Chapter 43
Chapter 43
ruwan biri da gada. Ina da ikon na kawo duk wani wanda nake so cikin ɗakin nan a duk lokacin da nake so kuma a duk sa'ilin da na ga dama idan buƙatar hakan ta taso". Kalamanta suka ɗura mini takaici a cikin raina na cika na yi fam. "Au! Haka ma za ki ce? Amma kin san da cewa ai ba ke ɗaya ba ce kike da iko da ɗakin. Akwai hakkina da hakan zai tauye mini shin ba ki yi tunanin hakan ba? A lokacin da ƙaramar curin ƙwaƙwalwar kanki take yi miki saƙa da mungun zare". "Su haƙƙin manya. To ke ki na tunanin har wani haƙƙin kike da shi a cikin gidan nan? Ai yanzu kuɗinki shi ne mutumcinki tun da biya nake yi kamar yadda ke ma kike biya don kana ina da lasisin kawo duk wanda nake so". Kalamanta suka sanya zuciyata ƙara tunkura raina ya ci gaba da tafasa na cije leɓena kafin na ce"ai kuwa zan ba ki mamaki, don wannan ƙatoton gardin ba zai kwana a cikin gidan nan ba. Idan suna son ku aikata baɗalarku ku tafi can wani waje ku je ku yi amma ba a cikin ɗakin nan ba". "Ai kuwa kin yi kaɗan ki korar min kwastoma. Ko don ki na baƙin ciki da farin jinina ban kasance irin karfa ba da kare ba ya zuwa cikin ɗakin nan da sunan ya zo wajenta". Ban tanka mata ba na soma waige-waige can na da hango wuƙar da suka yanka kankanan na yi hanzari na je na ɗauke ta. "Ka za fita daga cikin ɗakin nan ko zai na yi maka mummunan lahanin da ko uwar da ta haife ka in ta ganka ba za ta shaida ka ba. Ku je can wani wajen ku haɗu amma cikin ɗakin nan kam sai dai gani sai dai hange". "Ke Amatullah anya ki na da hankali kuwa? Wuƙa ce fa kika ɗauka". Na juya ina nuna ta da wuƙar hannuna"idan kika ƙara ɗaga ƙafarki ki ka yi taku ɗaya sai na ɗaba masa wuƙar nan, ke ma na yi miki rauni sannan daga ƙarshe ni ma na kashe kaina. Dukkanmu mu ukun mu yi asarar rayuwarmu". Cak ta tsaya a inda take ba tare da ta motsa ba ganin yadda na furzar da zancen babu alamar wasa a tattare da ni. Na nufin Saurayin na tan da yake tsaye cike da tsoro yana ta ƙif-ƙifta idanu tamkar shege a yayin rabon gado, yana ja baya ina nufar sa gadan-gadan har sai da ya kai ƙarshen ɗakin. Sha'awanatu ta ɗaura hannu a kanta ta soma kurma ihu da kururuwar neman agaji, kan ka ce kabo mutane suka cika gidan har da Hajiya Babba. "Lafiya Amatullahi me ye yake faruwa?". Hajiya Babba ta jefo mini tambayar yayin da take ƙoƙarin ƙwace wuƙar da yake hannuna, na turje ina faɗin"Hajiya ki bar ni, ki bar ni na koya musu hankali". Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai da ta karɓa wuƙar daga hannuna. "Wai me ye yake faruwa ne?". Hajiya Babba ta ƙara maimaita mana tambayar a karo na biyu, Sha'awanatu ta kwashe komai ta sanar da ita sai da ta gama sauraron ta kafin ta waigo gare ni"duk abin da ya faɗa haka ne?". Ban iya amsa mata da kalmomin da baki kan iya furtawa ba illa gyaɗa kai da na yi alamar e, don cikin abin da ya faru babu wanda Sha'awanatu ta rage ba tare da ta furta ba. "Kai solofiyo zo ka fice daga cikin ɗakin nan". Hajiya Babba ta yi zancen tana saitawa saurayin hanya, cikin rawar jiki ya fice. Haka ta sallame kowa daga cikin ɗakin aka fice ana ta ƙananan suturai da yamaɗiɗi. "Ke Sha'awanatu kin gan ni nan da kike ji da gani duk yadda na yi ƙaurin suna a haɗa gurmi, to ba ba son abin da zai ɗaga min hankali. Ɗakin nan kin san da cewa ba ke ɗaya kike rayuwa a cikinsa don haka duk wani baƙon da za ki yi ko iyakarsa wuni ne babu kwana". "Amma Hajiya ba ki dubi abin da ita ta yi ba sai ni? Shin idan ban kawo kwastomana cikin ɗakina ba ina ake so na kai shi?". Sha'awanatu ta yi zancen cikin ɗaga muryar da ina ta tsbbacin shi ya fusata Hajiya Babba ainun. "Matuƙar ina ƙaunar ci gaba da zama a cikin gidana to ya zama tilas a gare ki ki bi dukkan umarni da sharruɗan da na gindaya miki. Idan kin ga ba za ki iya zama ga ƙofa nan sai ki haɗa kayanki ki san inda dare ya yi miki". Shuru ta yi ba tare da ta ce ko kanzil har Hajiya ta gama zancenta ta waigo gare ni. "Ke kuma zan ja miki kunne a karo na farko kuma wanda zai kasance shi ne na ƙarshe, kar ki ƙara yin gangancin ɗaukar makami a cikin gidan nan". "To". Kawai na amsa mata da shi a taƙaice, ta juya ta bi ta tare da wuƙar da yake hannunta. Kallon-kallo muka yi wa juna ni da Sha'awanatu kafin na wuce zuwa makwancina na kwanta raina a jagule. Ina ta jiran na ji ko za ta kunna sautin da ta yi ikirarin cewar ba ta iya bacci ba tare da ta kunna sa ba, sai na ji shuru kamar Malam ya haɗiye shirya. Na yi ƙwafa ina gyara kwanciyata tare da ƙara tabbatar da cewar wargi ma waje ya samu, kuma maganin biri karen maguzawa. [12/5, 5:07 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ________________________________________ Page 6️⃣2️⃣ Ban iya runtsawa ba har sai da dare ta raba sosai, sai faman juyi nake yi na kasa yin baccin. Gabaɗaya ba na jin daɗin komai raina ya gama ragulewa yayin da zuciyata ta lalace ainun. Ƙwafa na yi ina tashi na zauna duk da kuwa duhun da ya mamaye cikin ɗakin nan sai dai hasken farin wata yana hasko cikin ɗakin daga tagar da yake a buɗe. Karatun alƙur'ani na soma yi tun sautina ba ya fita har sai ya soma fita na ɗau tsawon lokaci ina karatun har sai da na ji wani sanyi ta ratsa sashin ruhina, sai da na yi sallan asubahi kana na kwantar da haƙarƙarina wani bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ni, sosai na yi baccin ban farka ba sai da hantsi ya fito. Ina buɗe idanuna na ga ranar ral ta galle, na yi zumbur ina miƙewa tare da murtsike idanuna don tabbatar da sahihancin abin da nake gani. Tabbas rana ta yi saboda yadda ta galle haske da zafinta ya mamaye ko'ina. Kallabina na za ra na ɗaura akaina na saka hijabina na ɗauki buta na fito na wanke fuska da bakina na mayar da ita cikin ɗaki, kana na fito ina fitowa muka haɗu da Zinariya. Muka sakarwa juna murmushi kafin na ce"ranki shi daɗe kin tashi ke nan? Sai yanzu na ki safiyar ta yi ke nan?". Ta yi miƙa kafin ta ce"wallahi ke dai bari daren jiya ban samu na yi bacci da wuri ba ne, na tsaya yin waya ban yi aune ba har sai da lokaci ya ja kin gan ni nan sai yanzu na sama daman tashi da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98