Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 91

Chapter 91

Dafin Harshe Part 1 Complete Hausa Novel – Full Story 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nema na rasa". Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce mini komai ba ya juya ya fita daga cikin ɗakin na raka shi da kallo har ya fice kafin na sauƙe ɓoyayyan ajiyan zuciya mai nauyin gaske. Na daɗe zaune a wajen kafin na tashi na je na nuna wa Anty Sawwama kuɗin ta yi ta sanya mana albarka tare da yi mana addu'ar Allah ya haɗa kawunanmu kana na fito na soma rage wasu ayyukan cikin gidan. Haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa lokaci yana shuɗawa har aka dosa kwanaki biyar ba tare da Saifullah ya ƙira ni ba hakan nan du ƙiran duniyar nan da zan yi masa layinsa ba ya shiga, duk na bi na damu hankalina ya yi mummunan tashi da na zauna shuru to ba ni da aiki sai tunaninsa da tunanin halin da na jefa sa ba na sanin lokacin da hawaye yake zuba daga idona sai dai kawai na ji ɗumin su a bisa kuncina. Duk wanda ya ganni ya san inda cikin matsanancin damuwa da ƙololuwan tashin hankali amma haka na yi ta ɓoye wa duk tambayar da za a yi miki cewa nake yi ba komai idan aka matsa mini ba sai na fashe da kuka ala dole suke haƙura su bar ni ba don sun sama abin da suke so ba. Ranar da aka cika sati da faruwan lamarin a wata safiyar ranar lahadi ƙiran Saif ya shigo cikin wayata kafin na ɗauka ƙiran ya tsinke ina ƙoƙarin bin ƙiran ya ƙara ƙira a karo na biyu. Jikina yana rawa na ɗaga ƙiran na soma amayar da tulin damuwar da yake kwance ƙasan raina. "Lafiya kuwa kwana da yawa inna ƙira layinka ba ya shiga, sannan ba na ji daga gare ka ina fatan dai lafiya babu wani matsalar ko?". Sai da ya numfasa kafin na ce da ni"ki na gida ne?". "E". Na amsa da shi har zuwa lokacin jikina yana rawa tamkar mazari. "Nan da awa ɗaya mu na zuwa, ki sanar da mutanen gidan". "Ku na zuwa kai da waye ke nan? Sannan lafiya zuwa haka bakatatan ba tsammani?". Na yi zancen jikina yana tsananta rawan da har sai da ya tilasta mini yin zaman ƴan bori dirshan a ƙasa ina sauraron amsar da ya dawo mini da ita muryarsa cike da rashin walwala. "Idan mun zo za ki ga wanda za mu tare da shi, sannan za ki ji dalilin zuwan mu". Daga haka ya katse ƙiran ya bar ni da faman faɗin"hello! Hello". Har sai na fahimci ba ya kan layin kana na saduda. "Innalillahi wa inna ilahirin raji'un!". Na furta ina dafe ƙirjina da yake buga wa fiye da kima a kimiyyance. Jikina a sanyaye na je ɗakin Anty Sawwama na sanar da ita zuwan su Saifullah, ita kan ta sai da ta tambaye ni ko lafiya na ce da ita ni ma ban sani ba. Haka na gudanar da aikin da ya kallafa a kaina cikin sanyin jiki da rashin kuzari. Ina zaune a ɗaki na ji sallamarsu a tsakar gida na leƙo ta taga na ga tare suke da Yaya Alhassan da kuma Umar da suka yi musu jagoranci har zuwa cikin gidan suka shigo falo suka zauna, Anty Sawwama ta fito suka gaisa kana Umar ya zo ya ƙira ni na fito na gaishe su, ganinsa tare da Muhammad Taufik ya sanya jikin ƙara sanya tamkar kazar da aka gauraya a cikin ruwan gishiri, na je musu ruwan sha na ajiye a gabansu zan koma ciki Yaya Alhassan ya ce na dawo na zauna haka na yi na koma na zauna kaina a ƙasa ina sauraron yadda ƙirjina yake bugu tamkar zai faso allon ƙirjin ya fito waje ya taka rawan disko. "To kamar yadda na riga na sanar da kai tun a waje wannan shi ne dalilin zuwanmu, don na ga ya dace ku san abin da yake faruwa. Sannan aminina Sultan ya buƙaci ya zo don ya gabatar da godiyansa a gare ku a madadin dukkan ahalinsu". Saifullah ya yi zancen a dunƙule da ya sanya kan Anty Sawwama kullewa, take Saif ya warware musu duk yadda muka yi da shi akan wannan memory card ɗin akan kowa. Anty Sawwama ta cika da mamaki don a ta yi zaton hakan ba, Yaya Alhassan ma duk da Saif ya riga da ya sanar da shi zancen tun kafin su shigo ciki sai da ya cika da mamaki ainun. A wannan karon Muhammad Taufik ne ya karɓe zancen cikin faɗin"tabbas sa'ilin da na saurari wannan sautin muryar ba zan iya fasalta tashin hankalin da na shiga ba, duk dauriya da juriya irin zuciyar na miji sai da na ji hawaye sun zubo daga idanuna na kasa fassara kaina da har sai da hankali na gushe daga gare ni. Saifullah shi ya kasance a tare da ni a cikin wannan yanayin mai tsauri ba zan taɓa mance wa da shi a cikin tarihin rayuwata, cikin hikima da fasaha muka tunkari Sheik da zancen kuma cikin ruwan sanyi ya amsa cewar duk abin da muka ji haka ne, kuma tun daga ranar da lamarin ya faru shi kansa ya yi nadama mai tsananin gaske, tun daga lokacin ya kasance cikin zulumi, fargaba da kuma jiran fitan sautin muryar a duniya sai dai kuma shuru lamarin da ya karya masa zuciya ke nan. Tsoronsa ɗaya kar asirinsa ya tuno a idon duniya kar kima da darajarsa ta gushe a idanun jama'an da suke yi masa kallon tamkar waliyi a gare su, haƙiƙa manyan mutanen da ya sani da tarin ƴan siyasan da yake mu'amala da su za su yi ɓatan dabo, don babu wanda zai so ya lalata tafiyar siyasansa sa boda ƙoƙarin kare masa martaban sunansa. Tabbas ya aikata laifin da ya yi ikirari sai dai yanzu ya yi nadama matuƙa don na hangi hakan a cikin idanunsa, Malam ya yi nadama matuƙa don har sai da ya yi ƙwalla kuma ya nema gafara a bisa samar da ni ta hanyar da ba ta dace ba, ya tara dukan iyayensa ya sanar da su abin da yake faru ya kuma roƙi yafiya da gafaransu. Tabbas ba mu san inda za mu sanya kanmu ba idan maganan nan ya watso a duniya, ba mu san wani hali Malam zai shiga ciki ba, na zo ne musamman na yi miki godiya a bisa madadin dukkan ahalin Sheikh Dawood akan killace wannan sirrin da kika yi kika kuma ɗamka sa a hannun da ya dace har ya iso gare shi a cikin sigar da ya dace". Tun da ya soma maganar nake kuka marar sauti har ina ƙoƙarin shiɗewa, sai da Anty Sawwama ta riƙo hannuna tana murzawa a hankali cikin sigar lallashi da kwantar mini da hankali. Muryarta a shaƙe sa boda kukan da ya gama galabaitar da ni na soma magana a hankali, sautina ba ya fita yadda ya kamata. "Yaya Alhassan ka yi haƙuri na kasa bin umarninka, na kasa yi maka biyayya wallahi zuciyata ce take azalzala ta yayin da ni kuma na gaza jure wa har sai da na biye mata. Ban aikata hakan don na nuna maka ba ka isa da ni ba, ban aikata hakan don

Table of Contents

Chapters

98 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});