Chapter 66
Chapter 66
tashe ni na yi salla bayan na iddar ta zo ta zauna da inda nake zaune. "Yanzu me ya tsarinmu na gaba? A tunanin a waye ya dace mu turawa wannan sautin muryar da kuma hotunan nan?". Na ja dogon numfashi mai nauyi da sauti na fesar kafin na sama lasisin faɗin"tunanin da ni ma nake yi ke nan, amma zuciyata ta fi aminta da cewar mu nema lambar Muhammad Taufik mu tura masa sautin muryar. Hotunan kuma mu goge su tun da daman sa boda mu gamsar da Hajiya muka yi su". Ina rufe bakina Aminu ya ɗago labulen ɗakin ya shigo ya zauna duk muka bi shi da kallo. "Ga can baƙinki fa sun iso, su na falon Hajiya su na jiranki". "Wai daman da gaske ne an zo nema na? Ni kuwa waye na sane da zai taso takanas ya zo cikin gidan nemana?". Ya ɗage mini kafaɗarsa alamar shi ma ba shi da masaniya akan hakan. "Ke kuwa ki tashi mana ki je ki ga su wane ne. Tun da an ce gani ya kori ji". Zinariya ta yi zancen da ya kama hankalina, ba cire hijabina da yake kaina da na yi sallan da shi ba na tashi na nufi ɗakin Hajiya Babba. Na bi takalaman maza da suke ƙofar ɗakin kafin na shiga ciki. "Hajiya ga ni". Na furta ina daga tsaye tare da tsayar da ƙwayoyin idanuna akan ta. Ta taɓe baki"ba ni nake nemanki ba. Baƙinki ne ga su can". Ta ƙare zancen tana yi muni nuni da samari biyu da suke zaune a cikin falon da sai a lokacin idanuna suka kai kansu. Take numfashina ya ɗauke na wuce gadi sakamako tozali da na yi da mutanen da ba na tunanin sake ganin su a nan kusa a cikin rayuwata. Jikina ya na rawa tamkar mazari na nuna su da ƴar manuniyar ƴatsata. "Yaya Alhassan da Amir ku ne?". Na yi zancen cikin rawar jiki da na murya, duk su biyun suka tashi tsaye muna kallon juna. Yaya Alhassan ya ce"Amatullah ke ce kika dawo haka? Ke ce kike rayuwa a cikin gidan nan". A raunane ya ƙarishe zancen kamar zai yi ƙwalla. Na ji kaina ya soma juya idanuna suna hango mini abin da yake gabana bibiyu, ƙafafuna suka soma karkarwa na yi lu na faɗi a wajen babu wani gaɓar da take motsa wa a cikin gangar jikina. [12/18, 3:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 7️⃣2️⃣ Tun daga lokacin ban ƙara sanin takamanmen inda kaina yake ba, ban ƙara fahimtar komai ba haka nan idanuna ba su ƙara gano mini wani haske ba face gilmawar duhu baƙi ƙiri da babu alama ko ɗigon haske a cikinsa. Ban san iya adadin awannin da mintunan da na ƙarar ba na cikin hayyacina ba sai buɗe idanuna da suka yi mini nauyin gaske na yi na ganni kwance a cikin wani ɗaki wanda na ƙare wa kallo tsaf na kuma fahimci cewar ɗakin asibiti ne, kamar yadda na ga robar ƙarin ruwa a maƙale a hannuna na yi yunƙurin tashi sai dai kash! Gangar jikina ya ƙi ba ni haɗin kai wajen aiwatar da hakan a aikatace. Ban san sa'ilin da ruwan hawaye masu ɗumi suka soma rige-rigen fita daga koramar idanuna ba sai jin ɗumin sauƙarsu na yi a bisa fatar fuskana. Abubuwan da suka wakana kafin na tsinci kaina cikin wannan yanayin da nake ciki ya soma dawowa cikin kwanyanta tiryan-tiryan, na cije leɓan bakina ina jin zuciyata tana buga wa ɓat-ɓat tamkar allon ƙirjina zai dare zuwa gida biyu. Wahalallen numfashi na ja a karo na barkatai na fesar daga bakina yayin da na kai hannu na fincike ƙarin ruwan da aka maƙala mini a hannu. Na tashi na zauna da ƙyar yayin da nake jin kaina ya na sarawa tamkar zai faɗo ƙasa. Ban yi aune ba na ji hawayen da suke zuba daga idanuna sun ƙara ƙarfin gudu ta yadda suke wanke mini fuskata babu ƙauƙautawa. A bayyane na furta"Yaya Alhassan me yasa kuka bayanna a cikin rayuwa a daidai wannan lokacin? Lokacin da nake dab da cika buri da muradin raina burin da ya daɗe a cikin farfajiyar ƙirjina. Ba zan iya haɗa ido da ku idan lokacin da ya dace na koma gare ku ya yi tabbas ni da kaina zan kai kaina inda kuke amma ba yanzu ba". Ina gama zancen na diro daga kan gadon na ɗauki hijabina da yake gefe na mayar da shi kaina na fice daga cikin ɗakin, ina ta faman dube-dube da waige-waige, Allah ya tarfawa garina nono har na fita daga cikin ɗakin ban ga ɗaga cikin waɗanda nake guje musu ba. Daidai na iso ƙofar da zai sada ni da harabar cikin asibitin na ji na yi karo da mutum har sai da na yi tangal-tangal zan faɗi aka riƙo hannuna na tsaya cak akan ƙafafuna, na dafe ƙirjina sa boda tsananin tsoron da na ji yayin da nake cira kai don ganin wanda ya kawo mini agaji. Idanuna suka gauraye cikin na Yaya Alhassan da yake tsaye a wajen ya kafe ni da idanu kamar yadda ni ma na kafe sa da na wa idanun, da har suka ƙanƙace sa boda azababben kukan da na yi a cikin ɗakin bakin na fito. Shi ya fara janye idanunsa daga kaina yana riƙe ƙugunsa da hannu ɗaya yayin da hannu ɗayan yake riƙe da wani ledan baƙa. Cike da takaici ya soma faɗin"ina kika fito za ki je bayan ke da ba ki da lafiya har an kwantar da ke a gadon asibiti?". Bai jira na ba shi amsa ba ya ci gaba da faɗin"guduwa kika fito za ki yi ko?". Ya jinjina kansa kafin ya zarce da faɗin"Amatullah me yasa lalle kike son ki ga kin butulcewa ni'ima da ilhaman da Allah Ubangiji ya yi miki ne? Me yasa kike ta ƙoƙarin watsa ƙasa a idanun mutanen da suka ɗaura yarda da amimcinsu kacokam akan ki? Allah ya rufa miki asiri amma ki na ta ƙoƙarin tona wa kanki asiri ga idon duniya, wai ina hankali da tunaninki suka yi ƙaura suka tare ne? Ina wannan ilmin nakin da sanin ya kamata da kowa yake yabanki da shi?. Idan kin zaɓa ki guje mana a wannan karon kam ba zan yi ƙoƙarin dakatar da ke ba, tun da ba ki duba wahala da tudu da gangaran da muka bi kafin har muka gano inda kike rayuwa muka zo domin tsamo ki daga halaka ba, idan a baya mun yi miki uzuri akan duk abin da kika aikata tare da danganta hakan da cewar damuwar da kika tsinci kanki, zafin mutuwar mahaifinki da kuma raɗaɗin kalaman da mahaifiyarki ta furta a gare ki su suka haɗu suka yi taron dangi wajen ingiza zuciyarki har kika aikata abin da kika aikata. Wallahi a yanzu idan kika ƙara gangancin ƙara aikata wani kuskure babu wanda zai yi miki uzuri. Amatullah ba mu zo don mu tursasa ki ba amma tun da har yanzu zuciyarki ta na kitsa miki ki sanya ƙafa ki guje mana ba za mu yi miki tilas ba rayuwarki ce ki na da dama da ikon ki yi duk yadda kike
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98