Chapter 77
Chapter 77
ta kafin na ce"Amira ke ce?". "Ni ce Amatullah". Ban san lokacin da na ji wani ƙarfi da kuzari ya mamaye jikina ba, taku uku na yi na iso gabanta muka rumgume juna ni da ita, muna kukan da takamanmen ba za mu iya bambamcewa tsakanin kukan farin ciki ne ko na akasin sa ba. [12/22, 3:46 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam __________________________________ Page 7️⃣6️⃣ Mun ɗauki tsawon lokaci muna kukan kafin na ja hannunta muka isa bakin katifan muka zauna muna fuskantar juna, yayin da muke ta ƙarewa junanmu kallo. Tabbas wannan Amiran da take zaune a gaba yanzu ta sha bambam da ainihin Amiran da na sani a lokutan baya. Wacce na sa ni ƴar gayu ce na buga wa a jaridar Aminiya, saɓanin wannan da take zaune a gabana cikin suturun ba su rufe mata kattara ba. Wacce da na sani ma'abociyar ta'ammali ce da kayan gyaran jiki da ƙamshi ne saɓanin wannan da babu wannan abubuwan a tattare da ita. Wancan da na sani fatarta kullum cikin gyara da ƙyalle yake yi saɓanin wannan da ta yi duhun gaske. Na kasa jurewa har sai da na furzar da mamakina na ce da ita"Amira yanzu ke ce haka? Me yake faruwa ne? Don rasuwar Umma ban gan ki ba kuma ban sama nutsuwar da zan tambaya inda kike ba". Numfashi mai dogon zango ta saka kafin ta furta mini dunƙulalliyan maganan da na kasa fahimtar inda ta dosa. "Amatullah rayuwar ce ta yi min atishawan tsakin barkono, tabbas na fahimci idan ka san farko to ka kiyayi ƙarshe". Na ɗan waro idanuna waje kafin na ce"me yake faruwa ne Amira? Shin ina Mansur? Ina alƙawarin da kuka yi wa junanku?". Wani murmushin takaici ta saka kana ta furta"Mansur yana nan mun yi aure da shi, yanzu haka maganar da nake yi miki ni da shi miji da mata ne". Na rarumo hannunta na riƙe gam cikin son gaskata abin da ta faɗa. "Don Allah Amira wannan zancen da gaske ki ke yi, kun yi aure da Mansur? To a ina kuke zaune kuma me yasa na gan ki cikin wannan yanayin?". Sai da ta ja numfashi mai dogon zango kana ta ce"Amatullah za ki yi mamaki idan na shaida miki cewar yadda Mansur ya bayyana kansa a gare ni ba haka yake a zahiri ba, ya nuna min soyayya a zahiri alhalin a baɗili ba hakan ba ne a cikin ransa. Bayan barinki gida sau uku yana ƙoƙarin keta min haddina Allah ya na kuɓutar da ni, lokacin da iyayensa suka zo gidanmu aka sanya ranar aure sai ya mayar da ni tamkar matarsa ba ya shayi ko shakkan taɓa ko wani gaɓa a cikin jikina. Ya lalata min rayuwata yayin da hankalina ya gushe da tunanin tun da aure na zai yi hakan ba matsala ba ne, ban sa ni ba ashe wuƙa na ɗauka na burmawa cikina. Idanuna sun gama rufe burin auren mai kuɗi kuma ɗan soyayya kawai nake hangowa. Haka aka yi bikin ya yi da ya yi min ɓarin Naira kamar bai san zafin nemansu. Ya ɗanɗasa min gida na gani na faɗa komai na cikin gidan shi ya yi da ƙudinsa daga ni sai kayan jikina aka kai ni cikin gidan. Ban cika satikai biyu masu kyau a cikin gidan ba na fahimci na yi zaɓen tumun dare don na gani Mansur ƙwararren manemin mata, har daga wasu jihohin ake yi masa dillancinsu. A lokacin hankalina ya tashi matuƙa babu kalar bazaranar da ban yi masa ba amma ya murzawa idanunsa toka daga ƙarshe ma ya ba ni zaɓi ko in kwantar da hankalina na zauna na ci azurki na bar azurki a inda na same shi, ko kuma ya sauwaƙe min ungulu ta koma gidanta na tsamiya". Ta tsagaita ta hanyar jan dogon numfashi ta fesar da shi daga bakinta kafin ta ɗaura daga inda ta yi birki"dole na ba da kai bori ya hau don ba zan iya rabuwa da shi, bayan soyayyan da nake yi masa hakan ina gudun dariyan da magauta za su yi mana ni da Umma idan aka ji cewar Mansur ya sake ni tun kafin na rufa wata guda a cikin gidansa. Haka na yi haƙuri na shanye dukkan baƙin ciki da takaicin Mansur a lokacin ko zanen lallen da aka yi min na bikin bai gama goge daga hannaye da ƙafafuna ba. Tun ina kuka da shiga damuwa har na saki raina na sa ba don har akan gadonmu na sunna yana waya da ƴan matansa, idan na ce zan tayar da hankali sai na ga ba ni ma da wani dalilin yin hakan tun da bai rage ni da komai ba. Bai hana ni ci ba balle sha haka nan sutura sai wanda na zaɓa zan saka a jikina. Ko da na sanar da Ummata sai ta ƙara ƙarfafa min gwiwa akan na zauna da mijina a cikin dukkan yanayin da na tsince shi, ta ƙara da cewar mazan wannan zamanin daman duk haka suke ko sun yi aure ba za iya rabuwa da ƴan matan da suke mu'amala da su, na yi matuƙar juriyan zaman da shi don a wasu lokutan har cikin ɗakina yake kawo mace sun yi duk abin da ransu yake so ba tare da na iya cewa da shi uffan ba har sai da ya kai jallin da na ji gabaɗaya auren ya fice min daga cikin raina. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya duk halin ƙuncin da zan shiga ba ya ɗaɗa Ummata da ƙasa in dai har zan kawo mata ƴan sulalla to baka lafiya ciki lafiya, shuru za ki ji tamkar Malam ya haɗiye shuruwa. Rana tsaka Mansur ya soma jinya tamkar ba zai yi rai ba ko da aka je asibiti aka tabbatar da cewar yana ɗauke da cuta mai karya garkuwan jiki, da aka gwada ni ma aka same ni da cutar a tattare da ni sai dai nawa bai yi ƙarfi tamkar na sa ba. Ina da yaƙinin cutar ba ta yi min illa kamar yadda tunani da halin ƙunci da kukan da na shiga ya yi min illa ba, lokaci guda na rame na fige na fita daga cikin hayyacina. Ko da na buƙaci ya sake don ba zan iya zama da shi ba Umma ta lashi taboki akan in har na kashe auren to babu ni babu ita kuma daga ranar na dai amsa sunan ɗiyar da ta haifa, haka na rumgumi haƙuri ya zama min abokin rayuwa, aka ce gani da wane ya isa wane tsoron Allah sai dai wanna karin maganar ba ta yi tasirin akan Mansur ba bayan faruwa waɗannan abubuwan aka kama shi da wata a wajen aikinsu yana lalata da ita, take aka rubuta takardan kora ya dawo gida ya zauna babu aikin fari balle na baƙi". Daga haka ta fashe da wani gigitaccen kukan da na ji sautinsa yana ratsa wa har cikin ƙoƙon kaina, na kasa yin komai balle har na sama ƙarfin gwiwan lallashinta na haɗa mata da kalaman ban haƙuri. Haka ta yi ta gaji don kanta ta tsagaita tare da ɗorawa da faɗin"kin san an ce zara ba ya barin dami kuma yau da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98