Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 71

Chapter 71

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gidan nan ba ki aika wani abun ashsha ba, balle kuma wanda Allah ya haramta aikata sa?". Hawaye suna gudun famfalaƙi a bisa kuncina na furta"wallahi Anty ban aika ko ɗaya daga ciki ba, na kiyaye mutunci da kuma kimar kaina". Daga haka na zarce da ba su lamarin duk abin da ya wakana tun daga ranar farko da na sa ƙafata na fita daga cikin gidan har zuwa lokacin da muka yi ido huɗu da Yaya Alhassan da Amir a ɗakin Hajiya, sai dai na ɓoyeH musu haƙiƙanin gaskiyan abin da ya kai ni otel a cikin wannan daren. Haƙiƙa na ga zallan tausayawa kwance a cikin idanunsu yayin da Anty Zulaihatu da Umar suka zubar mini da hawaye tausayi sosai, Amir da Yaya Alhassan kuwa duk jikkunansu ya yi sanyi ƙalau tamkar kazar da aka jefa da ruwan gishiri. Anty Sawwama kuwa baƙinta ya ƙi rufewa sai godiya take ta faman jeranta wa Allah na yi ta ƙara gode masa, tare da addu'ar Allah ya ba ta ikon kulawa da rayuwata daga yanzu har zuwa fitar numfashinta na ƙarshe. "Ga Amatullah nan na ba ku amanarta da ragamar kula da ita duk wani a cikin ku da yake son faranta min, to ya faranta mata. Haka zalika duk wani da yake son ganin ɓacin raina to ya musguna mat yy yh h yh hmy a, ko bayan raina ban yarda ku wulaƙanta ba ko kuma ku bari ta yi kukan maraincin mahaifinta". Jikinmu gabaɗaya ya kuma yin sanyi na kwantar da kaina a bisa cinyar Anty Sawwama ina faɗin"Anty ina Ummata tun da na zo babu wanda ya yi mini maganarta, ina so na je na gan ta ita ma na nema yafiyarta". "Ummanki tana nan Amatullah. Kuma sa boda ita ne ma ya sa muka saya kai da fata wajen ganin mun dawo da ke gida". Babu shiri na ɗago kaina ina kallonta"sa boda ita kuma? Wani abun ne ya faru da ita?". Ganin yadda na birkice ya sanya ta sanyaya muryarta tana faɗin"ki kwantar da hankalinki babu abin da ya faru da ita. Za kuma ki je ki gan ta a yau ba sai gobe ba". Kaina kawai na yi ƙarfin halin gyaɗa mata don jikina ya gama ba ni tabbacin cewa akwai wani abu a ƙasa. Muna yin sallan asubahi ko abincin ban tsaya ci ba muka nufi gidan ni da Anty Zulaihatu har izuwa lokacin ƙirjina bai daina harbawa haka yana dakan lugudan-lugudan tara-tara. Muna sauƙa a ƙofan gidan na ji wasu tulin hawaye sun ciko mini idanuna rayuwata ta baya ya soma dawo mjni cikin kwanyata, yayin da wani haske ya ratsa idanuna tamkar majigin da yake hasko mini jiya ta zuwa yau. Babu abin da na fi tuna illa lokacin zaman makokin Abba yadda aka cika a ƙofar gidan. Sai da ta riƙo hannuna muka shiga cikin gidan yayin da yaran gidan da na maƙwabta suna cika a kaina suka mamaye ni kowa burinsa ya ɗaura hannunsa a jikina don kawai ya tabbatar da cewa ni ɗin ce na dawo ba wata ba. Muna shiga filin tsakar gidan da Umman Amira na fara cin karo ta saki kwanon wainar da yake hannunta ya faɗi ƙasa. "Amatullah ke ce? Jama'a ku fito ku fito ga Amatullahi ta dawo gida. Allah alhamdulillah". Ta yi zancen cikin ɗaga murya yayin da take rugowa da gudu ta zo ta ƙanƙame ni ƙam a jikinta. Kamar an kaɗa ƙararrawa haka ragowar matan gidan suka soma fitowa ƙwansu da ƙwarƙwatansu. "Allah buwayi gagara misali. Amatullah ke ce tsaye a gabanmu? Ko da yake daman masu iya magana ai sun ce giji lahira ce". Maman Adnan da na gan ta da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe a jikinta, kaina kawai na jinjina cikin ƙarfin hali na kallo Umman Amira na ce"ina Ummata take?". Ta yi mini nuni da hanyar ɗakinmu"tana cikin ɗakin". Da gudu na nufi ɗakin ina ƙwalla mata ƙira cikin muryata da ta gama dushashewa sa boda kukan da na ɗauki tsawon lokaci ina yin sa, turus na yi na tsaya lokacin da na yi ido huɗu da ita yashe a falon a bisa kan tabarma na bi ta da kallon tsaf yayin da ƙirjina yake buga wa kamar zai bayyano waje. Daga ita sai zani ɗaurin ƙirji a jikinta sai kuma wani ɗan ƙyallen da ta lulluɓe kanta da shi, ƙafafunta na yi da kallo da wani wari da ɗoyi yake tashi daga gare su, ƙafarta ɗaya na ga an yanke har zuwa gwiwar ƙafar yayin da ɗayar kuma ta kumbura ta yi tsimtim kamar za ta fashe. "Um-um-um-umma ke ce haka me ye ya same ƙafafunki?". Na furta zancen cikin tsintsinkewar zance numfashina yana sama yana ƙasa tamkar ceron da yake bugan sa a cikin turmi. Ta kasa cewa da ni komai illa kallon da ta kafe ni da shi hawaye suna tsiyaya a bisa baƙin fuskarta da ta yi duhun gaske tamkar bayan tukunya, ta ƙanjame kamar mai cutar ƙanjamau duk ta lalace kamar kamun mayu. Na duƙufa a gefenta ina kuka yayin da ita ma take taya ni babu ji babu gani kamar waɗannan aka yi wa mutuwar ƙare dangi. [12/20, 1:48 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________ Page 7️⃣4️⃣ Mun ɗauki lokaci muna kukan daga ni har ita babu mai lallashin wani haka Anty Zulaihatu da Umman Amira suka shigo ciki suka iske mu, yayin da ragowar sauran matan suka tsaya a ƙofar ɗakin ba tare da sun shigo. Sai faman ƙorafin wari da ɗoyin da take tashi daga cikin ɗakin suke yi. "Haƙuri za ki yi Amatullah ai yanzu jikin natan ma da sauƙi sosai, tun da har ta na iya gane wanda yake tsaye a kanta". Muryar Umma Amira ya ratsa cikin ƙoƙon kaina da ya tursasa mini cira kaina ina dubansa bakina yana rawa yayin da haƙwarana suke karafɗiya da juna na furta"yanzu hakan ne jikin da sauƙi? Don Allah ku sanar da ni me ye ne abin da ya same ta har ta koma haka?". "Wallahi wani azzalumin mai mota ne ya buge ta kuma don tsabar tsagwaron rashin mutumci ya yi tafiyarsa ba tare da ko waiwayanta ya yi ba, haka ta zo nan ta yi ta jinyar ƙafar bayan an yi mata ɗaurin gargajiya abin ya ci tura dole aka dangana da asibiti, shi ma ɗin da ƙyar da suɗin goshi ta amince aka je har aka sanar da Gwaggonki Sawwama. Nan Likitoci suka ce wai wani abu shi infection ya riga da ya kama ƙafar dole sai an yanke ta haka kuma aka yi mu na ji muna gani ana yanke ƙafar, bayan wasu kwanakin ɗayan ƙafan ma ya harbu ya soma fitar da wani ruwa mai ɗoyi da wari tare da ƙarni kamar jinin haihuwa. Kin gan ta nan yadda take jaɓe a nan ko ƙofar ɗaki ba ta iya fitowa ba ta iya taimakon kanta da komai, a nan za ta yi fitsari ta sauƙe duk wani buƙatunta babu mai shigo wa ya yi mata sannu balle ya taimaka mata da ko da abin da za ta saka a bakinta ne, tun da ke ma sanin kanki ne ba halin ƙwarai ba ne da ita haka nan

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});