Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na ciyar da kaina". Na yi ƙuri tana kallona tamkar ba da yaren Hausa na yi maganar ba. "Ba na ce babu ba amma dai na sanar da ke abin da yake a zahiri ne. Idan tun farko kin ga ba za ki iya ba ina mai ba ki shawarar tun kafin tafiyar ta yi nisa gwada ki koma gaban iyayenki don na ji ana cewa mutumcin kowacce mace a iske ta a gaban iyayenta komai talaucinsu. Ina takaicin ganin yadda kullum a cikin gidan nan sai an yi baƙin mata wasu sa'annina wasu ma na fi su a shekaru". Kafin na yi magana aka ɗago labulen ƙofar ɗakin babu neman izni Aminu ya faɗo cikin ɗakin ya bi mu da kallo kafin ya ƙariso ya zauna. "La'aniyatutu manyan gari wannan ɗin ma kin zo ki hure mata kunne ne kamar yadda kika saba? To ina so kin san wani abu guda ɗaya duk abin da kika ga ya sa ɓera fitowa daga raminsa ya faɗa wuta to haƙiƙa ya fi wutan zafi da ƙona a gare sa". Ta banka masa harara tana cuno baki ta ce"ni fa ka daina ɓata min suna, sannan ni ba wani hure mata kunne da na zo na yi na dai faɗa mata gaskiya ne kawai sannan ban mata dole ba in ta ga dama ta yi amfani da abin da na ce da ita in ta ga dama ta watsar da shi a nan da muka yi maganar". Tana gama faɗin haka ta tashi ta fita tana ƙananun magana. "Ina kwana an tashi lafiya". Na gaishe shi cikin girmamawa maimakon ya amsa sai ya jefo mini wata tambayar ta daban. "Ba wannan ba ne ya kawo ni na zo na ji hukuncin da kika yanke ne?". Na sadda kaina ƙasa ina sauƙe tagwayen ajiyan zuciya kafin na ce"zan zauna". "Za ki zauna?". Ya maimaita abin da na ce na gyaɗa masa kaina alamar e da hakan ya ba shi damar ci gaba da zancen daga inda ya tsaya. "Kin yi kyan kai kuma ina mai tabbatar miki da cewar ba za ki yi dana sanin zamanki a cikin gidan nan. Tun da na fara ganinki na hango wani a tattare da ke bariki za ta yi miki riga da wando". Na yi hanzarin katse shi"ni ba bariki na zo yi ba, zan nema sana'an da zan riƙe kaina da shi". Da mamakina sai na ga ya fashe da dariya har yana riƙe ciki sai da ya yi mai isars kafin ya ce"ba yau na saba jin irin wannan kalaman ba hasalima duk wacce kika gani a bariki da irin wannan kalaman take farawa, amma idan tafiya ta yi tafiya sai zancen ya sauya. Da ƙafarki za ki zo ki na neman wanda zai kwana da ke......". Na runtse idanuna tare da kai hannuna na toshe ƙofofin kunnuwana"ba zan taɓa aikata zina ba". "Lokaci ne zai tabbatar da hakan ƴan mata. Yanzu dai akwai wani abun da kike buƙata ne?". "Babu wani abun da nake buƙata, don wanda ka kawo jiya ma ban yi amfani da shi. Sama ko ƙasa na neme shi na rasa". "Ai mantawa na yi ban gaya miki ko filin tsakar gidan nan za ki fita ki ja ƙofar ɗakinki ki rufe shi da makulli. Don akwai ɓerane masu suffa mutane a cikin gidan nan da kuma masu dogon hannu, zan karɓo miki makulin ɗakin a wajen Hajiya Babba sannan zan taho miki da abin kari". Bai jira abin da zan ce ba ya tashi ya fice ya bar ni zaune a cikin ɗakin mamaki ya hana yin ƙwaƙwƙwaran motsi, so nake yi na yi karatun alƙur'ani amma ban ga alamar zan sama littafin alƙur'ani mai girma a cikin gidan ba, don haka na kifa kai da gwiwana ina karato abin da yake haddace a cikin kaina. "Da kin bar karatun nan tukunnan kin sa wani abu a cikin cikinki ƴan mata". Na tsinkayo muryar Aminu a tsakiyar kaina, na ɗago kaina ina duban sa yayin da yake ajiye wani baƙin leda a gabana kana ya miƙo mini wani ɗan makuli na kai hannu na amsa. "Wannan shi ne makullin ɗakin duk inda za ki motsa ki ja ƙofarki ki rufe ta, in ba haka ba kuwa an dinga yi miki sakiyan da babu ruwa, wataran hatta tabarman da kike kwance akanta sai an ɗaga ki an ajiye a gefen an ɗauke ta". "In sha Allah zan na rufewa". "Da kin yi kyan kai kuwa, ga abincin nan ki samu ki ci. Zan ciyar da ke na tsawon sati guda kafin ki waye da wasu abubuwan daga nan kuma zan bar ki da halinki ke za ki fita ki nemo ki ciyar da kanki har ni ma na raɓe a jikinki". Jikina ya yi sanyi ƙalau na kasa cewa komai har ya fita daga cikin ɗakin na ɗade zaune a inda ya bar ni ina ta saƙa da warwara a cikin raina. Ganin yunwa tana neman yi mini lakani ya tursasa mini jawo ledan na buɗe awara ne da buredi sai pure water guda biyu, na soma ci don maganin yunwa ba don ina jin daɗi ko ɗanɗanonsa a bisa harshena ba. Sai da na cinye tas na shanye ruwan guda ɗaya na bar ɗaya a waje na yi bacci ban san adadin awannin da na kwashe ina baccin ba sai hayaniyar da na ji kamar a cikin mafarki ne ya tashe ni. Na fito ƙofar ɗakin na tsaya domin ganewa idanuna abin da yake faruwa, kowa tana tsaye cirko-cirko a filin tsakar gidan. Yayin da wata matashiyar budurwa ta sha ɗamara tamkar mai shirin zuwa filin gwabzawa sai bala'i take yi kamar za ta yi aron baki. "Daman na daɗe da fahimtar don ƴan gidan nan hassada suke yi min sun ƙi jinin su ga na yi wani babban kamu. Tun da na haɗo da Alhaji Bashiru yake yi min ruwan sulalla ake yada min da magana, shi ne yau don an ga ba na nan aka haɗa baki za a yi min sakiyar da babu ruwa, shi ne aka ja shi har cikin ɗaki akan tsegumta masa cewar wai ba shi kaɗai yake zuwa ɗakina ba. To kwarankwatsa dubu ba zan laminta ba ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa, ko a fito min da munafukar ko kuma na bankawo gidan nan wuta kowa ya ƙone". Kamar wacce aka jefo ta haka Hajiya Babba ta fito daga cikin ɗakinta tana bala'i. "Wacce shegiyar ce mai tsinin baki nake jin tana ambata ƙona min gida?". "Hajiya ni ce munafurci aka haɗa min. Don an ga bana nan shi ne da Alhajina ya zo aka ja shi ɗaki ake tsegumta masa wai ba shi kaɗai yake zuwa ɗakina ba". "Ke Farida ƴar mutan gabas sa idonki a cikin nawa ki kalle ni da kyau. Idan ba ki shiryawa bariki ba kika shigo cikinta to ki kuma ki je ki nema ilminta sannan ki dawo. Ke yanzu akan wannan abun ne za ki zo ki na tada jijiyar wuya har da ikirarin ƙona min gida, ke yanzu sai na zaunar da ke na fassara miki ma'anar wannan karatun da ake faɗin duk wanda ya yi maka kan kara ka

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});