Chapter 88
Chapter 88
sa boda yadda ya tsare ni da idanunsa har sai da na ɗan tsorita na ce"lafiya kuwa?". Ya ja dogon numfashi mai nisan zango kana ya furta"don Allah ƙara ƙiran sunan na ji, sai na ji kamar babu wanda ya kai ki iya furta sunan daidai. Ban taɓa jin an ƙira sunan da na ji daɗinsa irin haka ba, don Allah ki ƙara faɗa ko sau ɗaya ne". Na ɗaga ido na saci kallonsa daidai lokacin da yake ƙara faɗin"Please mana". "Cewa na yi Yaya Saif". Ina furtawa na juya da sauri na shige cikin gida muka yi kiciɓus da Yaya Alhassan yana ƙoƙarin fitowa da mashin ɗinsa na yi saurin ja da baya na ba shi hanya yayin da kunya ya gama mamaye ni har na kasa ɗago idanuna, sai da ya gama fito da mashin ɗin na sama hanyar shiga ciki. Na koma wajen su Ayan na iske su har sun gama cin abincin, ina zama ƙiran Saif ya shigo cikin wayata na ɗaga ƙiran na ba wa Aryan na ce ya yi magana. Sai da suka gama na tambaye shi yadda suka yi ya shaida mini cewa ya yi in su gama su fito su tafi yana jiransu a waje. Kimtsa su na yi na kamo hannunsu muka je wajen Anty Sawwama suka yi mata sallama yayin da take musu leda taf da tarkacen abubuwa dangin su bushashshan kuɓewa, zogale, kanwa da kuwa yajin ƙuli ta ce su kai wa Umminsu. Har bakin ƙofa na rako su sai da na fitan su har suka isa wajensa kafin na jawo ƙofar na koma ciki. Haka na ƙarar da wunin cikin tsinkewar zuciya da faɗuwan gaba. Bayan na yi sallan isha'i na ɗauko alƙur'ani na soma karantawa sai da na yi izu biyu daga suratul Naba'i zuwa suratul Nasi. Ban jin sha'awan cin komai hakan ya sa ni yin shirin kwanciya na kwanta ina ta saƙe-saƙe a cikin raina. Har bacci ya fara ɗauka ta na jiyo rurin wayata na zabura na tashi na ɗauko ta tare da ɗaga ƙiran don dama shi nake jira har bacci ya sace ni. "Amatullah ina kika sama sautin muryan nan? Idan ban yi ƙarya ba fa muryanki ne me ya kai ki wajen mutumin nan? Me yasa kika naɗi sautin nan?". Ko sallama bai yi mini ba illa jerin tambayoyin nan da ya soma jefo mini a jere wani na bin bayan wani. "Ka tsaya na yi maka bayani". Na zancen cikin sanyi ganin yadda gabaɗaya lokaci guda ya birkice. "Wani irin bayani za ki yi min Amatullah bayan abin da na saurara yanzu?. Tambaya ɗaya zan yi miki wanda nake so ki ba ni amsarsa shin da gaske wannan sautin muryan da na ji mallakin Sheik Dawood ne mahaifi ga aminina Muhammad Taufik ko kuma na ce Sultan?". Cikin ƙwarin gwiwan da ban san ina da shi na furta"ƙwarai kuwa muryarsa ne, kuma duk abin da ya faɗa haka yake babu kuskure a cikinsa. Na ba ka ka saurara ne don ka ceto rayuwar abokinka da har kake ikirarin a zama amini kuma ɗan uwa a gare ka. Na ba ka saurara ne sa boda mu ceto rayuwar ƴaƴan matan da zai iya lalatawa rayuwa a nan gaba" . "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un! Allahuma ajirni fi musibati. Ya Allah ta ina zan fara? Kin san yadda nake ganin girma da darajar Malam kuwa? Wallahil azim kallon uba nake yi masa haka nan shi ma ya ɗauke ni tamkar ɗan da ya haifa a cikinsa. Ina da tabbacin Sultan bai taɓa sanin cewa ba shi ya haife sa sa boda ya ba shi dukkanin kulawan da uba zai ba wa ɗansa". A sanyaye ya ƙare zancen cikin yanayin damuwa da ya haɗe da ruɗani. "Dole ne kuwa sai na ji hakan ko ba daɗe ko ba jima. Ka fi ni sanin hanyar da ya dace ka sanar da shi wannan ɓoyayyan sirrin". Shuru ya yi na tsawon lokaci mai tsayi har sai da na yi zaton ko ƙiran ya katse ne sai da na duba na ga yana tafiya. "Hello". Na yi furucin cikin sanyayyan amo. "Amatullah". Ya ƙira sunana muryarsa ba ta fita sosai. "Na'am Yaya Saif". "Tabbas kin zo da babban lamarin da na ji kaina ya gaza ɗaukansa, zuciyata ta kasa yarda cewa Sheik ɗin da na sani ne ya rikiɗa ya zama wannan. Tabbas zan bayyana wannan sirrin ga Sultan sai dai ta ya ya kuma ta ina zan fara?". Daga ni har shi muka yi shuru don ban san amsar da ta dace na ce da shi ba. "Zan neman wani layin da bai san ni da shi ba na buɗe what's app da shi sai na tura masa, na tabbatar idan ya saurara ni ne mutum na farko da zai fara tunkara da matsalar daga nan sai mu warware matsalar a tare. Amma kai tsaye kam wallahi ba zan iya tunkararsa na sanar da shi cewar ina zargin Sheik da aikata wannan ɗanyen aikin ba". Shuru ina sauraronsa har ya gama ban iya cewa komai ba. Ina jin sa sai faman maimaita kalmar hasbunallahu wa ni'iman wakil yake yi kafin ya ce"amma me yasa kika zaɓi ni ki ka ba ni wannan memory card ɗin?". "Ba ni na zaɓe ka zuciyata ce ta zaɓe a bisa wannan aiki don a wannan ɓangaren, tabbas ka sama yardanta". "Amma da farko me ye kika yi niyyan aikatawa da sautin muryan da kika naɗa?". Babu wani ɓoye-ɓoye balle nuƙu-nuƙu na fito ɓaro-ɓaro na sanar da shi komai har da yadda muka yi da Yaya Alhassan. Ya ɗan yi jim kafin can bayan lokaci mai tsayi ya ce"tabbas kin yi kyan da kai da ba ki bayyana wa duniya wannan sautin muryar ba, Sheikh babban mutum ne a idon jama'a kuma ko ba komai shi ɗin ubana ga ƴayansa, marayu har ma da masu uban. In sha Allah na yi miki alƙawarin shawon kan lamarin nan cikin ruwan sanyi har mu warware komai ba tare da kin shiga cikin wata matsala kamar yadda Alhassan yake tunani ba". Ji na yi zuciyata ta yi saƙayau nauyin da ƙirjina ya yi mini na ji tamkar ana warware mini shi, ban san sa'ilin da hawaye ya zubo daga idona ba. "Idan har hakan ya tabbata ni kuma na yi maka alƙawarin babu abin da zai hana ni aurenka, na tare a cikin gidanka a matsayin matarta". Da gaggawa ya katse ni"wannan abun da kike faɗa har cikin zuciyanki haka yake?". Jikina a sanyaye na ce"ƙwarai kuwa". "Alhamdulillah! Alhamdulillah Ya Allah". Kit! Na kashe wayar ba tare da saurari ragowar zancen ba, na kwanta na yi ruf da ciki ina hawaye. Ina jin wayar tana ruri wanda ina da tabbacin Saif ne yake ƙira amma ban ɗauka ba. [12/26, 8:27 PM] Maimunatu Iyam🥰: *DAFIN HARSHE* ©️ Maimuna Tijjani Iyam ____________________________________ Page 8️⃣0️⃣ Haka na raya tsawon daren da sallan dare sai bayan sallan asubahi na samu na kwantar da haƙarƙarina take wani bacci mai nauyin gaske ya yi awun gaba da ni, cikin baccin na ji ana ƙiran sunana cikin sanyin amo tare da bubbuga matashin da nake kwance akan sa. A hankali na soma buɗe idanuna har na buɗe su tar akan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98