Chapter 78
Chapter 78
gobe mai ƙarar da sabulun wanzami, duk wani dukiyar da Mansur ya tara sai ya zo ƙarshe cikin ƙiftawan ido tamkar ki haɗa auguda ki cilla musu ashana. Nan fa rayuwa ta yi mana tsauri tun muna cin abinci sau uku a rana ko da kuwa babu daɗi muka dawo ci sau ɗaya ma yana neman gagaranmu. Dole ƙanwar naƙi Mansur ya ajiye duk wani girman kansa a gefe ganin yunwa yana neman halaka mu, ga shi tun lokacin da aka kore sa daga wajen aiki sa boda munin abin da ya aikata iyayensa suka yi fushi da shi suka janye masa dukkan tallafi. Yanzu da nake yi miki wannan maganar adaidaita Mansur yake ja don mu rufa wa kanmu asiri, ya yi nadama dana sanin abin da ya yi a baya ya kuma durƙusa a gabana amma duk da haka zuciyata ta ƙi amsar tubansa balle har ta yafe masa irin cutarwan da ya yi mata". Har ta ƙare zancen na gaza motsa wa daga inda nake zaune, tamkar gunki na koma ba na iya yin komai illa kafe da ido da na yi yayin da hawaye suke kwaranya daga cikinsu. Cikin ƙarfin hali na furta kalmar"innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Ta tsuƙe majiyan kukan da ya zo mata kafin ta furta"ki na mamaki ko?". Na gyaɗa mata kaina da hakan ya ba ta damar ci gaba da cewa"to kar ki yi mamaki duk abubuwan da na faɗa miki babu kuskure ko kuma ƙage a cikinsa. Yanzu ma shi ya kawo ni har ƙofar gidan nan kuma shi zai zo ya mayar da ni, wallahi ban ji rasuwar Umma ba sa boda babu waya a hannuna da tun ranar na zo ni, sai yau da na zo Ummata take sanar da ni". Nauyin da ƙirjina ya yi mini ya hana mutane samun damar cewa da ita komai illa jinjina kaina da na ci gaba da yi ina amsa addu'ar neman rahama da take yi wa Umma a cikin zuciyata sa boda bakina ya gaza. Muna nan zaune har aka yi ƙiran sallan zuhur muka fito muka yi alwala muka yi sallan tare da ita muka yi girkin rana muna aikin muna tattaunawa da jajanta lamarin da suka faru, bayan ni ma na kwashe duk irin rayuwar da na yi na sanar da ita ta jinjina lamarin ainun tare da tausayawa a gare ni. Sai da muka gama aikin girkin tsaf na zuba mana namu muka shiga cikin ɗakin, duk yadda ƴaƴan hanjina suke kukan yunwa na kasa kai ko da loma ɗaya na dafa dukan shinkafan cikin bakina illa juya cokalin da nake yi a cikin abincin na kallo ta na ga yadda take cin abincin hannu baka hannu ƙwarya, take na ji hawaye ya ciki mini kurmin idanuna wani irin tausayinsa ya mamaye mini rai da ruhina, tabbas rayuwa abar tsoro ce matuƙa kuma na yarda da wannan karin maganan da ake cewa duniya budurwan wawa ne. "Ban taɓo zato rayuwa za ta zo mana a haka ba Amira. A duk sa'ilin da na rufe idanuna sai na din ga tuno irin rayuwar da muka yi baya sai na ji hawaye suna zuba daga idanuna ba tare da ni kaina na sani ba. Ki duba duk irin soyayyan da ku ka yi da Mansur da yadda yake ba ki kulawa yake kuma tarairayanki kamar ƙwai amma hakan bai hana sa wulaƙanta ki a cikin gidansa ba, hakan bai dakatar da shi daga neman wasu matan ba. Ki dube ni duk yadda nake ƙoƙarin kame kaina da killace mutumcina sai da na yi ciki ba tare da igiyoyin aure sun hau kaina ba, duk yadda nake martaba kaina sai da ƙaddara ta ja ni izuwa can inda ban san kowa ba, na yi zaman kaina a cikin gidan karuwai". Ban ƙarishe zancen ba sa boda kukan da ya kufce mini da ƙarfin gaske, ina yi Amira tana taya ni a haka Anty Sawwama ta zo ta iske mu ta din ga ba mu baki da kuma yi masa nasiha tare da ba musalai kala daban-daban. Wunin ranar tare muka yi shi da Amira sai da muka yi sallan magrib Umar ya shigo ya shaida mana cewar wai ana magana da Amira a waje in ji mijinta. Kafin mu fito daga ɗakin har ya shigo ciki tare da Yaya Alhassan da ya dawo daga masallaci muka iske su a falo suna gaisawa da Anty Sawwama. Idanuna na tsayar ƙar akan fuskar Mansur tabbas kamanninsa bai sauya ki da da ɗan taƙi ba, amma ya lalace ya rame ya yi baƙi ƙirin da shi tamkar wanda ya yi taimama da garin gawayi. "Amatullah ke ce wannan?". Ya jefa mini tamnayar yayin da muke ƙarisowa cikin falon muka zauna, kaina kawai na gyaɗa masa da hakan ya ba shi lasisin ci gaba da maganan. "Na ji matuƙar daɗi da na sama labarin cewan kin dawo gida, Umma kuma lokaci ya yi Allah ya jiƙanta ya sada ta da Mala'ikun rahama ya kyautata makwancinta". "Amin". Duk muka haɗe baki muka amsa da shi, nan ma Anty Sawwama ta ƙara yi musu nasiha sosai don na saurari duk labarin da Amira ya labarta mini, sai ga Mansur har da ƴan guntun hawayensa, tare da su Yaya Alhassan ya tashi suka je masallaci don gabatar da sallan isha'in da ya gabato mu ma muka yi namun sallan, Anty Sawwama ta ce mu zuba musu abinci kafin su dawo, hakan kuwa aka yi muka shirya musu abincin muka ajiye musu a falo yayin da muka koma cikin ɗakin. Muna jin su har suka dawo daga masallacin suka ci abincin suka ɗan taɓa hira kafin Umar ya ɗago labulen ɗakin yana daga tsaye a ƙofar ɗakin ya furta"sun gama ke yake jira". "To ka ce masa gani nan fitowa". Kansa ya gyaɗa tare da juyawa ya fita don iskar da saƙon, muka miƙe ni da ita mu na kallon junanmu tamkar yau muka fara tozali da junanmu. "To Amira sai kuma na zo ni in sha Allah, ki ci gaba da haƙuri akan wanda kika yi sannan ki ci gaba da addu'a Allah ya ƙara shirya sa ya kuma ƙara rufa asiri". Cike da gamsuwa ta ce"wallahi na yi kewar shawarwarinki a gare ni, na tabbatar da ki na a kusa da ni da abubuwa da yawa sun zo min da sauƙi". Murmushi muka sakar wa juna hannunmu riƙe cikin na juna ta yi sallama a Anty Sawwama da ta haɗa mata turaren wuta taf a leda ta bata a matsayin tsaraba. Har ƙofan gida na rako ta muka hango Mansur tsaye a jikin adaidatan tana waya da wata ƙaramar wayar da yake kunnensa ƙiran kamfanin tecno. Yana hango mu ya katse ƙiran ya ɗan faɗaɗa annurin fuskarsa tare da faɗin"Amatullah kun fito ke nan?". Na gyaɗa masa kaina na lura sai wani ƙasa-ƙasa yake yi da kansa kafin na yi magana ya riga ni cewa"wallahi Amatullah kunyar haɗa ido nake yi da ke, tabbas na cutar da ƙawarki na ci amanar yarda da amanar da ta ba ni. Amma duk da hakan ta yi min halaccin da har ƙasa ya rufe idanuna ba zan taɓa manta wa ba, ki taya ni ba ta haƙuri ta yafe
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98