Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

amma dai babu ɗawainiyyar iyali akansa ko?". "Waye ya gaya miki? Yana da matarsa har da ƴaƴa, sai dai ya ce min matar ba wani son ta yake yi ba don auren ma iyayensu maza ne suka haɗa". Na saki ɓoyayyar ajiyar sa bsa yadda zantukan natan suka daki zuciyata tare da mummunan mini raina, na ji wani takaici yana taso mini tabbas in dai har abin da nake zargi ya tabbata to fa haƙiƙa akwai gagarumar matsala. "Aikin me ye shi kuwa yake yi haka da yake iya yin kyautar irin waɗannan maƙudan kuɗin, sannan me ye sunansa?". Kallon da ta tsare ni da shi tun kafin na dire zancen ya sa ni fahimtar na zuga wa kwaɓata ruwa kuma na wuce gona da iri don ina ƙoƙarin wuce makaɗi da rawa. Na ɗage mata ido ɗaya alamar lafiya? Da hakan ya ba ta damar furzar da zancen da yake cikin bakinta. "Wannan tambayoyin hakan wani na bin wani sai ka ce jami'ar ƴan sanda. Kin ga ni nan da kike ji da gani an sha ni na warke wallahi, don an yi min cin amana da zangon ƙasan da ba zan taɓa mantawa ba har zuwa lokacin da zan yi numfashin ƙarshe a rayuwata. A cikin gidan nan aka sama wata tsinananniya ta ɗauki lambar saurayina a cikin wayata ta ƙira shi ma da yake mai bakin uwa ne ya biye mata suka ci amanata, har ta kai ta kawo suna haɗuwa a otel ranar da labari ya iske kunnuwana kuwa na shirya na je ni har otel ɗin na gan su da idona. Sai dai ban yi sakaci na bari sun ganni ba, sai da na saita lokacin da suka saki jikinsu shi da ita wani rana ya zo har cikin gidan nan ɗakinta ba tare da sun san da cewar ina cikin gidan nan. Na dafa ruwan zafi na je na sheƙa musu ita da shi". Tun da ta soma zancen nake bin ta bakinta da kallo har ta kai aya da hakan ya yi daidai sauƙe tagwayen ajiyan zuciyan da na yi ina zame hannayena daga tagumin da na zabga. A taƙaice na ce"to Allah ya rufa asiri". "Amin". Shuru ya ratsa wajen na tsawon wasu mintuna kafin ta kawar da shi ta hanyar faɗin"ba ni da saurin yarda da mutum tun bayar faruwar wannan lamarin, haka nan na ƙudurce a raina ba zan ƙara aminta da wata ɗiya mace ba ko da kuwa cikin ɗaya muke da ita. Sai dai ban san dalili tun ranar farko da na fara ɗaura idanuna akan ki a cikin gidan nan na ji kin kwanta min a cikin rai, na kuma ji a raina cewar zan iya aminta da ke har na ja ki a jikina". Taƙaitaccen murmushi na saka kafin na ce"me yasa kika yi mini wannan shaidar? Ba kya tunanin ni ma idan kika ja ni a jikin idan tafiya ta yi tafiya zan iya cin amanar da kika ɗauka kika ba ni?". Wani shu'umin murmushi ta saka kana ta furta"ban ga alamar hakan a tattare da ke ba Amatullah, domin ido ba mudu ba ne amma ai ya san kima". Kaina kawai na jinjina tare da miƙewa tsaye na ce"bari na je na ɗebo ruwa na yi wanka kafin magriba ta yi".Ta yi caraf ta riƙo hannuna. "Ai dai za ki tsaya na sauƙar da girkin ki ci kafin ki tafi ko?". Na jijjiga kaina"kar ki damu a ƙoshe nake don ban daɗe da cin abinci ba". "Ai ko yanzu kika tashi daga gaban kwanon abinci sai kin cin girkina, don haka kawai ki koma ki zauna idan ruwan wanka ne ki sha kuruminki ina da ruwa a ɗakina sai na ba ki bokati guda". "Kin dai matse ne kawai amma ba na jin yunwa". "E dai na ji koma ki zauna". Ta yi zancen tana jan hannuna na zauna a inda na tashi, mun ɗan taɓa hira da ita kafin abincin ya tahu ta sauƙe ta ce na shirgar da shi ɗakin yayin da ita kuma take kashe ragowar garwashin. Sai da ta gama ta shigo ta zuba mana abincin muka ci tare, ta matsa mini akan sai na ci gaba yadda take ta ja na da hirar da ba na gane kansa balle gindinsa. Haka muka gama abincin na tattaro kwanunkan zan wanke fafur ta hana ni, ta ɗauki ruwa bokati guda ta ba ni na je na yi wanka na yi alwala na fito. Sanda na dawo kawo mata bokatin na iske ta tana waya don haka na ajiye mata na wuce ɗakinmu. Sallan magrib na gabatar na zauna a inda na yi sallan na karato wani sashi daga cikin haddan karatun alƙur'anin da yake kaina. Tunani kala daban daban suka ziyartar kwanyata amma ciki babu wanda ya fi jan hankalina tare da rikitar da ni sama da hoton Abbinsu Aryan da na gani a fuskar wayar Zinariya da kuma kalaman da ta yi mini. Tabbas indai ba idanuna ba ne suka gano mini abin da ba shi ne ba ko kuma suka sama matsala gabaɗaya Abbinsu su Ayan mijin Hajiya Muhibbat ɗin dai na gani. Sai dai me ye haɗin sa da Zinariya kuma a ina suka haɗu da shi? Idan ban manta ba na taɓa jin Hajiya tana cewar mijinta ba mazauni ba da yake shafe tsawon lokacin ba tare da ya zo gida ba. Ta gyara zamana ina ƙara yin zurfi cikin tunanin da nake yi tare da yin nisan kiwo cikin nazarin. Ta ina da zan fara wannan yaƙin balle har na ci galaba? Akwai tarin abubuwa a gabana da nake son cimma a cikin rayuwata, haƙiƙa sai yanzu na yarda da karatun da Amira take bi ya know na cewar dukkan maza halin su guda ne wanda hakan yake nufin ko wani gauta ja ne sai dai wanda bai ji rana ba. Na tashi na gabatar da sallan isha'i na zo na yi shirin kwanciya sai dai baccin ya ƙi zuwa haka na yi ta juye-juye har izuwa lokacin da bacci ya yi nasarar sace ni. Kamar a mafarki na ji soma jin tashin sautin yana tashi daga cikin ɗakin, wanda hakan ya tilasta mini buɗe idanuna tare da sauƙe su akan Sha'awanatu da muke ɗaki ɗaya da ita. Zaune take akan katifarta tare da wani saurayi suna manne da junan tamkar za su haɗiye junansu, kankana ne a gabansu yana yanka da wuƙa yana ba ta a bakinta yayin da take wani lumshe idanuna tare da gantsarewa. Tsam na tashi tsaye ina rarumo hijabina na mayar da shi jikina da hakan ya sanya hankalinsu karkaro wa gare ni, Shaawanatu ta buga wani uban tsaki tare da kawar da kanta gefe. "Wane ne wannan Sha'awanatu kika shigo mana da shi har cikin ɗaki?". Kamar wacce take jira na ce kule ta ce as, ai kuwa ta miƙe ita ma tana mayar mini da martani a zafafe"amma dai ai kin san da cewar ina da cikakken iko a cikin ɗakin nan, tun da kuɗi nake biya na kaya ba kyauta nake zaune ba kuma ba alfarma aka yi min ba. Yadda kike zaman kanki haka ni ma nake zaman kaina babu ruwa wani da wani kamar yadda babu

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});