Chapter 58
Chapter 58
Washe gari da ƙyar na tashi sa boda daren jiya ban iya runtsawa da wuri, a makare na gabatar da sallan asubahi na zauna inda na yi sallan na yi shuru ina tunanin ta yadda ta fara gudanar da rayuwata a wannan gaɓar, sai dai kamar yadda Zinariya ta faɗa ne dole na tashi na yi yaƙin nema wa kaina ƴancin kai. Haka kuwa haka ba ta cika sati guda da tafiya ba sai da na zama babu wanda bai sanni ba a kaf cikin gidan, hatta baƙin da suke zuwa san sunana ko da kuwa ba su taɓa ganin fuskata ba. Na yi ƙaurin suna fiye da tunanin mai tunani ta yadda duk wani rashin mutunci da tijara na san farillai da sunnoninsu, har na kai munzalin da babu wanda yake rayuwa a cikin gidan da za a ƙira sunana ba tare da ya sha jinin jikinsa. Babu wanda ya isa ya nuna mini ɗan ƴatsa rashin mutuncin da nake yi ina sa yaƙinin ko Zinariya ce ta dawo ba za ta yi rabinsa. Faɗa da jagwal babu wanda ba na shiga, rigima kuwa ko ba da ni ake yi ba zan shiga na amshe balle kuma da ni ake yi. Yo wani ma ya yi rawa balle ɗan makiɗi. Duk tijara da kwashe-kwashen Aminu sai da ya zubar da makamansa ya duƙa a gabana ya sara mini. Har na kai lokacin da duk sa'ilin da aka kawo wata sabuwar yarinyar cikin gida waje na ake fara kawo ta na yi mata darasi. Sai dai duk barikin da nake bugawa babu wani na mijin da nake sake wa fuska balle na ba shi gangar jikina, haka nan duk shagalata ba na wasa da addini ko kaɗan du abin nake yi kuma a duk inda nake da na ji an yi ƙiran sallan zan bar abin da nake yi salla, haka nan azumin Litinin da alhamis ba ya taɓa wuce ni. Hakan nan ba a yin cikakkun kwanaki goma sha biyar ba tare da na sauƙe alƙur'ani ba, sadaka kuwa sai dai in ban sama taro da sisi ba. Wasa-wasa sai da Zinariya ta ci satikai biyar cur ba ta dawo ba, tun abin ba ya damu na har ya soma damuna. A duk lokacin da zan ce Aminu ya ƙira mini layinta a kashe yake lamarin ya yi matuƙar ɗaga mini hankali da jefa ni cikin cakwakiyar tunanin an ya kuwa lafiya?. [12/14, 12:30 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ___________________________________________ Page 6️⃣9️⃣ Haka nake kwana na tashi da tunanin halin da Zinariya take ciki, tabbas da na san garin Abuja ko kuma na taɓa zuwa cikinsa babu abin da zai hana ni tashi takanas na je neman Zinariya. Sai dai na ji an ce mini babban gari da ya tara manya da hamshaƙan mutane neman mutum a cikin irin wannan garin ba ƙaramin aiki ba ne. Ina ƙwance a ɗaki ina ta saƙa da warwara a cikin raina yayin da wani sashin zuciyata yake hasko mini rayuwarta ta baya mussamman yadda muka rayu da Abba, ta tabbata a gare ni ba ni da wani masoyin da ya wuce shi haka nan babu wani wanda zai nuna mini ƙauna kwatankwacin irin wanda ya gwada mini. Murmushi kawai na yi ina jinjina kaina don izuwa yanzu a zo bijiren da zuciyata ta bushe ta zama tamkar dutse wajen dake wa, babu abin da yake sani fargaba balle tsoro ko kuma tausayi haka nan hawaye ba za zuba daga idanuna. Maimaikon lokacin da suka shuɗe da ba na sanin sa'ilin da suke cin gashin kansu. Babu shiri na tashi daga kwanciyar da na yi sa boda hayaniyar da na ji yana tashi a tsakar gidan ana ta ruwan shariya tamkar dangin maguzawa. Diro wa na yi daga kan katifar Zinariya da nake kwance na bayyano waje. "To ƴaƴan kaji dangin karnuka wani gurmin kuma aka haɗo da sanyin safiyar nan?". Na yi zancen yayin da nake iso wa inda na ga su a tsaye cirko-cirko tamkar sun haɗiyi taɓarma. "Wai don tsabar iskanci da rainin wayon mutanen cikin gidan nan, na ɗaura girki daga na fito na shiga banɗaki na dawo na samu an sace tukunyar gabaɗaya, sa boda rashin ta kunya da tsiya. Wallahi a fito mini Sabuwar yarinyar da aka kawo da na bi ya mata littafin sirrin zaman bariki babi-babi, kuma aka yi karati yarinyar kanta yana ɗauka uwa uba kuma a wayenta ta shigo harkar. "Ke Kyawawa shi ne kika hargitsa gidan haka da sassafen nan? Ko da yake ban ga laifinki ba a ɗauke tukunya sukutum ai dole ki tada jijiyoyin wuya. Yarinya ci gaba da masifa har sai an fito miki da kayanki ai bala'i da masifa babu uwar wacce ta kashe". Ina rufe bakina Aminu da shigowar sa ke nan ya amshe zancen"ina gaida uwar haɗa gurmi, yarinyar nan kin san kan tsiya kuma kin san wassulanta. Kin san har yanzu kaina ya ƙasa yarda cewar ki na da haddar alƙur'ani a cikin wannan kan nakin". Na saki shewa har da tafa hannu kana na ce"ai kuwa ya kamata ka yarda don yadda nake murza wulaƙanci na tofar. Haka nake sarrafa ayoyin cin alƙur'ani yayin rera su". Ya kwashe da dariya mai sauti"Mahaddaciya ga sani ga ilmi kuma ga shagala". Ban ce da shi komai illa murmushin da na sakar masa yayin da nake juya wa na koma cikin ɗakin. Na zauna na yi shuru tunanai kala-kala suna ziyartar cikin kwanyanta, tun da na sa ka ƙafata na fito daga cikin gidanmu daidai da rana guda ban taɓa jin ina son na ƙara kallon fuskar Umma ba balle har na yi kewarta ko na ji sha'awar son kasancewa a tare da ita, kamar yadda nake ji a cikin ƴan kwanakin. Wani tsananin kewarta da son ganinta nake yi. Haka na wuni ina wannan tunanin bayan na yi sallan asr na kwanta a nan inda na yi sallan, take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ni. Irin da baccin da zan iya bugan ƙirji na ce rabo na da bacci cikin kwanciyar hankali irin sa tun kafin rasuwan Abba. A firgice na farka jikina gabaɗaya yana karkarwa ga wani uban zuffan da ya jiƙa mini jiki lajab kamar wacce aka kwarawa ruwa. Ƙirjina ya na dakan lugudan-lugudan tara-tara tara cikin daƙiƙu tara. Na buɗe baki zan kurma ihu sai kuma na yi hanzarin tufe bakina da tafukan hannayena. Allah ya ba ni ikon karato addu'ar da ta yi nasarar fara zuba kaina a cikin wannan rikitaccen yanayin mai kama da almara. "Hasbunallahu wa ni'iman wakil". Na furta har izuwa lokacin ilahirin jikina yana rawa sa boda munin mafarkin da na yi da Ummata. Mafarki na yi wai ga ni ga ita a gaban Allah ya na yi masa hisabi yayin da yake tuhumarta akan amanarta da ya ba ta ta yi masa riƙon sakainan kashi ta kuma wofartar da nauyin da yake bi sa wuyanta, wai Ummata ta gaza kare kanta Mala'ikun azaba suka saka mata sarƙan wuta su ka nannaɗe mata jikinta suka jefa can cikin ƙasan wuta, ina ji ta na ihu ta na kururuwar neman ceto da agaji na yunƙura zan je na taimaka mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98