu babu wanda ya yi zaton abin da zai fito daga bakin Anty Sawwama

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});