Chapter 63
Chapter 63
nan? Me ye kike nema daga gare ni?". "Ka ci abincin tukunna sai mu yi magana". "Na fi buƙatar amsar waɗannan tambayoyin fiye da komai a yanzu". "Ko kaɗan dai ka ci sai mu yi maganar". Ina gama maganar na ɗauki kofi na tsiyaya masa ruwan shayin wanda ina da tabbacin shayi ne na musamman kuma na girma aka yi masa. Na miƙa masa kofi ya ƙi karɓa ban yi ƙasa a gwiwa ba na ajiye masa a gabansa na koma na ci gaba da cin abincina. A ƙalla ya yi mintuna ashirin kafin ya ɗauki kofin shayin, nan ma sai da ya daɗe da shi riƙe a hannunsa kafin ya kai bakinsa ya kurɓa, na ji wani sanyi a cikin raina tare da wani nutsuwan da ya yi bake-bake a cikin ruhina. Sai da ya kusa sanye wa kafin ya ajiye kofin ya na kallona ya ce"ke nake sauraro". Na ajiye cokalin da nake cin abincin da shi na ɗauki gorar ruwa na kora na yi hamdala kafin na dawo kan kujerar da yake kusa fuskantar wanda take zaune a kai na zauna. [12/17, 4:47 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ______________________________________ Page 7️⃣1️⃣ Tagumi na zabga tare da zube idanuna akan sa yayin da shi ɗin ma ni yake ta faman kallo, cikinmu babu wanda ya ce uffan illa murmushin da yake ta sakar mini na lura izuwa lokacin maganin da na sanya masa a cikin lemon ya fara aikinsa a cikin jikinsa. "Ka na ta kallona ba tare da ka ce wani abu ba, ahalin ka san cewa kai nake sauraro". Na yi zancen muryata can ƙasa ina sarrafa harshena cikin salo da hikima. Sai da ya lumshe idanunsa kafin ya cikin wani irin yanayi ya ce"Amatullahhhh". "Na'am ya Sheikhi". Na yi caraf na amsa ina ka she masa ido guda da hakan ya ba shi damar soma zuba tamkar bakin indararo, hakan ya sa na yi wuf na fito da wayar da take jikina na danna recording na soma naɗar muryarsa. "Amatullah na neme ki sosai bayan da na sama tabbacin cewar kin ɓace watau kin gudu daga cikin gidanku, kin bar gaban iyayen da danginki kin shiga duniya. Na ba za mutane ta yadda na ba da aikin nemanki a ko'ina sai dai har zuwa wannan lokacin babu wanda ya zo min da wani labari game da ke. Tun ranar da na fara ganinki a ciki wannan tashar ki na tallan kunu na ji cewar kin kwanta min a cikin raina, na ƙudurce cewar komai runtsi komai tsanani sai na cimma buri akan ki sai dai ke ce mace ta farko da kika fara karya alƙadarina da kuma ikirarin da nake yi wa kaina na cewa duk abin da na sa a gaba da niyyar mallakarsa babu makawa sai na same ko da kuwa nisan da yake tsakanina da shi ya kai tafiyar dake tsakanin nan inda muke zuwa cikin birnin sin. Tabbas a zahiri ni malamin addini ne a idanun duniya, ilmina ya jawo min girmamawa da mutuntawa daga wajen mutane da yawa wanda ko da a cikin mafarki ma ban taɓa tunanin zan ina saka kafata a inda suke ba balle har su ba ni wannan girman da mutuntawa, a idanun mutanen ƙasar nan ni mutum ne mai gudun duniya da kuma ruɗin da yake cikinta ni mutum ne kamili da duk wani abun cikin duniya bai dame ni ba balle ya ɗaɗani da ƙasa. Duk da kasancewa ta ba ɗan siyasa ba ne kuma ba ni da haɗi da gwamnatin da ayyukan da take yi amma ganin kimata da darajata da duniya take hakan ya jawo min kusanci da gwamnoni bila adadin ta yadda nake iya ganawa da su a duk sa'ilin da nake so, babu wata buƙatar da zan je da ita gabansu ba tare da sun kawar min da ita ba". Ya tsagaita tare da yin wanin gatsa mai warin da ya tilasta mini ɗauke numfashina na wucen gadi idanunsa suna ta ƙoƙarin rufe wa amma ya na tilasta buɗe su tare da ci gaba da zance daga inda ya dakata. "A zahiri ni malamin addini ne wanda ya ke kiyaye dokokin da ya shimfiɗa kuma ya yi hani da a aikata su, sai dai a baɗili ni ɗin tantarin manemin mata ne sai dai duk cikin wannan duniyar babu wanda ya san hakan don ni idan zan nema yarinya ba na zuwa inda aka san muryarta balle kuma fuskana, na fi mu'amala da matan ƙasashen waje mussamman ƙasar Ghana, Senegal da kuma Kenya sa bosa gudun matsala da tashin zance, sai kuma matayen can kugu su ma sai lokaci zuwa lokaci. Ke ce mace ta farko da na fara ƙyalla idanuna akan ta har na ji sha'awar kasancewa tare da ita a nan arewancin Najeriya, haka nan ke ce mace ta farko da na yi buri a kanta daga ƙarshe kuma ban same ta ba, a yadda na tsara ranar da ayi walimar yaye ku daga islamiyya a ranar zan kwanta da ke sannan na cusa miki tsoro da razani tare da fargaba a cikin ranki ta yadda ko bakin bindiga aka sanya miki a goshinki ba za ki taɓa ambaton sunana ba ko da kuwa maganar ta tashi asiri yana neman watsewa. Kwatsam sai kuma wannan abin mamakin ya faru". Ta katse shi"wani abun mamaki ke nan?". Ya kafe ni da ido kamar zai cinye ni ɗanya kana ya ce"bayyanar ciki a tare da ke mana da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinki, sannan mahaifiyarki ta yi ikirarin ta sallamaki ga duniya ba ta buƙatar ƙara sanya ki a cikin idanunta. Wannnan dalilin ne ya sanya ki shigo harkar bariki gadan-gadan tun daga lokacin da na tabbatar da cewar kin bar gida kuma har cikin da yake jikinki ya zube tun daga sa'ilin na sauya akalar manufata akan ki don a tsarina ba na taɓa haɗa shimfiɗa da wacce wani ya taɓa kwantawa da ita ko da kuwa bisa tsautsayi ne balle wacce take da ƙarfin halin da bushewar zuciyar shigo wa bariki, a tarihin balaɗala sai yarinyar da ba ta san ko wani ɗa na miji ba nake mu'amala da ita sai kuma wacce ta ƙoshi da tarbiyya aka yi mata shaidar nutsuwa da kamala ni kuma na zo cikin daren guda na wargaza dukkan shiri da tanadin iyayenta akan ta na bar su su na cizon ɗan ƴatsa, watan har mun gama komai na yi cinikinta a kawo min ita ba za ta taɓa jin muryarta ba balle ta mu yi ido huɗu da ita sannan ba na amfani da komai wajen kawar da hankalinsu ko shaƙa musu abin da zai sa su fita daga hayyacinsu, ki na cikin hankalinki kuma ki na ji ki na gani za mu yi komai sai dai na ri ga da na rufe bakin kuma na goge komai na cikin ƙwalƙwalwar". Jikina ya soma rawa tamkar mazari haƙwarana suka datse harshena wasu hawayen suka ciko kurmin idanuna sai dai na ƙi ba su damar kwaranya, sai da na haɗo jarumta kafin na iya faɗin" wani buri daman kake da shi a kaina?". Bai amsa mini ba illa dariyar da ya saka mai sauti ya na ƙoƙarin kai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98