Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 40

Chapter 40

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na kawo ƙarshen muhawarar ta hanyan ɗauko musu wani kayan. Farin riga t-shirt na saka musu mai gajeren hannu gaban rigar an yi rubutu da jan kala, na saka musu wandon jeans da tsayinsa ya tsaya daidai gwiwansu. Na gyara musu sumar kansu ya sha musu mai tare da taje musu shi, ya yi kyau tare da ƙara yin sheƙi gami da ƙyalle, sosai kayan ya amshi jikinsu da hakan ya taimaka wajen fito da ainihin sihirtaccen kyawunsu. Na lura su ma kansu sun san cewar kayan ya yi musu kyau don gaban madubi suka tsaya suna kallon kansu suna dariya. Na zo na tsaya a bayansu Aryan ya yi wuf ya ce"Anti ni da shi waye ya fi wani kyau? Ai na fi shi kyau ko?". "Ƙarya ne ai Uncle Saif ma ya ce ni ne wanda ya fi kama da shi". Ayan ya mayar masa da martani cikin gaggawa, duk suka juyo gare ni suna rige-rigen yin magana. "Waye ya fi kama da Uncle Saif a cikinmu Anti?". Aryan ya koma jefo mini tambayar a karo na biyu, kafin na amsa masa Ayan ya amshe zancen cikin faɗin"ai ni Ummi ta ce da Abbinmu nake kama". "To ni ai yanzu ban san Abbin nakun ba haka shi ma Uncle Saif ɗin ban san shi sosai, ina dai ganin sa ne kawai. Kun ga kenan ba zan iya bambamce da waye suke kama ba a cikinsu". Ina rufe bakina Aryan ya juya ya je ya ɗauko mini wani hoton da yake ajiye akan dirowar dake gefen gadon baccinsu ya kawo mini. "To kin ga wannan shi ne Abbin namun". Ya yi zancen yana miƙo mini hoton na karɓa tare da zuba idanu, hoton Hajiya ce zaune ta sha wani uban leshi launin hoda da ya amshi jikinta kuma ya hau da zubin jikinta, an yi mata kwalliya a fuskarta da ta zauna a fuskar ta yi ɗas da ita tamkar da shi aka halicce ta. Wuya da kunnenta har da hannayenta sun sha ado sarƙa, ɗan kunne da kuma awarwaro. Gefenta na hagu Ayan ne zaune yayin da gefenta na dama Aryan yake zaune. Wani mutum ne fari sol tsaye a bayansu ya ɗan ranƙwafo ya dafo kadaɗun Hajiya da hannunsa guda ɗaya yayin da ɗayan hannun ya ɗaura akan Aryan, dukkansu fuskokinsu washe da maɗaukakin annuri da ya gauraye da nishaɗi, sai dai na lura hoton kaman tsoho ne don a hoton su Aryan ba za su wuce shekaru ɗaya da wasu watanni da haihuwa ba. Sai da na saka ido sosai na gano Aryan da Ayan sam ba sa kama da mahaifinsu, duk kamannin mahaifiyarsu Hajiya Muhibbat suka kwaso kwabo da kwabo babu abin da suka bar mata, sai dai hasken ubansu da suka ɗauko. Ban yi aune ba na ji an fizge hoton tamkar za haɗa da hannuna, babu shiri na ɗago kai don ganin wanda ya aikata hakan a gare ni, idanuna suka sauƙa akan fuskar Altine ta take tsaye tana ta cika ta batse wa. Me ye kike yi a cikin ɗakin nan sannan me ye wannan hoton yake yi a hannunki?". Ba ta jira na ba ta amsa ba ta ci gaba da balbalin wutar ba'lain da take yi tamkar za ta yi aron baki. "Watau kin ɗauko hoto kin sa a gaba ki na ta kallo, kin zuba wa mijin mata idanuna kamar mayya kin shagala da kallonsa har ma ba ki san sa'ilin da na shigo cikin ɗakin ba balle tsayuwar da na yi a kanki. Irin ku ne wanda ake ɗaukowa daga rana a shigo da ku cikin inuwa daga ƙarshe ku ku tura mutum cikin ranar, daman ni tun ranar farko da na gan ki nake kokonto a game da ke. Tukunnan ma me ye dalilin da ya kawo ki cikin ɗakin nan?". Murmushi kawai na yi tare da miƙe wa tsaye, na kai duba na ga su Aryan da suke tsaye da na lura jikinsu gabaɗaya ya yi sanyi ƙalau har sun kasa motsawa daga inda suke. Sai da na yi dogon tunanin kafin na ce"daman an iyakance mini inda zan shiga ne a cikin gidan ban sa ni ba?". "Tambaya kike yi ko kuma neman sani?". "Duk wanda kika ɗauka a ciki daidai ne ranki ya daɗe". Na yi zancen ina ɗage kafaɗana alamar babu abin da ya sha mini kai ko ya ɗaɗa ni da ƙasa. Na sa kai zan fice daga cikin ɗakin ta jawo gefen hijabina har sai da na yi tangal-tangal zan faɗi Allah ya kiyaye. "Ke har kin isa ina miki magana za ki tashi ki tafi ki bar ni? Wace ce ke kuma da me ye kike taƙama, sannan wa ye ya tsaya miki a cikin gidan da har kike jin cewar za ki iya yin duk abin da kika ga dama?". Duk da abin da ta yi mini ya yi mini matuƙar ciwo tare da tusa mini takaici amma ban nuna mata ba ko a fuska, maimakon hakan ma murmushi na sakar mata ina tsayar da idanuna ƙar a kanta. "Ni ba kowa ba ce a cikin gidan nan face ƴar aiki kamar ki, wacce ta fito aiki domin rufa wa kanta asiri da kuma samun abin da za ta ɗauki nauyin buƙatun rayuwarta". Ina dire zancen na juya na yi ficewa ta ina jin wani gigitaccen tsawan da ta dokawa su Aryan yayin da nake fice wa daga cikin ɗakin ko kanzil ban juyo na ce da ita ba. Kai tsaye ɗakin Altine na nufa wanda kai tsaye zan iya ƙiran da ɗakinmu na shiga banɗaki na ɗauro alwala na zo na gabatar da sallan zuhur, na ɗaga hannayena sama ina jero kirari ga Ubangiji kana na shafa doguwar addu'ar da na yi wanda dukkaninta addu'ar neman rahama da gafara ne ga Abba. Wanda babu ranar da za ta fito ta faɗi ba tare da na yi tunanin sa ba ko kuma ya faɗo mini a cikin raina ba. Hoton da na ɗauko a sashin Saif na tsince ɗaga gefen hijabina da na ƙulle na zura wa hoton idanuna yayin da wasu tambayoyi masu rikitarwa suke yi mini yawo a cikin kwanyata. Tabbas akwai buƙatar na nemo wata iriyar alaƙa ce tsakanin Muhammad Taufik da kuma Sheikh Dawood ko kuma na ce baƙin Balarabe kamar yadda na laƙanci haka daga wajen Baba Mai gadi. Numfashi mai nauyi na ja na fesar daga cikin baki sa boda tunawa da na yi da Amira, babu wanda yake saurin gane ina cikin damuwa ko da kuwa ban furta ba sama da ita, babu abin da ta ƙi jini a rayuwarta kamar ta ganni cikin ƙunci. Mun shaƙu da ita sosai ta yarda ba na shakkan sanar da ita dukkan sirrina domin ba ni da kaufi akan ta, ina jin ta tamkar ƴar uwar da muka rayu a mahaifa guda da ita kana muna fito duniya a tare kuma a lokacin ɗaya. Na san ta yi nemana har ta gaji ta sadadu ta fawwalawa Allah komai, ko har yanzu suna tare da Mansur ko kuma ƙaddara ta raba su, wataƙila izuwa wannan lokacin sun mallakin junansu sun cika burinsu na zama miji da mata oho? Ɓoyayyan ajiyan zuciya na sauƙe ina zame wa

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});